Sashe 47
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai ta girgiza tanaiwa idannuwanta wani irin warrrr sannan ta dan yatsine fuskarta ta ce" Kin san menene burina?, Burina na gama abinda ya kawo ni gidan nan, na smau yancina, burina na aikata aikin da ake so na aikata na kama gabana, domin a waje inada rayuwata wace nake matukar son na ga na cika, ni nan da kika ganni burina na yi kudi na gagara, ai ba laifi bane ba kuma haramun bane yar kauye ta yi buri da mafarki ko? Ina iya ranste maki a kan kudi komai sai na aikata, wani yardar tawama dan na tabata za'a bani wani dan abin ko yayane na je na ja jari, ba kowa rayuwa take tafiyarwa ba a cikin daula kin fahimta? Ki yi hakuri zaki ji maganata wata iri kamar na raina ki, aa ba raini bane, kin daga hannu kin mareni ido da ido, ba'a yi min haka, ki sani da ba dan na san jakarki da nauyi ba da sai na maida maki goman wanda kika yi min!" NADIRAH ta ajiye maganar, da wani yannayi da ya saka innarta dagowa tana kallonta, domin tamkar wata rikakiyar yar daba ko irin rikakun yan barikin nan
Ita da kanta Ummar shan jinnin jikinta ta yi, a lokacin abu daya ke ranta shine bata kyauta ba da har ta kai hannunta fuskar NADIRAH, ashe yarinyar tanada mafarki nata na kanta, gaskiya ne mai yawo a cikin mafarkin kudi ko mulki baya tsoron kowa, baya tsoron komai, a mutu ko a yi rai du ba shi bane a gabansa in dai yana irgen ta ina kudi zasu shigo
Lalle ta yarda yarinyar na iya aikata masu aikinsu, ama duda haka bata ga dalilin da zai saka ta je bangaren HUZNAH ba, har maganar nan ta fito fili haka ba gaskiya
Umma ta dan dubi Inna, sai kuma ta sake kallon NADIRAH, ta dan rage gautsin Muryarta ta ce" Kema kin san marin nan dan raina a sama ne, ni na mareki ama ni na ji a zuciyata"
Ta idasa tana mai dora hannunta daidai zuciyar tata
A dole NADIRAH ta kalli innarta, da sauri kuma ta kalli Umma
Umma ta ce" Ama kawai ki yi hakuri, ba za'a kuma ba, yanzu ki fada min me kuka tatauna da wancen ne?"
Tabe baki NADIRAH ta yi, sai kuma ta cirw kanta ta ce" idan ta hanyar da nake tunanin za'a bani aikina a gidan nan ne na yi sharar fage, dan ya zamto an samu abinda ake so ba da labe labe ba, dan kuwa in ban samu hanyar yi masa girki ba, hakan ba zai tana samuwa da sauki ba, ina fata kina gane yarena"
Wani irin farin ciki ne ya ratsa Umma
Har ta rasa me zata ce a irin wannan lokacin
Kiran dake ta shigowa ya sakata mikewa ta masu alamun sai ta dawo ta fice domin a cen kicin din ne ale ta kiranta,
Kai tsaye ta je, tana jin ba'asin kiran ga mamakin HUZNAH sai Ummar ta bata damar dafawar hankali Kwonce, duda dan abin da ta saba sakawa a irin abincin auta yai ba zata saka ba kennan? Ama zata yi hakuri har gobe Girkin NADIRAH
A dakin NADIRAH
Umma na fita Innart ta dubeta, da duba irin na karra son gane gaskiyar lamari
Sai kuma ta sauke numfashi ta ce" haka nake so, ina matukar son idan kina magana ya zamto tana sauraronki, dan karfin muryarki ya fi nata zafi?, Haka kuma ina fatan Allah ya nuna min ranar da zan rama marin nan, walahi ko ana ruwan mazuru da zaho sai na zabga mata mari in sha Allah, Kwartuwar bamz da wofi, wai zuciya, ina ta ga zuciya wancen?"
NADIRAH ta yi murmushi ta zauna tana tunanin idan har hakarta ta cimma ruwa, matarsa zata amshi girkinsa, hakan na nufin za'a rage wata jarabar, idan kuma an kawo maganin da za'a zuba masa a abinci hakan na nufin ita za'a ba ta zuba, ba Umma bace zata zuba abincin ita kuma a bata ta kai masa!, Ko ba komai Abam su Inna za'a dan karra kwanakin shiruftaka bawan Allah!...............
Kusan sallar magarib takarda ta sameta ta gayata cin abinci, wanda a kusa kusan nan Umma ta fada masu da wahala ta sake samun zuwa falon UMUGHLUK ITIBEL sai idan ya huce
Murmushi kawai ta yi ta ajiye abin tana sake karantar girman girmama abu irin na gidan sarauta, zo ki ci tuwo ne aka buga a computer? Watau tvn nasara? Allah shi kyauta
Da dare ya yi sai da larfe takwas din ta kusa ta shige wanka, a nutse ta fito ta bude tarin kayan dake sakata nishadi idan tana kallonsu ta zaro wata doguwar riga irin ta kantin nan ta zaman cikin dakin nan mai laushi mai ruwan fatar kare ta ajiye, sannan ta dauko pant shima fari kal shi kuwa ta ajiye
Bangaren alkyaba ta bude ta zuba masu ido
A hankali ta dora hannunta ta ringa shafasu tana kare masu kallo
A kalla zasu kai talatin ko fi a irgenta,haka kuma kowace da irin yannayinta, watau da tsarinta da kyanta da komai
Ajiyar zuciya ta sake saukewa a hankali ta janyo wata mai ruwan gashin mage, laushinta da dukan da ta yiwa kirjinta ya dakata daukota domin tana kallonta sai da ta ji ta sace zuciyarta, haka kuma tana daukota a hannunta ta ji wani laushinta sai da ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya
A hankali ta karasa wajen abin turaren wuta ta dauki abin kyastawar ta ciro ta kyasta daya ta dora ta dan dakata ya kama sosai har ya fara zama toka toka kadan , sannan ta je ta ciro turaran wutar na kaya ta zuba ta loda kayan
Wajen madubi ta karasa ta tsaya cike da tunanin me ya dace ta yi?
A hankali ta zauna tana dan dora hannunta sama ta shiga tuna maganarta da matar dake koya mata yannayi da lamura irin na sarauta
A hankali ta maimaita kalmar da take yawan fadi da yaren nasara, watau CLASSSSS
Hannunta ta dan bi da kallo sai kuma ta saki gashin kanta ta dan wana kanta kadan ta sake zubawa madubi ido
Cikar gashin da bakinsa yanada yawa sosai, ya ishi bawa kwaliya ko wace iri ce , cen dama ta gaji iya kwaliya da gashinta, kitso ne bata so sai sun sha rikici da innarta take yi mata tafka tafka biyu, ko hudu
A nutse ta saka abin tsaga daga gefen hagu na gashin kadan ta yi tsaga mai dan tsayi kadan ta ja gashin gefe sannan ta saka macaji karami a hankali ta ringa caje wanda bashi da yawan har ya kwonta luflufluf, sai kuma ta saka yan yatsunta a na gefen ta dan kara sakashi ya karra tudu kadan ta barshi zube a gaban kijinta da gefen fuskarta kadan
Jan baki take ta kallo, da kyar ta iya janyo mai ruwan kasa kasa ta bude shi ta shafa dan kadan a bakinta , sannan ta dauki kwali tana ta kallo da tunanin anya ba sai ta yi kiran innarta ta saka mata ba? Domin bata taba sakawa da kanta ba ai
Karshe dai dagewa ta yi ta ringa karkata kai da kyar ta saka kwalin tana tsale da ihun ta saka sannan ta koma wajen kayanta bayan ta ga takwas ai ta gota tuni t dauka ta saka pant din da rigar ta koma wajen madubin tana kallon kanta harda dan juyawa a gabansa kadan ta dora hannunta a saman cikinta dake shafe uwa babu hanji a ciki ta yi murmushi , sai dai tudun duwawunta ne suka bata mamamaki, ba kasafai ta cika kallonsu ba, aminiyarta, kawarta Yar dubu ke yawan cewa ta ringa saka sutura mai rufe jiki saboda maza lalatatu masu bata ya'yan mutane dan Allah ya bata kira, ita kuwa sai tace Aminu zai iya tarda mutun ya kashe shege a kanta Alkur'an!
Murmushi ta yi tana gyada kai, idan ta koma ta labartawa yar dubu abinda ya faru da ita bata san ko zata yarda ba, ta yiwu sai ta sakata ta sha Kur'ani ko zata yarda, ama in sha Allahu ko kwana zasu yi sunna dambatuwa sai ta sakata ta yarda tunda ita ba makaryaciya bace bale a mata iya shege
Turaruka ta dauka a fili ta ce" Ku zo nan yayan albarka mu bare banza, tunda an zubaku uwa ba siya aka yi ba"
Karshe dai ta kai mintu talatin bayan karfe takwas din sannan ta fito da takalmi plat mai laushi ta yiwa Innarta salama bayan ta ja rantsuwar ba zata aikata aiki makamancin na jiya ba sannan ta fice ita daya babu ko yar rakiya ta bi ta babar hanya hankali kwonce tana tafe tana kallon yannayi da tsare tsaren ginnin sarautar ta garin AGADAZ, komai a al'adance sannan da tsarin zamani, kana gannin abin zaka gane an narkar da kudi fa ba abin wasa bane
Bata san cewa shiga ita kadai sai ta sha wahala ba sai da ta karasa bangarensa
Hanyar ta samu kanta da zubawa ido da tafka tafkan dakarun masu tsaitsaye sunna gadin wajen
A lokacin da ta sanar masu itace Bahija amarya aka yi mata tambayar zata halarci cin abinci ne? Ta bada amsa aka nemi da ta bada takardar gayata sai da mamaki ya kamata
A nutse ta aro halaya irin nasu, a dake ta bada umarnin a shiga a sanar da zuwanta idan an bada umarnin ta koma sai ta koma
A kan dole suka aikata hakan, bayan kamar minti biyar aka bata danar shiga
Baki ta tabe a ranta tana ayana' dama na zo da redion innata na saka kidan kai ku kama sana'a mata na maku habaici kitika kitikan banza kunna gafin kato...., Koda yake na san yana dan baku na sakawa na salati'
Haba dai ta samu ta karasa ta wuce bayin dake zaune bayan sun zube sun gaisheta sunna mamakin ganninta ita daya kuma amsa masu harda su ya gajiya sannan ta bude madubin dake fitar da danshin AC ta shiga da salama kasa kasa a bakinta
Ta tabata koda shi namijin bai kalleta ba, yan matan sun zuba mata ido, domin tana ji a jikinta kallonta ake yi,