← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 99

Sashe 41

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya ta yi har sai da jerarun hakoranta suka bayana sannan ta mike ta koma dan kusa da shi kadan da hannunta ta shiga nunawa ta ce" Abah, kana tune da labarin Papah da Anna?, Papah yace a gaban dogarai da fadawa nake saba babar riga na kai gaisuwa dan idan ta kiya tsaf zata ce ai itama mutun ce kulun kulun sai dai ita ta wani zo ta gaisheni?"

Rawanin da bai sauke ba ya samu kansa da yi masa kasa sosai har habarsa ta bayana, Dariyar da kanwarsa ke yi da tsohon tarihin da ta tuno ya daka shi jin kamar numfashi ya masa kadan dan farin ciki

A hankali ya saki lalausan murmushi, domun ya gane da me take hada zancen, sai kuma ya dan karra kure fuskarta da ido kasa kasa ya ce" Auta, ita fa ai ba irin na su Aba bane ba fa"

Auta ta dafe habarta ta ce " Abah, sakon naan daga wifey dinka ne, Allah ma ko"

Ido ya zarro da mamaki ya ce" Noh,kar ki rantse Auta"

Auta ta sake sakin yar dariyar da ta saka Yayanta lumshe idannuwansa yana mai godiya ga Allah, uwa uba ya shiga tunnanin kennan akoy sauran dariya irin haka a tare da ita?, Ya Allah kennan tana da sauran tarihi a zuciyarta da kwakwaluwarta? Kennan kanwarsa bata shige cikin duhu gaba dayanta ba da sauranta?

Auta ta kara dubansa ta ce" Abah, ka bada dama a kawota gobe sai mu gani ka ji? Please Abahna ni ina soma na ganta plz"

Idannuwansa ya kankance, sai kuma ya gyada kai yana murmushi ya ce" Me yasa kika damu haka Auta bayan baki santa bama?" Ya yi tambayar ne dan ya gane idan har ba kanwarsa na neman shakuwa da abar da yake da takaitacen zama da ita a zuciyarsa

Auta ta yi murmushi ta ce" Abah, ina son mutun mai karfin zuciya, mai courage, in dai daga ita sakon nan ya fito nima ina saka ran wata rana na yi karfin zuciyarta, Abah Kaine UMUGHLUK ITIBEL sunnan da talaka ya baka , kuma sarakai suka amsa, ba kai ka sakawa kanka dan isa da fin karfi ba, du wanda ya aiko maka da sakon nan, ko ita, ko ba ita ba i swear ina son ganninsa Abahna"

Murmushi ya yi shima, sosai mamakinta na neman hanna shi yin abinda yake yi,

Idan har zai tuna rabonsa da gannin haka daga Auta gaskiya an jima, irin mugun jimawar nan, murmushinta kansa sai a jima bata yi ba, bale dariya? Kai ko hira ake yi sai ka ga kamar bata san me ake cewa ba, ashe tana iya doguwar magana har haka hankali Kwonce?, Shima sai ya samu kansa da son yi mata abinda take so din, dan haka cikin nutsuwa ya ce" Ohk ohk, zaki gani yarinya da ba ita ta bada sakon nan ba, zaki gani, ama ba gobe ba, gobe da jibi inada zama a fadamai tsanani, inada Shari'a masu tsaurin gaske da rikici a ciki, in sha Allah ranar asabar alhamis sai mi zauna one 12 mu ci abinci tare?"

Da farin ciki Auta ta amsa har ta karra bashi wani mamakin ta ce" zaka cire Rawaninka?"

Da mamaki ya dubeta ya ce "

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

2️⃣8️⃣

Da mamaki ya dubeta ya ce" Me ya kawo maganar cire rawani kuma?"

Auta ta shagwabe fuska ta ce" Please Abah, idan ka yi haka zan ji dadi sosai fa?"

Murmushi ya yi ya mike yana fadin" Oya maza miko ki yi hardar na raka ki dare na yi fa"

Ajiyar zuciya ta sauke ta dauko ta mika masa sannan ta gabatar masa da hardar shi kuwa yana sauraronta har ta gama

Yana murmushi ya nuna mata hanyar da zasu bi ya rakatan sannan suka dauki hanya

Har suka karasa kowane na tunani a zuciyarsa

Shi yana mai karra godewa Allah da tunanin ai idan hakaa ta ci gaba da samuwa tsaf zai mayar da ita wajen mijinta, sauki ya samu Masha Allah, dama a gaban Umma ta yi hirar nan a sake, da Umma ta ji dadi aa ranta

Auta kuwa sunna tafe tana tunani kamar haka' shikenan kai ba zaka bude fuska ba sai kaa yarda da mutun? Na ga ai itama matarka ce, maganar yarda kuma ai ya kare ko?, Abah ban santa ba, hasalima ian tsoron iyayenta domin nice kat cewa summa da wani saka hannunsu a lamarinka, amaa haka kawai tunda akaa ce an daura aurenku nske zumudin son ganninta, ko dan zamu karru ne a cikin duniyarka? Ko dan zan kara samun wata yar uwar ne bayan HUZNAH, sam ba wai ina sonta dan na kuntatawa Huznah bane, ko daya, hasalima HUZNAH ni babu abinda ta min, yannayin mu'amalarmu ne haka, wani lokacin har hira muke yi fa, ama da wata zata karu cikinmu sai nake jin farin ciki sosai, sai maganar da aka fada , na tabata bayin masarautarmu ba dai maganar su ringa kawo karya ba, wannan Umma bata samu galaba a kansu ta wannan fannin ba, du inda maganar nan ta fitoz da tushenta, tushsen nake son gani ni kuma'

Har kofar dakinta ya rakata sannan ya koma ta hanyar da suka biyo bangarensa ya ci gaba da aikinsa yana sake rubuta hukunce hukunce ne na sata, da zina, uwa uba Luwadi .......................shara'ar dake gabansa mai zafi ce, kuma mai cakulewa ce, a dole Sheikh ya kawo masa su dan shi kadai ya isa ya tsaya ido cikin ido ya zartar kuma a bi koda ba'a sallah!

A ranar HINDU bata zauna da yarta ba sai washe gari, tana tsakar yi mata nasiha Kira ya shigo a wayarsu

Tana gannin yayarta ce ta tashi tana murmushi ta shige ciki dan su yi sirri

FADIME a sanyaye ta ce" Hindu kin kaura ba?"

HINDU ta yi shiru

FADIME ta ce" Ki tataro ki dawo dakinki kin ji abinda na fada maki, kina nan ko bakya nan abinda Allah ya nufa zai samu yarki sai ya sameta, kar ki yi wasa da aurenki mana"

HINDU ta gyara zama ta ce" Aunty ba wasa nake yi da auren ba, dama dan Habu baya nan ne, kuma kin ga jiya dai Indi cewa ta yi a cewa UMUGHLUK sai wani jikon zata je gaishe shi"

Ai kuwa rikicewar da Fadime din ta yi har ta zarce ta HINDU, haka take salalami itama ta saka aka ba NADIRAH wayar, kamar zata fito ta wayar haka take yi, fadi take tana maimaitawa cewa Babansu ne fa, a kan me zata yi aiki kamar na yar kwaya? Tsaf suka karra sileta, ita kuma ta yi shiru, dan a ranta ayanawa take yi' Ba ku gane komai bama yaya da kanwarta gaskiya, ni ba zan fara kai kaina ba fa, yo ai ba haka ake yi ba'!

Haka suka wuni sunna yan abubuwansu dan debe kewa, sai dai kowace zaman dakan ya fara isarta, domin ba sabawa suka yi ba gaba dayansu

A haka har kwanaki biyun suka shige, a ranar na ukun ne sabuwar maganar zuwa bangarensa ta karra tashi, wannan karron kam ta ga da gasken gaske suke,

Tun karfe goma aka shiryata akace cin abincin rana a bangarensa
Kwata kwata sai ta ga abin nan ba wani tsari sai shirme

Bata dai ce komai ba , haka ta zuba ido tana bin motsin kowa har lokacin ya yi aka rufa mata wata mahaukaciyar alkyabar da ita da kanta sai da ta ringa shafata, domin har ga Allah ba dai laushi daa kyau ba

A nutse aka bude hanyar baya domin rana ne gatse gatse da nufin bi ta bayan da ita,

Sun dauko tafia su hudu Umma sai karra gyarata take yi tana sake gyara mata rufarta ta ja ta tsaya

A hankali ta nemi dukewa, hakan ya saka jakadiya tareta da sauri ana faman ambaton Allah da yi mata sannu

Ido rintse ta kwashi barin jikin karya kab kab kab kamar da gaske

Hankalin Umma tashe take talabota tana tambayar menene? Lafiya? Ama NADIRAH ta kasa fadin komai

Hankali tashe Umma ta sake dagota tana girgizata ta ambaci sunnanta tana tambayarta menene?

Muryarta na rawa ta furta" Umma, bayi nake son shiga, innalilahi zai bale"

Har ga Allah Umma ta yarda, haka kuma da mahaukacin gudu ta saka aka juya da NADIRAH aka nufi ciki da ita hankali tashe aka nufi dakinta da ita Inna naa tambayar lafiya?

Bayin ta shige bayan ta watso alkyabar ta ja ta rufe ta haye saman abin aikin ta ringa jan ruwan tana kakari kamar wace ke aikata aikin da ba jira😌

A waje Umma da inna ke kai kawo ana tambayarta yaya da sauki? Tana buga gyaran murya

Umma ta dubi Inna hankali tashe ta ce" Sai fa mun yi da gaske, kar aje kishiyar ke son cin mata, kina ga haduwa ta gagara bayan an daura aure ba yau ba?, Kar fa aje mun raina wayonta ita tana mana kallon shashashu, kar aje wankin hula ya kaimu dare, kar aje ta san me muke shiryawa tana neman yi mana sakiyar da ba ruwa, ina zuwa zan je na sanar masu abinda yake faruwa sannan na fita da kaina na kawo jikakun karya tambaya da kaikayi koma kan mashekiya, ko me ta aikata mata sai dai ya koma kanta walahi, wannan wace irin masifa ce, ki duba ki ga kwaliyar da yarinyar nan ta sha fa? Ai karya take idan takamarta bokaye ni a hanya na kwana dan ubanta!"
Chapter 41 · 0% Book details