← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 99

Sashe 89

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muryarsa a raunane, hankalinsa du a tashe ya ce" Ki yi shiru haka Uman Abahnmu, haba Mariya mai baban daki, haba matar Lamido , dubi nan, dubi ban fa yi fushi ba dan wanu abu sai dan jin ciwo a zuciyata, Auta ina gefenki, ina tare da ke ba dare ba rana ina fita da isa da takama na je garin wanda na ga dama na kwato yancin wanda aka cutar na dawo kasata na kuma ja layi na tsaya na zartar da hukunci a zauna lafiya ama na gaza gannin hali na ukuba da aka saka min kanwata?...........kin san me haka ke nufi a wajena?, Auta na yi karatun rayuwa tunda na hau karagar mulki, abinda yake karkashin tunanina ni da kaina na san wani lamari ne na ubangiji, mutun kuwa na yi masa karatun da yake da nisan gaske, na riga na san cewa babu abinda ke gagawar juyar da kwakwaluwar dan Adam irin abu ukun nan *ARZIKI, MULKI, MACE*, a kansu dan Adam na iya mance kansa da asalinsa, a kan neman duniya da abinda yake cikinta dan Adam na iya mantawa ba matabaciya bace ya saki jiki ya yi ta tafka lamuransa sai a cikin bulala ukun nan daya ta riske shi sai kuma a dawo ana dana sani ko a rikice a bar dabi'u na alkhairi a koma kwashe kwashe watau *RASHIN LAFIYA, TSUFA, MUTUWA*, wa'inda basa yiwa kowa uzuri ko su baka dana ka sake gwada wani tashin daban da wanda ka yi..................................."
Ya ajiye maganar yana jan numfashi, dan ya zame masa jiki idan dai ya yi doguwar magana irin haka yakan ji ya gaji ne tikis kamar wanda ya yi wani aiki , sai yana yi yana ajiyewa ko zai iya karasa yawan maganar

A hankali ya sake budar bakinsa ya ce" Tabas mun bata yarda, ta ci amana, a lamarinta yanzu abu daya ne ke cikin duhu a zuciyata shine rasuwar mahaifiyata, me ya hadasa kumburin cikin ANNA kai tsaye? Harta a likafaninta cikinta a tashe yake sosai wanda na jima a cikin tunanin nan, da kuma bakin jinnin da ya fita ta hancinta..............Shin matar nan ta kai wajen da ta kashe min uwata Auta?"

Dummmm gaban Auta ya yanke ya fadi, zuciyarta ta shiga yi mata zafi domin tunano kamawar da ta yiwa Umma da irin rikicewar da ta yi kafin kuma ta ga ta sauke ajiyar zuciya a lokacin da ta ji jan numfashin Mai dakin Mai martaba na karshe, jan numfashi da ya yi wani irin tsayi ya fita bai kuma dawowa ba, kukansa a kunnenta da irin ajiyar zuciyar da ta ga UMMA ta sauke alamu na kwonciyar hankali ya wadata fuskarta, ama kuma sai ta kamata ta kaita dakinta ta rufo ta fada mata mamanta ta mutu , bayan tana cikin kukan wai mahaifinta ya rasu.............ta barota a ciki, ita daya kwal da ranta , ta yi kuka har nunfashi ya yiwa kofar hancinta kadan ta summe, wanda sai a washe gari aka ringa nemanta hankalin ASADEEK din a tashe kamar zai summa dan tashin hankali da kyar aka ganota a dakin nata summe.......

A harhade ta sanar masa komai , dukkan abinda ta sani, irin abinda ta gani a fuskar UMMAN har rufewar da akai mata Umma ce ta rufeta a daki

Ya jima idannuwansa lumshe, gaba daya ji yake yi me kuma ya rage masa na jin dadi a duniyar nan? Gaba daya ji yake yi sarauta bata yi masa rana ba , ji yake yi da ace su ba kowa bane da ba'a rabe su dan a cutar da su ba, saima yake ta kokonton anya zai iya sake yarda wani ya masa shigar da Umma ta yi masa a zuciya ta cutar? Wani tarin takaici gefe daya kuma yake mintsininsa, wannan maganar idan har haka ce dole zai ji ciwo a zuciyarsa mai tsanani, domin ya so ne ta rayu a cikin gidan kaso ta yadda zata yi doguwar rayuwa tana kallon abinda zai yi ta nukurkusarta, idan kuwa harda maganar kisa a ciki ai dole za'a kasheta itama, sai dai kashetan nan walahi walahi ba zai
aikata da wuri ba, bi'izinillah sai ta yi rayuwar gidan kaso koda ta shekara biyu ne tare da fargabar yau ko gobe, da rikicin tunanin kwonciyar kabari da irin abinda ta aikata, sai ya sakata daki mafi muni da duhu ta yadda zata ringa auna a duniyar kennan ina ga lahira da nauyi irin nata? Sai ya wakilta malamai irin masu zafin wa'azin nan sun ringa zuwa du safiya ta Allah sun yi wa'azi a kan mutuwa da girman laifin wanda ya cutar da bawan Allah da irin azabar dake cikin wuta, uwa uba hanyoyin da za'a tarar kafin a kai tsayuwar hisabin, bi izinillah sai ya bata damar dandanar ukubarta daidai misali, ta yadda zata zamo mahaukaciya ta gasken gaske ba wai ta karya da hade haden magani ba, sannan zai zartar mata da hukuncinta ta hanyar bawa du mai iya ganni damar zuwa dan hakan ya zamo babar bulala wa mai rabon dacewa da shiriya tun kafin lokaci ya kure masa

Daga hakanan kuma ya kasa furta komai sai idannuwansa da yake kawarwa baya so Auta ta kalla du irin yadda take son kallon dan kamalta abin a zuciyarta ta san yana cikin wani hali mai wutar fasara,

"ABAH" Auta ta fada a sanyaye tana kallonsa

Da kyar ya iya daga idannuwan nasa yana kallonta

Auta ta lumshe idannuwanta cike da jin tausayinsa a zuciyarta, ita ta fi tausaya masa fiye da nata, dan shi ya zame masa dole ya dauka ya kuma shanye, ya dauki damuwarsa ya kuma dauki ta talakawansa
Murmushi ta dora a saman lebenta, a hankali ta ce" Abahna, Aunty NADIRAH....... Au, Momy NADIRAH fa tana da ciki, Abahna zamu samu baby muma ABAHNA....." Ta karashe tana kallon yannayinsa a lokacin da ya zarro manyan idannuwansa yana kallonta, kamarma bai yarda ba, kamar kuma abu ya shigo maka kai tsaye, dama burinta kennan abin ya shigo masa kai tsaye , cikin tarin duhun da yake gani haske ya ratso alfarmar annabi da Alkur'ani.............

Muryarsa a cen ciki ya iya sake budar bakinsa da kyar yana kallonta idannuwansa a wajen nan ya ce" Me kika ce?"

Auta ta sake maimaitawa, yanzun har yar dariya take yi tana share hawayenta hadi da jan hanci

Jikinsa ba karfi , ama kuma yannayinsa na cenza salo ya dan rangwabar da kansa aa sanyaye ya ce" kuma tsokanar da zaki yi min kennan Auta?............"

Daria Auta ta saka mai dan sauti kadan, ta ce"

Hello people, morning all

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

6️⃣5️⃣

Ina kuke MATA, MATA masu ji da kansu,MATA masu aji, WA'INDA suka san girma da darajar gyara, WA'INDA suke iya cire kudade masu yawa dan gyaran kansu? Ku garzayo ku tuntubemu, ama ku tabatar jakarku ta cika taf, domin bamu da lalan kaya bamu da na kudi kadan, kayanmu gyara ne hajia magani ne na mata mai mayar da busashe tamkar teku..........ku tumtubemu ta wannan numbar *80229915* MAIMUNA MATAR ABDULAHI..... Sai kun zo

Daria Auta ta saka mai dan sauti tana kallon irin yadda yayanta ya yi kamar wani bakin marayan dake jin yinwa ta ce" Abah, ana wasa da irin maganar nan mai daraja da girma?, Ama fa ba likita ne ya fada mana ba, Mamah ce ta sanar mana, Aba ka san datijai sunna ganewa ko yau ka tashi da ciki sunna iya fahimta , a shekaran jiya n....................................................."

Sauran maganar ne ta hadiye tana zarro ido hadi da binsa da kallo, domin kafin kace meye wannan ya mike daga zaunen da yake ya durfafi dakin da Nadirah ke ciki

Bai tsaya tsaye tsaye ko jin kunya ba ya kama ya bude ya shige cikin dakin, hakan ya saka Auta sakin murmushi ta mike ta fice da wayar wajen Inna HINDU ta janyo kofar ta rufe da ky ta shiga tafiya a nutse da wayar tana neman layin wanda take mararin jin muryar mai shi

_________________________________

Karar bude kofar ta ji, tana tsaye gaban madubi daure da tawul, wanka take shirye shiryen shiga dan kuwa tun na asuba da ta yi kafin ta daura alwallah dan jikinta ya saku sai yanzu da zata yi wani, tana kallon mamanta da ya kumburo, bama irin kansa da ya yi mata wani iri ta yi saurin daura tawul din tana hade goshi a zuciyarta tana ta tunanin shin zata sanarwa Innarta abinda nononta yake yi ko zata yi shiru da bakinta ne? Idannuwanta suka sauka a saman fuskarsa

Irin kallon da yake binta da shi ko makauniya ce ita dole zai samu effet a jikinta
Da sauri ta dauke idannuwanta ta juya ta shiga rarumar abinda zata rufe jikinta gaba daya , kaffafuwanta da hannayenya sai bari suke tamkar mazari

A hankali ya sake lumshe idannuwansa ya ciro bayansa daga jikin garun da ya jingina ya ringa takowa zuciyarsa na bugawa har ya karaso inda take tsaye jikinta na mugun rawa ya rungumeta ta baya a hankali ya dora kansa a saman wuyanta lokaci daya kuma ya kama hannayenta da nasa, yana sake lumshe idannuwansa yana fitar da huci daga zuciyarsa ta bakinsa mai dumi a dokin wuyanta, muryarsa a sanyaye ainun, sannan a cen ciki ciki ya ce" Dan Allah, ki sasauta min haka mana Tarhanine…......"

A hankali ta ringa daidaita kokowar da take ta son yi da shi, zuciyarta na dokawa da masifar karfi, kanshin jikinsa na ratsa dukkan wata kofa ta hancinta, bakinta, kofofin jikinta sunna wanzar mata da muguwar kasala da mutuwar jiki ta karra lumshe idannuwanta tana cije jinjirin lebenta tana jin zafafar zufa mmai dumi na sauka daga gaban goshinta tana zuwa jikinta

A sanyaye, muryarsa na matukar son halakata ya sake riketa a jikinsa a hankali ya ci gaba da fadin" ki tausaya min haka dan ALLAH, kin ga ni marayaa ne gaba da baya, wace ta rikeni ta wulakantani......, Kin san a yau ji nake kamar zan mutu?, Zuciyata ciwo take min Indinah...., Zafi nake ji sosai momyn Autah.........." Ya karashe yana sake riketa a kirjinsa
Chapter 89 · 0% Book details