Sashe 95
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya ya sauke, a sanyaye ya ce" In sha Allah, za'a fitar da su dukansu sati nan da zai kama a zartar da hukuncinsu"
A hankali ta dago tana kallon fuskarsa, muryarta a sanyaye ta ce" Kashe su za'a yi ?"
Fuskarta ya dan zubawa ido, sai kuma ya sauke yar ajiyar zuciya a hankali ya ce" Kina tsoron gani ne?"
Da sauri ta gyada kanta , hakan ya saka shi yin dan murmushi ya ce" Idan za'a yi, za'a shigar da ke, domin ya zama dole a ranar ki fito da shigar Alkyabarli, ke da yar uwarki, dan kuwa a gaban kowa za'a zartar, ama idan aka zo gabar mumunan hukunci wanda yake da rauni ba'a matsa masa kallo
Gaba daya sai ta ringa jin shayinsa, da tsoronsa a zuciyarta, wani girmansa da kiyayeshi ya rinha ratsata, a wannan daren du irin jarabarsa bai nemi komai a wajenta ba, itama bata gabatar masa da komai ba, dan ta kula lalle fa ya shiga lokaci na bukatar tunani da zuciyarsa
A washe gari cikin baban gida da zagaye, da cikin gari ya dauka na rufe UMMAN ASADEEK da ka yi
Kafin kace meye wannan Fada ta fara neman dinkewa da baki, sai da aka dakatar da ziyarar kowa , ba baba ba yaro, ba na kusa ba na nesa, haka kuma aka zuba masu tsaro a ko'ina, bama irin bangarensa da na HUZNAH , da na NADIRAH
A hankali kwanaki ke karatowa, har ranar da aka tsayar da gabatar da hukuncin nan ta zo
Tunda garin Allah ya waye baban fili na shara'a ya cika makil da al'uma, dan kuwa har daga wasu garuruwa an zo kallon shara'ar nan, manya manyan sarakunna kuwa daa kusoshin gwamnati sun zo dan halartar shara'ar, manyan alkalai na gwamnati da na musulunci sun zo dan summa a yi shari'ar nan da su, wace za'a yita da sanyin safiyar ranar, ya zamana wajen tuni ya dauki harama , jami'an tsaro na gwamnati da dogarai kuwa sai sake tsara wajen suke sunna daidaita tsaron wajen
Lokaci na yi ya zamana waje ya gama dinkewa, kusan kowa ya fito banda mai martaba da matansa, a ka'ida kuwa sai sun fito zai fito, ko kuwa su fito tare
A hankali suke tafe, bayan an basu damar fitowa daga bangarenta dan nufar na HUZNAH, wace tale uwar gida, ya zama wajibi sai sun je bangarenta sannan su fito tare, domin su din iyayen al'uma suke, babu wata rana da zasu fito gaban al'uma kawunnansu a watse, ko wace iri ce kuwa
Daga sama ta sauko, bayan an sanar mata tana iya saukowa sun karaso
Itama shigarta Alkyaba ce mai tsadar gaske, bambancin alkyabar nasu color ne kawai, bayanshi komai na alkyabar nasu su biyu iri daya ne, kasancewar mai shiryasu ta cikin gida ta shirya su ita ta dauko haka dan su saka
Tunda ta sauko, da farko yannayin fuskarta a dinke yake, du irin yadda ta yi yaki kar ta nuna kishinta da farko sai da ya falasata
Sai dai ga mamakinta, a yau, maimakun ta ji kalamai masu zafi da neman shiga hanci da kudundune daga bakin NADIRAH, sai ta ga bayan sun yi ido hudu na farko tana kare mata kallo, a na biyu sai ta ga ta sakar mata lalausan murmushi sannan ta wani irin risinar da dubanta tamkar sarauniya hanshakiya a tausashe ta furta" Barka da fitowa, Aunty"
Murmushi Auta ta yi ta dauke idannuwanta ta cira kanta, cike da wani irin takama da isa irin na jinnin dake yawo a jikinta, hamshakiyar yarinyar mace mai cike da gayu da jinnin sarauta a jinninta, wace take takama da ikon Allah da kuma yarda da amincewar miji ta dan sake sada dubanta kasa kasa ta furta" Barka da saukowa aunty........."
Sai kuma ta kalli NADIRAH dake dan kallon hanyar kicin tana ta danne damuwar dake ranta na tarin tsoron abinda zata iya ganni a yau, hasalima rabonta da mijinta kwana biyu cirrr yau, sai dai ya zo ya ganta a bangarenta ya rungumeta a jikinsa, ya kuma tafi, haka ko zuwan ya yi wani dari dari take kallonsa, gaba daya wani bako ne da take son sani a gabanta a yanzu
Tana murmushi ta mike tsaye ta ce" Momyn Autah mu tafi , auntyn ta sauko"
Ajiyar zuciya NADIRAH ta sauke ta muke itama, tana jan alkyabarta dan rufe dan karamin cikinta, wanda du wanda ya santa a da da irin lafafen cikinta idan ya ganta a yanzu kallo daya zai gane ta dauko , in kuwa manya ne masu baiwar sani sunna kallon fuskarta zasu gane tana da wata kama
A hankali ta koma wajen da aka nuna mata ta tsaya, HUZNAH kuwa ta dan sake zuba mata ido sannan ta daga kafa a hankali suka shiga takawa kowace da nata kalar izar sun saka Huznah a tsakiya har suka karaso wajen zamansu, suka zauna karkashin rumfar da ASADEEK zai zauna, wace an dai tanadeta ne ama ba asalin zaman zai yi ba dan baya zama sam idan yana shara'a
Mintuna ƙalilan tsakani aka shiga shelar fitowarsa
Gaba daya sai da tsigar jikinta ya tashi sakamakon gannin dukkan wani sarki ya mike yana kallon hanyar da zai fito
A hankali ta kai nata idannuwan itama bayan ta mike tsayen tana kallonsa
ASADEEK ne wannan
Mijinta ne ita yar HINDU
Shine ke tahowa tamkar dawisu
Shine yake doso su tamkar rana
Takama a cikin tafiyarsa, girma da daraja a tare da shi
Ya dauki rawani mai girman gaske, suturar jikinsa ta jinnin sarauta ta dauke idannuwan dukkan wani mai kallonsa, hannunsa rike da sanda irin ta saraki yana tafe da ita a nutse har ya karaso wajen sarakunann dake tsaitsaye cikin girmamawa ya gaishe da su, baban yaronsa wanda yake tafiya kasashen waje da shi yana ta faman gyara masa kayansa , SARKIN YANKA yana tsakiyar fili a tsaye, hannunsa rike da sharbebiyar wukarsa, wanda da yawa basa son kallonsa dan tsoro yake basu, SHEIK na gefen ASADEEK hannunsa rike da Alkur'ani mai girma da fari kal din carbi, cikin shiga ta manyan malaman adini ya nada hirama a saman kansa
Bai karasa wajen da zai tsaya ba sai da ya gama gaishe da kowa cikin mutuntawa sannan suka karasa wajen da zai tsaya ya yi tsaye yana kallon abun da yaronsa ke gyarawa wanda zai makala masa a kunnensa ya taho kusa da bakinsa dan idan ya yi magana kowa ya ji shi
Idannuwa ne suka sauka a kan motocin da suka ringa shigowa da masu laifi, hakan ya sa shima ya zuba nasa idannuwan har suka gama karasowa suka layu
Idannuwansa ya sada, a hankali ya rufe amsa amon yana kallon SHEIK, muryarsa a sanyaye ya ce" MAI DAMAGARAM ya zo taron nan?"
Sheikh ya amsa shi a tausashe yana kallon yannayinsa
A hankali ya ce" Ka taimaka, ka sanar masa cewa, shi zai zartar da hukuncin da ya dace a kanmu baki daya, domin ba zan iya magana mai tsayi ba, ba zan iya ba"
Sarkin Yanka dake ta shawagi ne ya kallo wajen, sai kuma ya dauke kai, dn jinkirin nan dama ya san da wahala idan har ASADEEK zai yarda da maganarsaa, ama ba komai a zartar dinma zai fi
Nan da nan aka kai bayani wajen Mai DAMAGARAM, wanda ya zubawa ASADEEK din ido shima, zuciyarsa na tsintsinkewa da tunanin da shine yaya zai ji?
Ba ja ya mike ya amsa gayatar nan ya karaso wajen da zai saurari komai tare da neman alfarmar duk wani sarki ya shiga lamarin dan a hadu a yi abinda ya dace
A lokacin aka ringa fitr da su baki dayansu
Da farko du a gigice suke kale kallen filin da jama'ar dake zagaye
Furucin aban Bahija ya saka su tsurewa summa a lokacin da ya furta" Shikenan, tamu kuma ta kare" yana kaiwa zaune ya sada kansa jikinsa gba daya na rawa tamkar mazari, a lokacin ne kuma ya'yansa da suka halarci taron suma suka rikice waje ya nemi hautsinewa
Da kyar aka iya daidaita wajen da iface iface da koke koke da rikicewar masu laifi , zan iya cewa saima da SARKIN yanka ya doso su rai bace Bahija ta zauna tana rukunkume mahaifiyarta tana tsagewa da kuka tana sake hango mutumen da ba zata taba manta fuskarsa ba domin sun hadu ne a saudiya da masoyinta, shin me ya kawo shi nan? Ina masoyin nata? Kar dai shima ya zo kallon shara'ar nan ce da sam ita bata daga mata hankali dan kuwa du tsuntsun da ya ja ruwa , ruwa ya dake shi malan!, Ama ba zata so ya ga haka ba dan ba zata so wani abu ya faru da soyayarsu ba, ko me zai faru da iyayenta ta san mai tsauri ne, domin ita bata san wasu abubuwan da suka aikata bama sai a rufe sun nan da aka yi, walahi idan ya kama zata fito ta fadi abinda ya faru , ba abinda ya sha mata kai, mahaifinta ya yi nisa, ita sai da ta dawo kwana a zaune kar aje ta yi barci ya kasheta itama, irin yadda abin duniya ya sayi zuciyarsa komai yana iya aikatawa
A hankali aka shiga gabatar da addu'a, kowa yana amsawa, SHEIK na zubo adu'o'i har ya kai karshe
A tausashe ya ce"
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```

*https://www.facebook.com/106494781436168/*
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
_FREE BOOK_
*Na*
*SAJIDA NIGER*
6️⃣9️⃣
A taisashe Sheik ya ce" Alhamdulilah, muna godiya ga Allah da ya nuna mana wannan rana, muna rokon ALLAH ya bamu ikon zartar da sha'ar nan bisa adalci, ya hannemu sin kanmu koda na second daya ne, ya kuma sasauta mana zukatanmu, ya sanyaya mana su , ya yafe mana kura kuranmu, alhamdulilah, zamu gabatar da abinda ya tara mu a nan dan kowa ya tafi uzurin gabansa"
Daga nan ya juya wajen Mai DAMAGARAM ya dan risina da girmamawa ya bashi waje ya koma gefe ya tsaya
Takardar daake hannunsa yake dubawa na tsayin lokaci, a kadan ya dauki mintunna ashirin yana yi, dan kuwa harka ce ta shara'a ba kawai zai hauta ba duda aikinsa ne