← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 99

Sashe 94

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Danne zuciyarsa ya yi ya ringa nuna mata ko su waye zai samu bakin zaren, yanzu yanzu kuma za'a kawo mata masu gadi,kar ta yarda ta fito daga bangarenta, ta yi zamanta da hadimanta har ya samo bakin zaren

Da wannan ya kwontar mata da hankali ya fice a bangaren nata

Bangaren NADIRAH ya nufa

Daga kofa ya nemi izinin shiga , hakan ya saka Auta dake waya tana doka murmushi zuwa ta bude

Tana gannin yayanta da sauri ta zarro ido hadi da neman boye wayar, dan ya hannata ai waya da mijinta

Hannun nata ya bi da kallo, sai kuma ya dauke kansa ya yi murmushi, kasa kasa ya ce" ki gaishe da Inna, plz ki harhada kayanta a bani ta baya, dan bana so tana yawo da yannayinta....."

Auta na murmushi ta amsa shi
Shima yana murmushin ya juya, har zai tafi ya dawo ya dan dakata yana dan ragewa idannuwansa girma ya ce" ki ce masa, kusan sati bai kirayeni ba ko gaba muke?, Sannan ki ce masa ya zo ya dauki Matarsa dan Tuzuruwar kauye tace maza a mayar mata da ya gidanta....."

Daria ce ta fashe da ita har tana rike ciki, shima ya juya yana doka murmushi ya fita ya nufi bangarensa yana daga waya ya yi kiran Sheikh

A nutse ya sanar masa muradinsa, watau a saka sarkin yanka ya dora yaransa hudu bangaren UMMA, dan yana da bukatar sheda, yana matukar son sheda irin ta musulunci, ba zai iya dora mata laifin Madigo kai tsaye ba, sai ya kamata da shedu ta yadda zata fuskanci hukuncin da ya dace da ita.................

Wannan kennan

A hankali rayuwa ta ci gaba da tafia, a cikin sati uku harta Auta an shiryata Inna Hindu ta rakata dakinta, a censai da ta yi mata kwana hudu sannan ta gudo dan kuwa sai da ta zauna kusa da ita ta sake shiryata zama a cikin ahalin da aka saka masu tsanarta ta hanyar kage da karya kala kala

A tsayin lokutan kuwa, wadinnan mutane sunna cikin halin rayuwa, halin rayuwa mai tafe da tashin hankali, babu isashen barci, babu walwala babu cin abinci yadda ya kamata, tun daga matar sarkin Dogon dutsi da yaronta, da sarkin tanus da matarsa da yarsa wace ke neman haukacewa kan soyayar balarabenta tana dudurawa du wani mugun da ya sace su ashar da tsinuwa da Allah ya isa, a gangaro kan baiwar Umma, da Umma da hafimanta , wa'inda suka dinke a cikin daka suke fama da zukatansu babu dare babu rana, zaman waje daya ba nasu bane du a kuntace suke da halin kila wa kala

.................................................

Yau ta kama talata ce, tunda safe Umma ta sha maganin barcin da take ba Auta dan ta samu barci, ta maku ta je daki ta yi kwonce take barci tamkar mataciya har sai da yama ta yi magariba ta kusan shigowa ta dan motsa tana bude idannuwanta da kokarin tashi dan barcin ya saketa

Kasa kasa ta ringa jiyo nishi, da gurnani irin na iya shege, hakan ya sakata jin tsammmm nan da nan jikinta ya shiga amsawa

A dan zabure ta iya mikewa, ko ido bata wanke ba ta fito tana wara idannuwanta dan jiyo abin take sai karra shigarta yake yi,rabonta da wannan lamari fa a kadan an yi sati uku da kwanaki

A kan hadimanta biyu idannuwanta suka sauka, sun dage a cikin aiki irin wanda suke yi yau da kulun sunna yiwa junna shirme irin na Madigo, dayar kuwa a gefe ita ke kokarin taimakon kanta da wani salon masifar ta bata kai da fata tana yi

Nan da nan tsumi irin na aikin da aka saba ya motsa mata

Daga tsayen da take ta ringa cire suturarta har ta idasa cirewa tasssss sannan ta karasa cikinsu ta rabasu ta yi daidaya ya zamto su dukansu sun rufu a kanta dan bata nata taimako ta hanyar yadda badalarsu a tsakaninsu

A irin wannan lokacin ne, yaran sarkin yanka dake labe tun farawar yaren Umma sunna dauka a waya, suka idasa dauka sosai da sosai sannan suka dauka harda su din watau sunne shedu hudun da ake da bukata kafin suke bayana masu kawunansu ta hanyar shigowa kai tsaye suka kashe fitila, sannan suka sake kunnawa

A haukace hankalinsu ya dawo gangar jikinsu, hadi da bugawar zuciya mai tsananin gaske

Lokaci daya zufa, da murdawar ciki suka wanzu a irin wannan lokacin, daya ya juya ya fice da abinda suka dauka, ya rage ukun nan dake tsaye fuskokinsa babu alamar sun taba sannin menene dariya a duniya

Jiki na rawa, fata a yamutse na alamun tsufa ya fara salamowa, Umma ke wawure wawure tana son warto zanninta dan ta rufe yamutsatsiyar fatarta da kwasha kwashan nonuwanta da suka yi la'asar tana furta" Innalilahi wa inna ilaihi rajune meye wannan, ku kuwa su waye ku? Me kuke so? Yaushe kuka shigo? Waye ya barku kuka shiggggggg"

"Ke dilla rufe mana baki algunguma mai dati ko mu lalata maki fata yanzun nan, ku kuwa du wace ta kuma gwada mikewa sai mun kakarya mata jiki kafin UBAN TALAKAWA ya zartar da hukuncin da ya dace a kanta!, Tsitttt bama son mugun motsi ko mu motsa maku jiki shashashu mararsa tsoron Allah masu yada fasadina doron kasa a tsaftataciyar masarauta!" Ya daka masu tsawar da ta saka dayar sumewa, lokaci daya kuma su UMMA aka shiga hali na tabuwar hankali da gigicewar yannayi.........

Sake yinkurawa ta yi, a lokacin da ta tuna me yace, yana nufin zasu sanarwa UMUGHLUK ITIBEL wannan aiki, aikin da baya dagawa kafa, mugun aiki mai wuyar sha'anin,aiki mai zafi mai ci masa tuwo a kwarya, wanda ya yi rantsuwar ko shi ya faru da shi sai an jefe shi tunda yanada aure, bale wani nasa ko talakawansa, aikin nan da ta tabata idan aka kai masa rahoto babu mai kwatarta ko waye ya sakata motsawar, hankali tashe ta rikito kasa tana hade hannayenta, bakinta na bari cikinta sai kugi yake zata yi magana aka budo kofar aka shigo, shigowar da ta kunce mata ciki yararin abu ya shiga bin jikinta, mai ruwa mai tsami mai kalar kore, lokaci daya kuma ta ja numfashi tana bin fuskar wanda tunda ya shigo bai kalli inda suke ba, saima umarnin da ya bada da hannunsa cewar a basu sutura, dan sannin girman tsiraici da ya yi da kare idannuwansa kallon dati da yake yi, sannan ya juya bai ko dubeta ba, ita Ummansa ya fice......lokaci daya ta tafi kasa numfashinta na barin gangar jikinta!

Takensa kennan,
Namiji son gannin mai halayar kirkidauke numfashin marar gaskiya

Takensa kennan UMUGHLUK ITIBEL bawan Allah mai kare dokokin Allah

Miji a wajen HUZNAH DA NADIRAH

Uba a wajen AUTA

Idan na ce maku saura kiris kun yarda?😁😁😁😁

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

6️⃣8️⃣

Jiki ba karfi ya haye saman bed din da NADIRAH ke kwonce tana kallo a wayarsa tana murmushi

A hankali ya sanyo hannunsa ya zagayo saman cikinta ya dora sannan ya lumshe idannuwansa , kansa a wajen wuyanta,
Dama HUZNAH yanzu sati kusan hudu kennan rabonta da zuwa inda yake, tunda aka yi abin nan ta sheda masa tana so ta samu lafiya koda zata ci gaba da daukan kwana, wai dan koda ta dauka a yanzu ba wani anfani zata iya yi masa ba
Ya nuna fushinsa a kan hakan , ya tarda ita har bangarenta, ama ta nuna tana so ne ta kula da lanta sosai, ya yi mata wannan alfarmar, a dole ya kyaletan, dan kansa bashi da space din sake daukan wani matsalan ko kadan

A hankali ta ajiye, ta juyo ta fuskance shi, ta tsurawa fuskarsa ido
Dama tunda ta ga ya mike a zabure ya fita ta san da wani abun
Ita yanzu har fargabar ya fita ya dawo da wannan yannayin take
Sam baya iya dane damuwarsa a gabanta
Yanzu gaba daya fuskarsa ta dauki jajajir , idannuwansa kuwa sun kankance sosai

A hankali ta ce" Menene?, Waye ya taba min kai na je mu casu?"

Idannuwansa dake lumshe ya dan dago a hankali yana kallonta, dan murmushi ya yi yana kallon idannuwanta, muryarsa a shake ya ce" NADIRAH......, *INA SON KI*"

Dum gabanta ya buga, aa hankali ta ringa lumshe idannuwanta har ta zubawa lebensa ido
Numfashi ta ja kadan sannan ta idasa shigewa jikinsa

A sanyayen ya ce" Dan Allah, ki so ni domin Allah, sannan ki rike min mutuncina....., Idan a zamantakewar aurataya da muke yi ni da ke, akoy wani abu da kike so na yi maki wanda bana yi, ko menene, in dai bai taka dokar adinin musulunci ba, watau zuwarwa mace ta dubura....ki sanar min, ko ki kwatanta min....., Ba zan taba jin kyankyaminki, ko kiwyar yi maki ko menene ba, dan Allah kar ki dubi wani ko watana, hakan zai iya tsayar da numfashina NADIRAH......"
Yana fitar da huci ya karashe maganar, ya dora da fadin" In ba jaraba bama, meye za'a tsinta a dan uwan halita, ina zumudi da son gannin kwaf, ina abinda zai shigeka ya gigitaka?, Shikenan kaine wawa sakarai ka zo ka amshi iri irin naka? Allah ya wadaran naka ya lalace!"

NADIRAH dake ta danne dariarta, dan a bayane ta fahimci kishin mijinta ne ya motsa sakamakon wani abu da ya gani, tana kyautata zaton abin a waje ya gano shi har ya rikitashi haka, sam bata yi tunanin ya shafi Umma ba, shi yasa take dan murmushi ta ce" Ai kam, wai ka ga kwarata mata, kuma ka ga maza na mu'amala da maza, nima na sha ganni harma wata ta taba nunan wai inada kyau"

Raunanun idannuwansa ya zuba mata, a hankali ya ce" Bakya tausayina?, Kina gani fa hankalina a tashe, matar cen ne fa aka kama yau dumu dumu cikin alfashan nan, dan Allah ki daina mana"

Sai a lokacin ta gane, a hankali ta shiga nuna masa bata gane bane, ya yi hakuri, sannan ta shige jikinsa tana dan dora hannunta a saman kirjinsa
Chapter 94 · 0% Book details