Sashe 44
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kiran yaron nasa ya shigo, nan yale sheda masa daga garin Tanut ne, harta da anguwar sai da ya sanar masa
Wayar ya tsurawa ido, still kirjinsa na dukan tara tara
A hankali ya lalubi number SHEIK
Wayar na fara ringin shima ya daga a kamilance ya yi masa salama da gaisar da shi
ASADEEK ya bude idannuwansa yana fadin" Da wa ka daura min aure ne Sheikh?"
Sheikh ya yi shiru dan bai fahimci hausar ba, sai kuma ya dan gyara zamansa ya ce" Da yar gidan Sarkin Tanut ko? NADIRAH wace ake yiwa kiranye da BAHIJA?"
Wara manyan idannuwansa ya yi, da karfi ya damki abin rufar gadonsa ya jimke yana rintse idannuwansa, hakan ya sa jijiyoyin jikinsa mikewa birde birde
Muryarsa a cinkushe ya ce" Karfe bakwai ina son ganninka a sashena in sha Allah"
Daga haka ya kashe wayar ya sake gyara tsayuwarsa yana ta aunawa, abinda yake ta korewa baya son kawowa ransa shine, Umma ce ja gabar auren nan fa, me hakan yake nufi? Umma ce fa?
...........( Uhum ).................
NADIRAH hankali kwonce ta bude bangarenta, watau baban kofarta ta shiga, domin ta hanya sak ta biyo tana salama a saman lebenta
Mikewar Umma kawai suka gani, sai saukar yan yatsunta biyar a saman kuncin NADIRAH, wanda hakan ya kusan gigitata, domin wani ihu ta saka wanda ya saka innarta zaburowa hankali tashe ta nufo wajen tana kama sunnan Nadirar da karfi
Umma ta nuno su gaba dayansu ranta bace ta ce" Wannan shirmen, da gidadancin, da kauyancin da kika yi yana daf da tashin hankalinki, da cire numfashinki, daga ke har iyayenki, domin ni nan da kika ganni ba zan taba daukan wahalarku ba walahi!, Me yake damun kwakwaluwarki? Ko mahaifinki ne kya masa wannan gaisuwar bale wanda ya fi shi daraja?, Ina ce an ce maki idan baki san abin fada ba ki yi shiru?, ASADEEK zaki duba ki ce masa barka da saukowa?, Yana saman kujera kina bakuwarsa zaki haye darr ko zauna?, Yana cikin fushi kike kallon idannuwansa?, Karya kike yar talakawa yar bayi! Karya kike idanma kina nufin ke baki iya bane!, Mu zaki kawowa shirme? Mu zaki kawowa maganar banza?, Idan har gangancinki ya haifar da rashin yarda sai dai ke ki kwana ciki, yanzu ki fada min bayan fitata me kika karra aikatawa na hauka?"
NADIRAH da ta fashe da kuka a jikin innarta, innarta ta dagota murya a shake ta ce" Ki kama min baki, ki min shiru, marin na waye baki sani ba?, Ki min shiru nace!"
Kukan nata ta ringa shanyewa, idannuwanta jajari ta kai dubanta kan Umma
Zata yi magana Innarta ta tareta tana rufe mata baki
Innarta ta dauke Umma ta yarfa da asakaran kallon da ya saka Umma zuba mata ido
Rai Bace HINDU ta ce"
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```

*https://www.facebook.com/106494781436168/*
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
_FREE BOOK_
*Na*
*SAJIDA NIGER*
3️⃣0️⃣
Rai bace Hindu ta ce" Mari? A fuska? Waje mai daraja? A kan laifin da ba'a koya mata laifi bane? Ita fa bata rayu cikin gida irin naku ba, a sake ta rayu fa, hakan bata san laifi bane ba fa!"
Umma ta sake zubawa yannayin Hindu ido, tabas ta karanci ranta a mugun bace yake, a yannayin da take magana tana dan bari zai tabatar maka tana hanna kanta wani abu mai girma ne
Umma ta sake kallonsu su dukansu sama da kasa, sai kuma ta juya ta fice ba tare da ta karra furta komai ba
HINDU ta juyo kan Nadirah, stilll ranta bace ta mata nuni da dakinta a kausashe ta ce" ki je ciki"
Nadirah ta juya jiki amace tana jin kamar fuskarta ta sundume ta shige dakin nata
HINDU ta tafi ta rufe falon ta dawo ranta a bugun bace ta ringa doka hannunta a kasa tana cije lebenta har sai da ta samu hawayen sannan ta hade kanta da gwuiwarta tana shashekar kuka
Wannan shine daidaikun kalubalen da y'arta ke iya fuskanta
Rayuwar rashin yanci
Wannan shine abinda ke iya zuwarwa Nadirah a ba zata , domin a tunaninta haka din abu ne marar tsauri, ba wani laifi ta aikata ba a tunaninta, idan har aka yi duba da wajen da ta tashi, za'a iya yi mata uzuri
Gannin ta kasa daina kukan zuciyarta na daci ya sakata shigewa ciki ta dannawa yayarta kira
Rai bace take labartawa Fadime abinda ya faru har zuwa marin
FADIME ta lumshe idannuwanta a sanyaye ta ce" HINDU, tsaya ki ji, a irin hukuncin da ya dace yarki mari an mata mai sauki, sannan kar ki ji wai, idan har ta yi sake ya gane tabas zai fito neman ba'asi da karin haske, domin abinda ta yi ba aiki bane na ƴaƴan sarauta"
HINDU ta ce" Aunty, ama kina tune, abinda aka koya mata an koya mata gaisuwa? Ko ta yi zaman da zata ga yadda kike yi? Ba ita ba, nima fa ban iya ba"
Fadime ta ce" Haka ne, ama abinda nake so da ku baki daya shine, yanzu ya dace ku zauna ku karanci damuwarku, ku samawa kanku mafita, kar ku ringa manta abinda ya sakamu shiga bakin kura mana, ya dace ta aro halayan yayan sarakan koda bata sansu ba, ya dace a yanzu ta koyi kamantawa, in sha Allah da safe zan mata dogon kwatance na gaisuwarsa, dole ne ta bi dan gudun tonuwar asorinmu baki daya kin ji Innarta?"
HINDU ta gyada kai bata ce komai ba
Fadime ta ce" Ki daina kukan haka, ke da zaki karfafeta, Mari ai da sauki a kan abinda take iya samu matsayin hukunci, ta yi garaje Innarta, ba'a haka, ai Allah ne ya nada sarki kuma yace a yi masa biyaya ko?"
HINDU ta gyada kai, a hankali ta ce" Kuma Allah ne ya halata wasa tsakanin miji da mata, ya halata sakewa da hira tsakanin miji da mata, wace ta zarce tsakanin kowa, bai bambance cewa matan sarakai kar su yi irin haka a tsakaninsu ba ko?"
"HINDU, kar ki manta tsakanin da abinda ke boye, " Fadime ta fada
Hindu ta ce" Shinema abinda ya fi sakani gannin idan yata ta kula alaka ta sabo da shi, zai zo mana da sauki, ina gannin a yadda ake zuzuta daukan mataki a kan laifi a wajensa ta fito da gala mai girma tunda bai dauka a kanta ba, Aunty sabo yana da dadi"
FADIME ta ce" Haka ne, ama ta iya takun rawarta, kar ta bata ta da tsale, ta iya kame bakinta kar a yi mata kallon wace tale da sakin kai da halaya irin na yan gajaliya, ta kasamce mai taushi dan mace take, uwa uba kar tace zata takaita tafiyar dan zuwa ta yi ta koma, babu abinda ya gagari yarki, kin sani sarai, idan har ta saka gagawa ko raini a ciki, zata sa a gane da wuri a daura mata laifin komai da komai, bayan ita laifinta daya ne tak a tafiyar nan, yiwa iyayenta biyaya"
A sanyaye HINDU ta amsata, suka ci gaba fa zantawa, a yau din Fadime din da kanta tace lalle tana so HINDU ta fan karra zama kadan, ba dan komai na, sai dan ta wanke kanta, abinda NADIRAH zata fara da shi dan wanke kanta shine aikawa da sakon zata ziyarci kishiyarta, daga nan idan sun je ta nemi alfarmar ta mata rakiya ta ba UMUGHLUK ITIBEL hakuri domin rashin lafiya ta dakata yin wasu abubuwa mararsa dadi, harta abinda ya dace ta fadi a gaban UMUGHLUK ITIBEL FADIME tana ta sanarwa HINDU, har dai ta dan fahimci wasu abubuwan sannan suka yi salama
____________________________________
Washe gari daga masalaci yana dawowa ya shige ciki ya kimtsa sannan ya sauko dan ganawa da SHEIK
Umarni ya bada kan kar wanda ya shigo, yana da bako
Sheikh dai kallonsa yake yi, dan ya fuskanci ko barcin kirki bai samu ba
A nutse ya dubi SHEIK ya ce" Yarinyar da suka aura min, ba wace na sani bace"
A nutse Sheik ya dake fuskantarsa, a hankali ya ce" Bam fahimta ba, Allah ya taimakeka"
"Ina nufin wace aka ce da kai itace Bahija, ba ita bace" ya bashi amsa yana dan hade hannayensa
Sheikh ya dake dubansa da mamaki ya ce"Ban fa fahimci yarenka ba, Allah ya karra maka lafiya"
ASADEEK ya ce" Abinda kake ji shi nake nufi, ita yarinyar ta wajensu mun yi tafiya da ita Haji, na ganta, na kuma santa,wace na gani jiya ba ita bace"
Gaban Sheik sai da ya fadi dan abin wani iri ya ji, ya gyara zamansa shima da kyau ya ce" Wannan wace irin magana ce, gaba daya na kasa gane inda ta dosa, ba ita bace? Wacece? Me hakan yake nufi? Yaya aka yi ka iya ganewa cewa ba ita bace kai da baka yiwa mutun kallon tsaf?, Mahaifinta fa ya jadada min cewa ita ce, sunnanta na kirki ne NADIRAH, ama ana mata kiranye da Bahija a lokacin da na tambayeshi dama Bahija sunnanta NADIRAH? Duba da ka sanar min sunnan yarinyar"
Komawa ya yi ya zauna da kyau yana lumshe idannuwansa, ya jima a haka sannan yaa sake budar bakinsa a nutse ya ce" Idanma wacece wamcen, wata ce daban, wace ba Bahijar ba, domin bahijar a yanzu haka tana Tanut, wannan kuwa zan iya ce maka kamar ba yar cikin gida bama, dan ta fi kama da yar fashi!"
A zaburw Sheikh ya sake dubansa da yannayi na mugun mamakin sunnan da ya hada yarinyar da ita
Bakinsa har yana hadewa ya ce" Subahanalah yar fashi kuma?"
ASADEEK ya gyada kansa, sannan ya nunawa SHEIK wajen kujerar da yake zaune ya ce" Ka ga a nan, a nan ta kalleni shekeke tace min sannu da saukowa,wai sannu da saukowa, ko daga ina? Kamar ta sha kwaya a lokacin dan na kula tana ta layi, sai da aka rufa mata alkyaba fa, kowa na duke yarinyar tsayina da nata a laye, inaga in ba yar fashi ba to bata da hankali"