Sashe 20
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana shiga baiwar nan na karasowa , dan haka da ido ta kori sauran masu kula da ita sannan ta sabule rigarta tana yi mata wani kallo mai kama da dan iskan kallo kafin ta miko mata hannu suka shige ciki a daidai lokacin da ake kiran sallar magariba (subahanalah, Allah ka rabamu da lalacewa)
A hanyarsu ta dawowama basu yi tsaye tsaye ba, mazan nema ke sauka sallah , daf da magariba suka karaso garin su
A lokacin da mota ta tsaya Gimbiya ta sake fitar da wani huci na mamakin gannin ta kasa yiwa Fadime maganar nan a hanya bayan haka suka yanke da mijinta
A lokacin da Fadime ta fito ta mata rakiya har dakinta tana shirye shiryen yi mata salama ta dakatar da ita tace ta tsaya ta fito
Tana shigewa Fadime ta daura Alwallah ta gabatar da sallolin dake kanta domin ji take kamar ta fado daga motar ta yi su a hanyar nan
Taba tsaka da adu'arta da yan yatsunta Gimbiya ta fito ta sanar mata tana iya tafia
Dukawa ta yi ta yi godiya sannan ta juya ta tafi tana tunanin me ya sa da farko aka tsayar da ita?
Watsar da tunanin ta yi domin bashida wani anfani
Zama Gimbiya ta yi ta ringa kiran malamanta tana sheda masu kamar yadda mijinta ya kirayeta ya fada mata cewa bai yiwa Sarkin dogarai maganar ba, duda ya san abu ne wanda zai yi murnarsa, sai dai abinda ke boye a lamarin yake so idan lokaci ya yi ya fito masa a mutun kar ya nasa gardama, dan haka du su sanarwa malamansu na tsubu kan su rufe masu baki , watau Dogari da matarsa, duda ta ga kamar hakan wani basu darajar da basu kai bane, a tunaninta sun isa su tankwasa su kai tsaye su amince da komai, ama mijinta sai yake nuna alfarma zasu nuna sunna so, ba zasu nuna cewa za'a yi haka a matsayin bahija ce aka aura masa ba, no, zasu nuna mace ya nema kari shi kuwa ya ga babu wace ta dace irinta, abubuwa dai tsare tsare irin nasu wanda su suka amince da kayansu
A yau da darema hira suka sha, bama kamar Hindu da ta tsatsare yayarta da tambayoyi a kan BABAR MASARAUTA, karra karkata kai take tana sakin murmushi yayarta na fada mata irin tsarin masarautar
Tana murmushi ta ce" Aunty, kuma kin samu gannin sarki?"
Fadime ta zarro ido tana kamma haba ta ce" Gannin sarki kuma?, Da ace na samu zuwa wajen bayar da kyautar masu saukar na tabata da zan hango shi, kin san nima ina so na ga UMUGHLUK ITIFAL ganni na biyu, kawai na duka har kasa na gaishe shi na sake yi masa jinjina irin ta ban girma"
Hindu ta karkace kai tana sake dora kankara a saman kitson da NADIRAH ta matse mata kai ta yi mata ta ce" Baki san wani abu ba aunty, ai du ranar da na je babar masarauta, ko ana ha maza ha mata sai na ratsa na ga UMUGHLUK ITIFAL!"
Aban NADIRAH dake zaune yana sake nuna mata yadda ake daura damarar hawa doki da kyau dan idan ka yi rashin Sa'a ka hau doki mahaukaci kar ya ilatar da kai ya juyo yana kallon su ya yi murmushi ya ce" An fada maki kamar masarautar nan ce da mule yawo son ranmu?, Ko sarakai sukan nemi damar zuwa ne basa mata shigar kai tsaye, ko a yau na tabata dan a bude take du wanni na annabi na shiga kai tsaye, da ba dan wannan ba na tabata da sai mun jira koda zamu samu shiga, HINDU masarautar dake zagaye da masu kakin sojoji? Dogaransu fa horo ake basu irin na sojoji, dogari dake rike da bindiga? Salarry garesu du karshen wata mai tsoka , dogarensuma sarakin wani kauyen ne nake fada maki, wai inama mijinki?"
HINDU ta yi murmushi tana gyara zama ta ce" Yaya ai a nan muka wuni shima ya tatso nonon Indi, yaya dan Allah wata rana ka kaimu mu ga masarautar koda bamu je mun ga sarki ba, ka san me nake son gani? Wannan kofar da aka ce a cikinta gangar dake kuka idan jinnin masarautar ya rabo, wanda aka ce a kulin sai gangar ta yi idan UMUGHLUK ITIFAL ya zo wucewa, ina mamaki, shin tsafi ne ko menene?"
Ajiyar zuciya ya sauke zai yi magana ya ga yadda NADIRAH ta cika tana neman fashewa sai kumbura take yi, ya tabata dan sun barta sun shige hirar sarauta ne, murmushi ya yi ya ce" Kin ga Hindu ku zanta da yayarki, ai itama na kula idan abu ya shafi sarautar Babar masarauta ce har sai na nuna na gaji idan ta fara labarinta, bara na iya da yarki"
Haka suka sha hira sai da dare ya tsala sosai sannan ya tafiyarsa su kuwa suka kwonta barci
Washe gari da sasafe suka fice wajen aikinsu, da nufin sai dare yauma, ita dai NADIRAH da ido ta raka mahaifiyarta tana cike da tausayinta a zuciyarta har ta bacewa ganninta, a irgenta dai gobe zasu tafiyarsu gidan bikin nan na kawar innarta, daga cen kuwa su yi tafiyarsu LABA, ta kagu ta je ta tarda masoyi, barowarta kauyen yana ciwon yatsa da suka je yana ihun kuka innarsa ta koro su tana cewa mai nacin namiji wannan ai sai ta tsotse mata Da!
Murmushi ta yi kasa kasa ta ce' Aminu aminuna, iyeah, aminu ina sonka, iyeah........'
_____________________________________
Jus din dake ajiye ta sake kallo, gaba daya jinnin jikinta kamar zai tsinke take ji, a hankali ta sake duban Gimbiya dake zaune kafarta na dan girgizawa itama tana kallonta
Gimbiya ta sake kallon jus din, ta kalleta ta ce" Baki taba lemun ba fa Fadime?"
Gaban Fadime ya sake faduwa, a sanyaye ta sake duban Gimbiya jikinta na karra mutuwa, sosai take son tambayarta ko lafiya? Domin abinda take ganni yana nan girmamar tunaninta, sai dai ta kasa, domin ba yar haka a tsalaninsu ai, sai sada kai da ta yi kawai tana sauke ajiyar zuciya a ranta tana Adu'ar ko menene Allah ya kawo mata shi da sauki
A hankali Gimbiya ta dan sake matsota tana dubanta ta ce" To shikenan tunda ba zaki sha lemun ba, dama abinda ya saka nace yau zamu zauna da ke dan ina tafe da gagarumin albishir, albishir din da na tabata shine burinki, shi kike jira, idan kika same shi hankalinki ya gama kwonciya, zaki kerewa Sa'a, zaki samu abinda kike so hankali kwonce"
Fadime ta sake dago idannuwanta masu kaifi ta tsare Gimbiya da ido ba ko kyaftawa
Gimbiya ta sake gyara zamanta a nutse ta ce" Gagarumin albishir din shine, Mai martaba ya yanke shawarar aurar da yarki wa UMUGHLUK ITIFAL a cikin sirri, wanda kafin a yi haka sai kun kaura daga gidan nan naku kun koma daya daga cikin maka makan vila dinsa, an zuba maku masu aiki, an yantaku yantawa mai girma, an baku makudan kudade ga mota, dukkan abunda kuke tunani na ci gaban rayuwa zaku same shi a kwana kusa, idan har komai ya daidaita nan da sati biyuma an yi an gama!"
Gaban Fadime sai da ya rugurguje ya fadi, a zabure ta sake kafeta da ido tana son fahimtar shin wasan kwaikwayo Gimbiya ta koma yi kuma ko menene?, Wannan tsarariyar maganar da ta zubo mata kai tsaye ba kwane kwane ba dan sakayawa da alamu irin na wasan poisson d'avril, ko tace magana irin ta yan maye? Gashi kuma su ba wasa suke yi da junna ba sai kawai ta zamto tamkar mutun mutuni tana kallon Gimbiya, wace ke dan neman damuwa da yannayin Fadime din, dan haka ta sake gyara zamanta ta ce" Fadime?"
A hankali Fadime ta sake saka kaifafun idannuwanta a cikin nata tana kallonta, muryarta a cen ciki ta furta" Bahija din, ta ki amincewa da abinda kuka tsarawa rayuwar nata kennan?"
Gaban gimbiya itama sai da ya yanke ya fadi, ta sake fuskantar Fadime ido cikin ido ta ce" Ban fahimci maganarki ba, ko kina so ki nunan labe kike min ni da mijina a cikin gidana da y'ayana?"
A hankali Fadime ta girgiza kanta tana dan gyara zamanta kadan ta ce" Ba labe bane, maganar ce kuka yi tun karfi, a yanzuma dan ta kama ya saka na fadeta"
"Yaya kike min magana a wani tsaye kamar kin samu wata sa'arki ko talaka irinku?" Gimbiya ta fada a kausashe tana duban Fadime, dan ta fara kular da ita, aa, dazu fa na gangare yace mata ta tarbi matar kai tsaye domin a kanta ya kwana, watau ya kwana yana surkulensa da sunnan Fadime din ya tabata ana fada zata hau tsalen hakan, bale an yi magana ta yanta bawa daga bauta? Ai a guje zata amshi wannan tayin har ta duka ta yi godiya, sai dai ga wani raini na nan.shiga tsakaninta da baiwarta bayan ta isa da ita?
Fadime ta sauka daga saman kujerar da aka sakata zama ta duka kanta a kasa sosai a sanyaye ta ce" Allah ya huci zuciyarki, ba nufina haka ba, idan na bata maki ki yi hakuri, ama NADIRAH tanada wanda take so, Allah ya karra maki lafiya!"
Fadime bata taba zato, ko tunanin zata dauki mari a saman fuskarta a kan wannan magana ba, ku gane ta san ta shiga matsala kennan, ama bata yi tunanin matsalar mai zafi irin wannan bace, mari? Ai mutun mai daraja baya marin fuskar mutun, ko yaro ne ka dali keyarsa, domin fuska daraja gareta, ba'a son marin fusla, bale tata da girmanta da komai wace ta tabata ta girmi gimbiyar?