← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 99

Sashe 28

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

NADIRAH ta kalli abanta da innar birni ta ce" To menene? Ku fada min menene kun ji? Me yake faruwa ne? Kalli Innar birni kamar wace ke kuka ko?"

HINDU ta karra hadiye nata kukan itama a hankali ta ce" Abinda yake faruwa shine, sun so bada yarsu aure wa UMUGHLUK ITIFAL dan ta je ta isar da bukatarsu na kawar da shi a doron duniya, sai ta kiya , kasancewar tanada damar hakan a wajensu, sai abin ya juye zuwa................"

"Hindu" Aban NADIRAH ya fada a hankali yana katseta

HINDU ta saki hannayen Nadirah ta sad kanta hawayenta suka bale

A hankali ta juya wajen Abanta tana kallonsa

Mahaifinta ya yi dan murmushi ya ce" kina ji?, Na amince da haka, innar birni ta amince da haka, dan baban abinda ya fi janmu amincewa da hakan shine tunaninmu zamu iya kare wani abun ta damar da Allah ya bamu, Gaskiyarsa da kare yancin talakawa ya siya masa makiya, barima ki ji NADIRAH, ina iya guduwa da ku, domin masu tsaron kofar cen su biyu babu abinda suka isa su yi, na tabata idan na shiga masarautar da ku na sanar masa abinda yake faruwa zai iya daukan mataki, sai dai tsorona shine , shin sunne kadai mafarautansa ko maciji zan kashe ban sare kansa ba?, Na karashe maki magana , a amincewar tamu mu din ba masoya zamu kasance a gaban idannuwansa ba, ta yiwu idan mun yi nauyin baki har muna iya samun mugun hukuncin da kawunnanmu ba zasu iya dauka ba....., Haka kuma cikin hatsarin da zaki je ana iya cin galaba a kanki, a haka duka muka amince NADIRAH muka salwantar da farin cikinmu, ba dan komai ba sai dan mu kamanta kyautatawa wanda yake kyautatawa bayin Allah "

Irin kallon da NADIRAH ke binsa da shi, kamar tana son gane a fuskarsa me da me aka hada aka haliceta ne!, Muryarta na rawa ta ce" Aba , da me kuka amince?"

"NADIRAH ke fa ba karamar yarinya bace, shekaru ashirin ba kwana ashirin bane, a birni ko a kauye kin isa ajiye ya'ya uku rass naki, abinda ake nufi shine an saka aurenki ke da UMUGHLUK ITIFAL nan da kwana goma sha biyu bi'izinillah, zaki je a matsayin yar sarkin garin nan, zaki je ki rayu a cen a matsayin matarsa, bisa umarninsu, sannan zasu biki da wani aiki wanda idan kika aikata ke da ubangijinki, watau kawar da shi a doron kasa!, Abinda mu muke maki nuni a nan kuwa shine, biyaya ta zame mana dole, itace abu ta farko da zamu yi a matsayinmu na wa'inda ke karkashinsu, muna iya bijirewa duda irin tarin alkawarin salwantar da rayuwarmu da suka yi, haka kuma muna iya guduwa wajen da za'a iya hukunta su, ama muka zabi amincewar dan mu kamanta kyautatawa wanda ke kyautatawa talaka, ta hanyar amincewa ba dan mulkinsa ko arzikinsa ba, zamu mika ki bayan mun gama fada maki cewa duk rintsi gwara a tsire ki da ki aikata abinda suke bukata, watau kashe UMUGHLUK ITIFAL!"

Innalilahi wa inna ilaihi rajune, mahaifiyarta na magana ne, barin jikinta na ninkuwa ninkin ba ninkin, wanda ya tsoratar da su baki daya ama kuma ta ki dasa aya sai da ta kai karshen maganarta sannan ta dasa aya tana mai saka idannuwanta cikin na yarta wace girman idannuwanta suka karru , fuskarta har ta dauki ja dan rikicewa, haka kuma numfashinta ya wuce misali a irin gudun da yake yi, watau sama sama kamar zata bar duniya

Da kyar ta iya juyo kanta da ya mata nauyi ta kalli mahaifinta, sai kuma ta kalli Innarta wace kukanta ke shiga kunnenta

Tabas maganar nan ba wasa bace, tunda a yadda suka sakata a gaba suka yi mata da kukan Innarta kadai zai tabatar mata da ba maganar wasa a lamarin

A hankali ta sake duban mahaifinta da ya jimke hannunta da karfi dan ya hannata barin jikin da take yi

Idannuwanta na shigewa sunna budewa ta kalle shi , muryarta na rawa ta ce" Abannnnnn, abbannnnnnnah, kunna nufin nice za'a za'a yiwa aure da UMUGHLUK ITIFAL Na baban Garin Agadaz a matsayin wace zata je ta kashe shi?"

Mahaifinta ya girgiza kai da sauri ya ce" Ba zaki kashe shi ba Nadirahna, idan kin je ba zaki kashe shi ba domin ke ba azaluma bace, ke ba makashiya bace....."

"Abana , to ni ai ya mutun zan fi so Abana....., Abana ku ce min muna iya guduwa a yanzuma, domin ba zan taba iya kasancewa yadda ake so ba, Abana kun san da wanda nake so ko? Kuma kun son bana son rayuwar sarauta ko ta dakika guda ce ko?, Abana ku taimaka min ku ce min zabi gareni, dan zan iya ce maku ya mutun ba zai dameni ba da a kaini gidna sarauta!" Ta fada muryarta a mahaukacin raunane, hawaye na bale mata, haka kuma tana haki tan sakw kure fuskar mahaifinta d ido

Hankali tashe mahaifiyarta ta ce" Kina nufin, gwara ki kashe shi da ki je aure gidansa?"

A zabure ta zarro ido tana girgiza kanta, muryarta a raunane ta ce" Ba zan kashe shi ba, Innar birni da na kashe gwara a samu gawata, ina fata da na kashe gwara a wayi gari a samu gawata, ama idn ya mutun ni kam babu ruwana, innar birni ku ce min shikenan mu tatara mu koma LABA kun ji? In sha Allah ba zamu kuma dawowa birni bama kun ji inna?"

Mahaifiyarta ta ja numfashin samun dan kwonciyar hankali, dan har ga Allah ta tsorata da farko

Komawa ta yi ta jingina da jikin gado ta ce" Ki yi hakuri, ki mana biyaya, bana son jan magana ki je dakinki ki yi sallah ki fadawa Allah, idan har alkhairi ne Allah ya tabbatar, in ba alkhairi bane Allah ya kade ta hanyar da kowa zai ji dadin abin , ki tashi kawai ki tafi zamu sake zama gobe in sha Allah "

Da mamaki Mahaifinta da Hindu ke kallon Innar birni, amaa ta hade fuska tama daina kallonsu

Magana abanta ya so yi ama innar Birni ta bashi barin fuska ta kara hade fuska alamun bata son maganar

Hindu ta sake kallon NADIRAH dake cicibawa jikinta gaba daya sai bari yake har kanta ba a daidaice yake ba, sai zabura take yi, kana kallonta zaka gane magana take son yi ama tana tsoron innar Birni

Tana idasa mikewa ta juya zata fita sai ji suke dimmmmmmm ta dimu a kasa ba numfashi a tatare da ita

A haukace suke rige rigen karasawa inda take

Da tsawa mahaifinta ya tare hannun Innar Birni ya ce" Ki barta, kar ki tabata Fadima!, Ki barta haka kar ki idasa kashe min ita!, Dan ni ina sonta, ina son abina!, Ko menene bako yake a rayuwarta, idan kika yi duba da irin kulafurcinta da abin, kuma mun zo mata kai tsaye da abubuwan da a maganar gaskiya sun girmami tunaninta dole mu sasauta, na san idan bamu yi mata da gaske ba, ba zamu iya tankwasata ba, ama kuma komai yanada lokaci, a kan me tashi tsaye zaki fitar mata da komai kuma ki koreta? Ki tuna ke kika sab da rayuwar bauta ba ita ba, Fadimata ki tuna ke kika san irin haka ba ita ba, ita din bata rayu da haka ba, shi yaa bata zama inda muke , dan bata son ganninmu a yadda muke, shi yasa take tafiyarta a wajen da babu hasken lantarki, dan ta fi ganewa ta yi dire direnta a birni hankali kwonce da rikicin cikin gida!, A hankali zata shiga irin rayuwar nan ba tashi daya ba, so kike ta gujeki? So kike ta kulaceki? So kike abinfa muke so ta kiyaye dan kauna ta aikata dan kiyaya? Haba dan Allah, dan muna talakawa ba mahaukata muke ba Fadimata, sai da muka yarda cewa mun amince, idan baki amince ba a yanzuma ina iya fitar da mu, da mu saketa a birkice gwara mu gudu tare!, A kan me zaki ringa irin haka? Kin hanna innarta ta bita ta yadda ta saba binta, kin ce ba zata saurara ba, bayan na tabata da ita din ce ta mata hirar sai dai su sha koke kokensu zata dawo ta rarasheta!, Haba Zahrah da wane kike so na ji? Ke Hindu daukarta mu je dakinta, ke kuma kar na ga kafarki a nan!"

Rai bace suka tafi suka barta a nan tana tsugune, a hankali ta silale ta hade kanta da gwuiwarta ta fashe da kuka tana kai hannunta daidai kirjinta ta jimke da karfi , muryarta cen ciki ta ce"

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

1️⃣9️⃣

Ba edditing 😊😂

Muryarta cen ciki ta ce" Allah, kaine gatan bawa, mai kudi da talaka, sarki da bawa, Allah ga yarinyata nan, ka tankwasa min ita cikin ruwan sanyi, Allah kai ka fi kowa sannin irin halin da nake ciki, wannan daula da tunanin zamantowarta matar mutun mai daraja baya dadani da kasa, na fi tsoro da zulumi a cen kasan zuciyata, bana iya ci, bana iya sha , bana iya rintsawa, dan na san wacece yata, na kuma san zata kasance ne a filin da babu wargi, ya Ubangi ka mayar da bakin abu fari a tafiyar NADIRAH"............... (Amen innar birni)

A saman gadon dakinta Hindu ta shinfideta, jikinta na rawa a amshi ruwan da Abanta ya miko ta gumtsa a bakinta ta fesawa NADIRAH fesawar farko a fuskarta
Sai dai bata farka ba, hakan ya saka mahaifinta a rikice ya ce" Hindu ko ki dauketa mu tafi asibiti?, Hindu ta ki farkawa?"

Kai ta girgiza da sauri ta sake gumtsa da karfi ta fesa mata, wannan karron kam ta farka a rikice, sannan tana nan rarume rarume

Da sauri HINDU ta rukunkumeta a jikinta tana bubuga mata bayanta tana ambaton sunnanta da sanar mata cewa itace a tare da ita kar ta tayar da hankalinta
Chapter 28 · 0% Book details