Sashe 63
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushin ya yi mata shima yana sake kallon yadda fuskarta ke kawatuwa da farin ciki, ya dora hannunsa ya tura mata jug din gabanta kasa kasa ya ce" Da ke, da du wani mai shanye min ga naku"
Wannan karron daria ta yi harda dora hannunta saman bakinta cike da mamakinsa, gashi ya yi maganar kasa kasa, kuma ya gimtse kamar ba shi ba, dariarta kadai ta saka su zuba mata ido su dukansu ukun, Huznah da mamakin wai Auta ce ke daria?, Umma gananta ya fadi tana sakw duban Auta zuciyarta na shiga a uku da gannin daria ne take yi? Na menene? , NADIRAH kuwa ta zuba mata ido tana kallon dariar tata wace ta sakata jin kamar zata saki murmushi domin kana kallo zaka ga abinda ya sakata dariar mai girma ne a zuciyarta
Hannunta ta cire wanda ke tare a gaban hancinta zata duba ta ga ko menene
Da sauri ta zarro ido tana mikewa tsaye hakama Auta fa sauri ta furta" Subahanalah aunty Jinni ne?"
Ihu NADIRAH ta saka ta tataro hijabin nata gaba daya ta cireshi tana karra saka ihu tana fadin" Na mutu jinni wayo Innata jinni, wayo jinni na mutu daga ina yake fitowa?........."
Sumurta kokowa take yi da kanta tana cire hijabin gaba dayansa ta bayana daga ita sai zani daban riga dabsn, rigar mai siririn hannu, zannin kuwa ta masa wani dauri a cen saman gwuiwarta gashin kanta a daure a tsakiya ta ringa kai hannunta tana shafowa ta karra kwala ihu tana fadin" Na shiga uku Habo ne, walahi habo ne nake yi............................"
Mutun biyu suka zabura suka nufota watau Auta da Umma, HUZNAH kuwa ta rafka tagumi tana tunanin anya tunda yarinyar nan ta fara cin abinci da su an taba zama aka wanye lafiya?, Shi kuma a hankali ya jingina da jikin royal kujerar ya zuba mata ido yadda take sumurtu tana kwala ihu tana gudu ta ki tsayawa bale su Umman su iya riketa karra fadi Take yi INNATA HABO NAKE YI
A zabure ya mike tsaye daga zaunen da ya yi a lokacin da ya ga tsutsar kan nata zata izata waje a haka
Taku uku ya yi a hanzarce ya damki hannunta na dama ya janyota gabansa sosai yana son dago fuskarta ama ta ki yarda da hakan sai zunduma ihu take tana a taimaketa habo take yi
Umma dake fadin" BAHIJA ki saurara mana, tsaya a duba mana, ki daina dukar da kanki ba zai tsaya ba" ya duba a hankali ya furta" Umma, je ki ci abincin bara na wanke mata"
Da mamaki Umman ta dakata da son rikotan tana kallon yadda ya saka hannunsa ya cicibata gaba dayanta ya dora a kafadarsa ya juya ya nufi hanyar sama da ita a lokacin kuwa bakinta fadi yake" Umma amsoni, umma dan Allah amsoni, UMMA kar ya tafi da ni, UMMA ki amsoni"
Sunna tsaye kamar a summe su biyun haka matarsa na tsaye a gaban abincin tana hangensu har ya bacewa ganninsu sannan Umma ta juyo tana sake zarro idannuwanta sai idannuwan nata suka sauka a kan HUZNAH da ta yi wani iri kamar zata fashe da kuka tsabar hankalinta a tashe yake
Dan murmushi ta samu kanta da saki, tabas idan har ta yi la'akari da maganar da yarinyar ke fada mata cewa ta barta ta yi aikinta yadda ya dace ya dace ta bartan, domin idan har hakan ne tabas yarinyar zata yi gagawar kaisu ga ci a mafarkin su, dan haka bara ta jefi tsuntsu biyu da jifa daya ta hanyar gumawa matarsa ta kasheta da kutu
Zama ta yi saman kujera ta sake janyo abincin ta saka cokalinta hankali kwonce ta sake kallon HUZNAH dake kallon hanyar da ya bi da NADIRAH ta yi murmushi ta ce" ki zauna mana Gimbiya?"
Gabann HUZNAH sai da ya karra faduwa, a hankali ta juyo tana kallon Umma
Gimshewa ta yi tana kokarin boye damuwar dake shinfide a saman fuskarta ta zauna tana kokarin ci gaba da cin abincin
Umma ta sake yin murmushi tana hangen Auta ta tafi falo ta zauna a ranta ta yi kwafa, a bayyane kuwa ta ce" Kin san ita fa mace, mai sunna mace bama sai ta zuba leshen daruruwa ta maka hodo a fuska ba ake kallonta, kuma ba zaki taba ganninta tana fadanci dan a dubeta ba, ita fa mace ginaniyar mace tana zamanta a daki za'a zo a roki alfarmarta, a rarasheta, a roketa ta amshi kudade sannan a kireta gimbiya........, Ita mace mai daraja ba ita ke roka ba, kuma walahi namiji ko ya ki ko ya so dole ya bata kudi da katsayi dan cencenta ce abin ai"
Sosai maganar ta soki zuciyar HUZNAH, kanta a kasa yake tana ta sake danne zuciyarta dan kar ta yi abinda ba shi ba, ama sai ta ji ta kasa, , ba zaku gane bane, abinda ya shafi mijinta na fin karfinta, du yadda zata yi dan ta kaucewa abin sai ya zo ya zame mata damuwa, domin yana fin karfinta ne sosai, bata san yaya aka yi abin nan yake neman cin mata ba, abinda ta sani shine lalle an soketa a wajen da bata iya hakuri
A hankali ta dago tana kallon fuskar Umma, Umma dai fara ce, ama a idannuwanta ganninta take yi tamkar kumurci bakin maciji mai bakin kwali
Gana daya matar babu fara'a ko annuri a fuskarta sai tarin bakin fencin dake bayana a koda yaushe a tatare da ita
A sanyaye ta ce" Hakane, kowace mace da irin tsarin rayuwarta, matar si dinma ai kala daban daban ce, wata macen wanda zai dubeta da maganar so dinma bata samu , komai matsayin da take gannin ta taka a duniya, komai girmanta da arzikinta sai ki ga ta koma ga ubangijinta a haka..................."
Ta ajiye maganar a hankali tana cakular abincin
Umma ta kureta da ido cike da mamaki, muryarta na cenzawa ta ce" HUZNAH nice zaki yiwa rashin kunya?, Nice zaki zaga?"
HUZNAH ta sake dubanta itama ta ce" Ba maganar zagi, magana ce ta rike mutunci, idan har kin yi komai wulakantani da zaki yi zan jure, in kuwa ba haka ba kina iya gannin ba daidai ba Umma, akoy jifan da idan aka yi min bana iya hakura, shine wanda ya danganci mijina, ina son abina, zan kuma rayu da kayana a kowani hali!"
Umma ta tabe baki, sai kuma ta yi murmushi tna yin kwafa ta ce" Hakane kuma, maganarma da kika yi gaskiya kika fada, wata macen kuwa yadda ta zo haka take komawa, ga mijinma a gefenta ama kuma ba wani katabus sai bakin ciki?"
Daga haka ta mike tana kallon abuncin a raine ta ce" Kin amshi kicin kuna ta faman hadamu da kayan fulawa, ya dace ki yiwa kanki fada ki kuma ba mai waje wajenta ta huta, koda yake kamaninki kamanin ta kicin ce, Gimbiya kuwa sai kafadar UMUGHLUK ITIBEL!"
Tafiyarta ta yi cike da gadara, tana zuwa falo ta tsaya gaban Auta wace ke zaune tsuru tana ta addu'a a ranta
Kasa da sama ta kalleta ta watsar ta ja tsaki sannan ta ce" Ki ci gaba da take dokata, ke kin san wacece ni, kin san na yarda da maganar ba zan hada maki sharin kina kwana da mace bane dan kina min biyaya, ki yarda ki take dokata sai na baki magani kin bugu sannan na tura yarinyar da zata yi maki zigidir ta gama abinda take so da ke ta kuma yi kukan kin afka mata, ai jaraba gadon gidanku ne, ko shi yayan naki na san a hannu yake kwana da wutsiya yana ihun a bashi mace ya farwa, sai dai kuwa ya mutu ba shi ba jin dadin mace!"
Daga nanma ta fice ta bar Auta jikinta na rawa tana kallon hanyar da ta bi
Zaunawa HUZNAH ta yi a gefenta tana kallonta, sai take gannin kamar da hankalinta,
A hankali Auta ta dubeta, sai kuma ta janye dubanta tana ta Adu'ar tana jin nutsuwa na ratsata sanadiyar ambaton Allah
A hankali HUZNAH ta sake duban hanyar sai kuma ta sauke ajiyar zuciya kasa kasa ta furta" Allah ya yi mana maganinta!"
Surmiyowa take son yi ama ko alamu ta kasa har ya karasa bayi ya bude da hannunsa daya ya shiga da ita ya karasa gaban ruwa ya dauko kan pampo mai igiya ya dan danna shi a hankali ya shiga wanke mata bayan ya tareta da kafarsa daya ya hannata zugawa da gudu
Fuskar ya wanke sosai sannan ya kamata a nutse ya dan dage kan yana dan sake tareta a jikinsa kasa kasa ya ce" Ke kam ki tsaya mana"
NADIRAH ta rintse idannuwanta sakamakon hucin numfashinsa dake sauka a fuskarta
Muryarta a raunane ta ce" Ka barni mana kaima menene haka?"
Fuskar tata ya zubawa ido yana ta kallonta, a haka din ya ce" Ba zan iya barinki ba"
Baki ta turo tana gungunnin da ya sakashi zubawa fuskar ido cike da mamaki yana son dole dole sai ya ji abinda take fada, ama ya kasa ji
Wanda ya dan taho ya kanjace ya tare hanyar ya dan goge mata sannan ya dago kan nata
Gannin zata dukar da kan ya saka hannunsa ya dago fuskarta yana kallonta ido cikin ido ya ce" Me yasa zaki dukar da kanki bayan na sani kema kuma kin san ba tsorona kike ji ba?"
Ido ta warro a saman fuskarsa sai kuma ta sake turo baki ta ce" To ka dan matsa mana ka matsen waje baka gani?"
Bakinsa ya dan tabe ya ki katsawar, hasalima rawaninsa ya shiga saukewa hakan ya saka gabanta faduwa tana kallon hanyar fita sannan tana kallonsa a sace tana dan matsa kafarta a dabarance har ya sauke rawanin ya rataya shi jikin abin shanya sannan ya fara yin gaba ya fito a bayin ya tsaya yana kallo ta fito ta nemi zagayeshi sumui sumui zata fice kasa kasa ya ce" Yaya aka yi jiya baki dawo ba?"
Turus ta yi tana jin wani haushi haushi na turnuketa
Juyowa ta yi a hankali tana dubansa , ta samu kanta da fadin" Me zan yi maka idan na zo ni kuma?"