Sashe 99
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
A ranar da ta koma baban daki sai da ta ringa ihun ya kyaleta haka, dan kuwa sai da ya dauki fansar kyaleshi da ta yi na tsayin kwana arba'in wai ita wankan jego, hanyar nan sai da ta ji kamar zai dade mata fata , da kyar ya sarara mata yana lekenta zuciyarsa cike da wani irin mamakin halitarta, itace dai karama, ama kuma a lamarin nan ta dame HUZNAH ta shanye, sai dai ya bar abinsa a ransa burinsa a kulun kwananta ya zagayo ya labe tunda magariba sai sallar asubahi.....to yaya zai yi da ransa, tuzuruwar kauye da ta tashi shigowa rayuwarsa da tumtube ta shigo, tunda ta auko kuma ta kanainaye gurbin adalci kawai ta bari a zuciyarsa.................
____________ranar kai ziyara gidan yari____________
A nutse yake tafia, gefensa Inna Hindu ce cikin zumbulelen hijabinta tana goye da Yarima ko nace daga bayansa dan kuwa a zagaye suke da dogarai da kuma Sarkin yanka sunna ziyartar mutanen gidan yarin har suka zo dakin da Umma ke ciki
Tun daga nesa kadan zaka ringa jin wani irin wari da duhu a daki har ka iso, sunna isowa da sauri ya dauke kansa, domin Umma a shanye take ta baza kafa kuda sai bin jikinta yake wanda ke fitar da wani irin ruwa mai tsami , haka kuma jikinta du ya yi wani irin kuraje luhu luhu, fatar jikinta ta dafe, gashin kanta tamkar na mai cancer du ya zube ya yi furu furu, ta rame sosai sai manyan idannuwa , ita daya ce a dakinta domin wa'inda suke daki daya sun gudu dan idan ciwo ya yi ciwo haka take yagar fatar jikinta tana ihu, an kaita asibitin ya fi a irga, ana bata maganin ama sai a hankali jiki fa ya tabu, wanda a yanzu take rokon a kasheta ta huta, abin ya gagara
Juyawa ya yi yana umartar su koma, a lokacin da ta hangi Hindu ta kuma hango goyon dake bayanta, a lokacin ta saka wani kukan mage mage kare kare tana nuno bayan na Hindu, dan kuwa wani irin abu da ya ringa tukota kennan dai da gaske har haihuwa ASADEEK ya yi? Lalle ita ta zo a banza zata koma a banza....................
Asadeek kuwa, a tausashe yana dan kallon kasa da irin girmama ya ce da Inna" Mamah, a raka ku gida, zamu je kauye mu dawo"
Inna ta amsa ta juya dogarai suka sakata a tsakiya tana taku daidaiya ana gaisheta tana amsawa hakoran nan a fili da hakoran makarta bibiyu sama da kasa suka wuce ciki
A cikin mota sunna tafe Sheikh ya dube shi, a hankali ya ce" ABU TUFAINAT, murmushin me kake yi?"
ASADEEK ya juyo ya kalli Sheik, ya yi murmushi ya ce" Ina yin dariyar sarkin yanka ne, yace wai anya zan kuma.iya yarda da wani dan Adam a kan abinda Umma ta min?"
SHEIK na kallonsa ya ce" Nima na ji tsoron haka sosai"
Asadeek ya koma ya ringesa, cike da iza ya ce" Idan na yi haka kennan ban godewa Allah ba, ai dole za'a iya haduwa da haka, ba kuma haka zai sa mutun ya rufe kansa ba, MUTUN ai rahama ne, Kamar yadda aka samu na banza sosai, haka kuma ake da na kirki sosai, misali GAKA nan, ina alfahari da hakan...ina kuma fatan mutuwa cikin jarabawa, dan kuwa bawan da Allah ke so yake jarabawa........"
SHEIK na murmushi ya ce" Amen ya Allah "
Nima na ce
*ALHAMDULILAH*
*ALHAMDULILAH*
NAN NA KAWO KARSHEN LITAFINA MAI SUNNA UMUGHLUK ITIBEL, INA ROKON ALLAH YA YAFE MIN KURAKURAN CIKI, SANNAN INA ROKON DU WANDA NA BATAWA YA YAFE MIN, INA MIKA GAISUWATA A GAREKU BAKI DAYA, DAN KUNNA DA YAWA WALAHI KUMA KUNA DA MAHIMMANCI SOSAI A RAYUWANA......, INA KUMA FATAN ALLAH YA SA DAGA WANNA LITAFINA NA GABA IN AJIYE RUBUTU HAKANAN, MAI TAKEN *ƊAKIKA ƁIYAR*
Nobel dina na gaba in sha Allah.........
*ƊAKIKA ƁIYAR*
TAKU CE yar mutan NIJAR.........
*Sajida*
Nd