Sashe 64
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Idannuwansa ya dan buda irin oh really? Din nan, sai kuma ya dubi gaban rigarta da jinnin ya bata sannan ya zubawa gaban rigar ido da kyau yana ji jikinsa na neman birkicewa
Da sauri ta juya tana kallon kofa tana auna irin gudun da zata arce da shi dan barin dakin wannan mutumen
A zabure ta rintse ido sakamakon jinta a jikinsa ta baya
A birkice ta juyo ya kasance ta shige kirjin nasa gaba dayanta sai kuma ta dago ta saka hannayenta dan yin kariya da hannunta da kirjinsa, muryarta a raunane ta ce" Ka bar min irin haka dan ALLAH"
"Yaya zaki tambayeni me zaki yi min bayan kina tare da abinda yake nawa? ............." Ya fada a tausashe , sai kuma ya dora hannunsa a hankali ya dan shafa bayanta yana lumshe idannuwansa a hankali ya dake fadim" Wai da so na yi na sake tsoma lipton dina a cikin shayina"
Ido ta rintse wata masifafiyar kunya na tasowa tun daga kafafuwanta ta rufe har kanta
Hannunsa da ta ji a wajen cinyarta a hankali ya sakata dora kanta saman damtsen hannunsa a hankali ta sauke sansanyar ajiyar zuciya sannan ta dago idannuwanta ta zuba dubanta a saman ni'imataciyar fuskarsa tana kallo
Hannunta ta dago a hankali ta dora a gefen fuskarsa mai dauke da ni'imtacen sajen dake kyali na duhu da tsarinsa ta dan shafa tana kallon karan hancinsa har zuwa jajayen lebunansa masu kama da fitsararun lebe
Idannuwanta ta lumshe a hankali ta ciro harshenta tana dan lasar lebenta da take ji kamar ya bushe mata kauuuuu dan wata bakuwar jaraba
A hankali ta ce " LIPTON din ne naka Aban datawa....................., Aban datawa kai baka san ba'a wawurar nama daga ganninsa ba?"
Wata irin ajiyar zuciya yake saukewa, jikinsa na saki gaba daya yana sake dubanta, subahanalah haukatashi aka aikota yi ne? A gaskiya wannan yarinya koda zuwa ta yi dan ta kashe shi ya shirya ya sakankance kawai ta auna masa ko meye ta morw abinta, ai ko a haka ya tafi kam ya ga mata gannin idannuwansa
Muryarsa ta riga ta koma cen cikin makoshinsa ya ce" Shi nama, idan naka ne, ai kana da damar ci a duk lokacin da bukatar hakan ta motsa maka ko?"
A hankali ta cire dubanta dan haka kawai sai ta ji kan mamanta ya fara yi mata kaikayi, yau ita ke karra gannin sabin salalamen rashin da'a a jikinta
A hankali ta dan janye jikinta baya tana jan rigarta ta rufe da kyau ta dan juyar da bakinta gefe ta ce" A daina kwace"
Ido ya dan zarro yana tsaye irin tsayuwar nan da ake dan wara kafa, so yake ya tambayeta shin wacece ita? So yake ya san kadan daga cikin lamarinta, ama SHEIK ya wani dakatar da shi
A hankali ya ce " Bafa kwace na yi ba, cewa kika yi na kama, da kyar na yarda fa"
Ido ta zarro tana shagwabe fuskarta kamar zata fashe da kuka tana kallonsa, hakan ya saka shi sake zuba mata ido, yana girgimama sarautar mai sama, yanzu dai wannan yar dukus din nan ce ta ga manya a yadda ungozoma ta mikowa GIMBIYA , gatanan abinta idonta idonsa, gaskiya mata Allah ya masu baiwa
Juyawa ta yi a hankali ta nufi hanyar ficewa hakan ya saka shi dan karkata kansa yana kallonta muryarsa na dan fita ya ce" Ina zaki je kuma?"
Dakatawa ta yi , sai kuma ta juyo tana nuna masa kasa kasa ta ce" Ka manta matarka na kasa?,"
Dan sake zuba mata ido ya yi, abinda ke zuciyarsa nada yawan gaske
Juyawa ta yi ta kama abin budewar tana kallin girman abin budewar kasa kasa ta kuma cewa" Bayan wannan, aikin da kake son bani, ba shine aikina ba......... Shi nama ai kanada da yawa, ya dace ka barawa wani nasa!"
Rufewar dakin ne kawai ya fargar da shi da tunanin da ya auka na furucinta,
Ba wannan aikin ta zi yi ba?, Ya dace ta barawa wani namansa? Me kennan?................ .............. ........
Readers me kennan?☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```

*https://www.facebook.com/106494781436168/*
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
_FREE BOOK_
*Na*
*SAJIDA NIGER*
4️⃣5️⃣
Ku karra hakuri jama'ata 😁 in sha Allah saura kiris na dawo daga hutu
A hankali ya karasa bakin bed din ya zauna yana sake kafe waje daya da ido
Ba wannan aikin ya kawota ba, shi nama ya dace ya barawa wani nasa??????????
Gefen mataunansa ya dan cije, hakan ya sa kashin gefen fuska dake boye bayana ƙadan ya nuna alamun abinda ke cikin zuciyarsa
Ya barawa wani namansa?, Ba wannan bane ya kawota?, Anya zai iya hakura har sai an nuna masa abunda ke wasa da hankalinsa kuwa?
A hankali ya sake lumshe idannuwansa, yana ji a cen kasan zuciyarsa anya zai iya ja da wannan rikicin kuwa? Bai san rikici irin na cen cikin zuciya ba, wanda ya sani na fili ne, a bayane, wanda zai ja tunga ya daka da kaffarsa a suma, ba irin wannan ba wanda yake daidai da boyayoyina da makaho
Safarsa ya cire ya dora kafafuwansa ya sake harde hannayensa yana jin jikinsa na ta neman rikice masa
'Ama me yasa zata yi min haka?, Na yi mata wani laifi ne? Bata san girman hakina dake kanta bane?, Ko bata gane a kanta na san lamarin bane? Ya dace ta zamto mai tausayi da jin kai a gareni, domin nima ai mutun ne, ko laifi na yi mata ya dace mu zauna mu yi bayani ko?' yake ta ayana a sanyaye cikin zuciyarsa, jikinsa kuwa banda sake rikicewa babu abinda yake yi, a yanzu bai san me zai yi tunani a kai ba, shi dai ba zai ce bai san so ba, domin matarsa uwar gidansa soyaya da yarda ke rike da mu''amalarsu, da babu so da tausayi da jin kai da sun raba hannu a yadda suka kasance mararsa anfani ma junna, haka kuma shi ya san cewa tsakaninsa da wannan yarinyar babu maganar so , yana dai tunanin abinda ya sa yake matukar jin kamar numfashinsa zai tsinke idan yace zai zauna ya zurfafa a tunanin son gane wacece ita?, Me ta zo nema rayuwarsa?, Tana daya daga cikin masu neman gannin bayansa? Idan har haka ne to shi yaya zai yi da rayuwarsa? Zai iya fadin yana ji a zuciyarsa sai dai su kashe junna shi da ita, yana jin a ransa cewa a kanta yana iya tafka aikin da za'a ga rashin wayonsa, gata yarinya karama duda bai san shekarunta ba, gata yannayin wajen da suka fito ba iri daya ba domin a bayane yake ita din ba jinnin sarauta bace, kai lamarinta na hadasa masa ciwon kai mai tsananin gaske...............
Da farko a zabure ta fito da gudu gudu ta nufo matatakalar saukowar tana waigen bayanta gabanta na faduwa tana Adu'ar Allah ya shiga tsakanin na gari da mugu, watau ita da wannan bawan Allah
Tana hango matarsa zaune da kanwarsa ta ja ta tsaya tana sauke numfashi wani na korar wani tana daidaita kanta da tunanin abinda ya dace ta aikatawa matarsa dan ta karra dorata a kan layin mijinta cikin dabara ba a bayane ba
Tafiyarta ta daidaita tana kin kallon jinnin dake gaban rigarta a ranta tana ayyana cewa' In sha Allah, na kusa gamawa, in sha Allah na kusa, ba zan tsaya sai sun banu damar sanar maka wacece ni ba , zan kwatanta maka ta yaren da na fi iyawa, zan kuma ganar da kai a aikace idan ya so sai ka kashemu dan mun shigo maka rayuwa!'
"Ana hutawa?" Ta fada a hankali a lokacin da ya rage mata matatakala biyu ta idasa saukowa bayan ta dafe hannunta a jiki ta yi wani iri da fuskarta irin yannayin nan na raini
A tare suka zuba mata ido sunna kallonta, irin kallon nan na karewa mutun kallo, bama kamar Bahija da sai da ta ji gabanta ya tsinke ya fadi da karfin balaki ta zubawa NADIRAH ido
NADIRAH ta dan tabe baki tana jan hanci ta kalli sama, sannan ta sake kallonsu ta idasa saukowa ta karaso fallon tana kallonsu kasa kasa ta ce" Ama ai dai ba sai an ce maku ku tafi ba ko? Fisabililahi mace da mijinta a ranakun amarci a ringa sakata a gaba ana mata ido ido kamar an kama kwartuwa?, Ni kam wannan lamari nakunyana daure min kaina, ta yaya za'a ce du dare na Allah a ranar da take taku ko ba taku ba sai kun zo kwayakwayanku da kwarkwatarku kun sakan miji a gaba kunna ci yana ci an hanna ni yar soyyayar da abina?, Sam wannan tsari baya birgeni, kuma na dakatar da shi!" Ta idasa tana hade girar sama da ta kasa tana duban HUZNAH da ta wara idannuwanta da suka sha kwali mai kyau tana yiwa bakuwar jarabar da ta risketa fashin baki dan ta gane irin jarabar da zata kasheta ne ko ta jigatatata? Yau ita Huznah wata mace mai daura zani zata koyawa zama da mijinta ko cenza tsarin mijinta?