← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 99

Sashe 76

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya dan sake rike hannunta yana danne zuciyarsa da kokarin ci gana da buga game din UMMA ba tare da ya sdakar da wuri ba ya ce" To menene na kukan a cikin nan kuma Auta ? C'est très simple hein?, Ki cewa mamanki kina sin zama tare da auntynki ba sai ki je ki zauna ba? Duka dai ai cikin gidan guda ne ko? Maganin kuma a ko'ina ana iya baki shi ki sha, wai inama magungunnanki na tabata baki sha na kwana biyun ba, oya tashi ki je ki dauko min maza share hawayen dauko min su dukansu"

Kai ta gyada tana dan share hawayen nata sannan ta mike jiki ba karfi ta bi ta hanyar nan ta cikin falonsa

Umma ce ta daga kafa da nufin bin bayanta ta ci kaniyarta kamar yadda ta saba, hakan ya saka NADIRAH mikewa tsaye , sai dai idon da ta ga ya zuba mata da alamun da ya yi mata kan ta koma ta zauna ya sakata zaunawa tana jin hankalinta na neman tashi da lamarin, ta sani sarai Auta ta riga ta tsorata da matar nan sai gyaran Allah kawai

A hankali ta dago ta dube shi, muryarta ba karfi ta ce" Abahnta, ta yaya yarinya ta nuna maka bata so zaka nemi tirsasata ne?"

Idannuwansa dake kanta ya sake zuba mata har yana wani dan kashe girmansu irin ita din dai yake kallo

HUZNAH ta kalleta da mamakin karfin halinta da iya shegenta, kai ta girgiza ta ci gaba da jiran nata maganar, dan ta san ba gamawa ya yi da ita ba, ita kam zata je ta ringa fadawa Allah a kan lamarin yarinyar nan, idan tana wani abin har tsoro take bata

NADIRAH ta karra dagowa ta dube shi,yanzu fuskarta ta fara hadewa sosai daga yannayin sakewar nan

Ido cikin ido ta ce " ina son tarda ita"

"Me ya sa?" Ya fada a tausashe yana sake kallon réaction dinta

Matarsa ta kalla, sai kuma ta kalle shi, a taysashen itama ta ce" kawai ina son zuwa kusa da ita!"

Hanyar ya kalla shima, sai kuma ya yi dan murmushi bai bata damar tashi ba, hasalima a hankali ya ce" zan so na dan ringa samun lokacin da zaku ringa kasancewa tare, gashi kun nuna bakwa son lokacin cin abinci, shin wani lokaci ne zamu ware?"

HUZNAH ta sake jingine bayanta a jikin kujerar nan tana jin du abin wani ba wai, kai kishiya? Kishiya ko ta kara ce gaskiya tana da daukan hankali, shekararsu nawa a cikin tsarin nan ba'a taba magana a kansa ba sai ita isashiya ta nuna bai mata ba, da acema mijin nasu na ratsa tantanin halitarsu ne da sai tace dole ai an riga an san dadin abin, to ama babu wannan ita me take yiwa neman fitinar?

Shi kuma a zaunen da yake wani irin abu kai kama da kishadi yake ji idan ya kalli fuskar HUZNAH yadda ta cikota, sannan ya kalli ta NADIRAH yadda ita kadai ke harare harare abinta tana kada kafarta ta dama, hankalinta gaba daya ya yi wajen da su UMMA suka shiga

Dan murmushi ya yi, watau abinda take yi du da dalili ko?

Zai sake yin magana Auta ta fara shigowa, Expression din fuskarta kadai ya kalla ya ji yannayin nishafi nishadin da yake ciki na neman gagararsa, hakan ya saka shi dauke dubansa a kanta yana mai ambaton Allah har ta dawo ta zauna a nesa da NADIRAR da kuma Shi Aban nata, hakan ya saka NADIRAH lumshe nata idannuwan tana dannar zuciyarta da tambayar kanta anya zata iya ci gaba da jure wannan cin zali irin na UMMA?

Ummar ce ta shigo itama, fuskarta a washe yanzu, watau ta nanagawa Auta abinda ta ga dama ta huce ko? Ta dawo ta zauna tana sake kallon NADIRAH, irin abinda suka yi da Nadirar jiya zuwa yau tana son ganewa wai a cikin tsare tsaren ne ko menene? Ta ga ai a lokacin baya nan, kuma ta sanar mata baya nan komai tana iya yi a bayan idannuwansa ama sai ta ga sam bata saurareta ba

A kausashe ya ce" Ku tashi ku tafi, zan neme ku, banda UMMA"

Su ukkun suka mike, sai ya ga kowace na neman daukan hanyarta daban

Watau harda AUTA da NADIRAH

A cikin sasaukan Furuci ya ce" AUTA, ki bi Maman naki kin ji?"

Da Auta da NADIRAH suka juyo sunna kallon fuskarsa, duda sun so fahimtar me yake nufi ama basu yi gagawar yarda da haka din bane, sai da ya masu alamu da idannuwansa sannan ya ga ikon Allah murmushin da ya fadada fuskar NADIRAH, murmushi irin na jin dadi sannan ta kama hannun Auta suka wuce da dan saurinsu

Dubansa ya maido Kan UMMA wace harda zarro ido ta yi dan mamaki tana kallonsa

Murmushi ya yi a tausashe ya ce" UMANA, ki yi hakuri da su dan Allah, kin san jiya tafiya muka yi cen garin gabas wajen gonakina, ana yin barna a ciki ne kuma ana neman a tayar da fada tsakanin manomana da makiyayan yankin, kin san makiyayi da abin kiwonsa, to fa shine muka je abu karami ya zamo baba domin a dole muka zauna aka yi ta rabiyar rikicin, da na dawo tuni dare ya yi sai muka zauna a masalaci muka gabagar da sallah sannan na shigo, Inaga lamarin AUTA dole zan fitar da ita, abin nata yanzu ya fara kawo yar gardama , duba ki ga ke fa take yiwa musu?, Allah dai ya bata lafiya" ya ajiye a tausashe da siga irin ta lalami, baban burinsa ya kawar mata da dukkan wani shaku a kan fitarsa, da du wani sake sake, ya kuwa kai ga ci ya kamata a cikin game dinta, domin ta yarda da hakan harma ta dora da kalar nata munafurcin na yin galaba a kansa a da ta shiga shashekar kuka da share hawaye ta ce" Idan na ga haka sai na ji hankalina na neman tashi yarona, shin Auta tanada wani wanda ya fi ni ne?, Tana ja baya da ni ne dan ina bata magani ina kuma tursasata cin abinci"

Murmushi ya yi yana fan sake dafe gaban goshinsa yana kuma ankare da kiran dake ta shigowa wayar Umman ama ta ki dagawa

Umma ta sake dubansa ta ce" Yarona kuma ka ga, dole sai ka yiwa Bahija magana fa, kar ta ringa anfani da damar da Allah ya bata ta kasancewarta yar uwarka ta ringa muzgunawa abokiyar zamanta sannan ni ta ringa rainani "

Kai Allah mai mutane, a cikin mutanensa ya halici rikakun munafukan da duka iya tafiyar da rayuwar munafurcinsu cikin kwarewar da ba zaka iya gani kai tsaye ba sai idan Allah ya so ka gannin, da wannan dama da Allah ya bashi ya dake budar bakinsa ba tare da gajiyawa ba ya ce" Hakane, inaga ko harda yarinta dake damun BAHIJA?, Ba laifi in sha Allah zan kwatanta mata, kema sai kin tayani UMMA ni bani da time din abubuwan nan ne ma, ta rikicin cikin gari na ji ko tasu?, Ama maganar cin abincin nan nine nake da wannan ra'ayin, ba dan komai ba dai dan a baki lafiya ki ringa hutawa kema, shekaru karra ja suke yi wannan zama na karfe takwas a dauki wasu lokutan masu wani tsayin yanzu ba naki bane UMMA, sauran magangannun kuwa dole zan zauna da su na sanar masu ke uwa ce a gareni du mai son zaman lafiya ya girmamaki"

Magana ne yake yi mata du a dadaure, sai ya fadi wace ya dace ta rikita mata lisafi sai kuma ya fadi wace zata Kwonce tunanin cen nata na cewar ko wani abu na faruwa ne?
Fahimtar da ta yi ta fa ishe shi fa yawan maganar ya sakata mikewa ta yi masa salama ta tafi

Bayan ta tafi maganin Auta dake hannunsa ya cusa a cikin aljihun jalabiyarsa, sannan ya cire alkyabar gaba daya a hankali ya ci gaba da jan carbinsa yana neman sauki a wajen ubangijinsa har sansanyan barci ya dauke shi a nan saman kujerar, domin kafafuwansa kawai ya hauda sama ya shiga hutawa

__________________________________

A ranar UMMA bata kula kiran da aka yi ta yi mata ba, a tunaninta so syke su ji ko an saka masa maganin a abincin, har sai da wata safiyar ta waye, da sanyin safiya ta daga kiran da abin barci a idannuwanta domin ko salllar asubah bata yi ba, yawancin lokutama idan ta tashi ta ga rana ta yi bata yi kwata kwata gaskiya

Muryarta a ciki ciki ta ce" Wai dan Allah ku idan kuka so abu kamar Da ya so fita daga cikin uwarsa ne? Haba dan Allah ban saka maganin ba a gaba fa, ama sai wani kirana kuke yi ba dare ba rana ?"

"Ke dan Allah ki min shiru da banzan maganarki, ke har kin san yadda da yake yi idan ya so fita daga cikin uwarsa ke da baki taba haihuwa ba sai na kashi?, Ba maganar magani ake son yi maki ba, so muke mu sanar maki abinda ya faru da iyayen yarinyar nan, an neme su an rasa yau safia ta biyu kennan wai sun yi fada da wani mutun, mu muna nan cikin tashin hankalin abin ke kina cen kuna hauka!" Muryar mahaifiyar Bahija a zafafe ta fada har tana huci da takaicin Umma

Gaba daya Umma ta rigijo daga saman gadonta lokaci daya kuma jikinta ya dauki mahaulacin bari gab gab gab , haka kuma kafafuwanta suka dauki mijirya

A rikice ta ce" wani irin an neme su an rasa, gidan uban wa suka shiga yo? Ina masu tsaron nasu?"
Chapter 76 · 0% Book details