← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 99

Sashe 91

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A dole Aban datawa ya manta dukkan wata damuwa da ta saka masa nauyin numfashi, ya kuma manta a ina ya tardo yar mutane ta hanyar janye wannan abu da ta daura a kirji ya yar idannuwansa na sake kankancewa yana neman kurma ihun MAZA ya damketa, ba ju ba gani ya ringa juyata kamar yadda yake juya akalar dokinsa idan ya hau, ya kuma sameta da wata irin biyaya domin du irin yadda ya yi tunanin zata gajiya da wuri sai ta bashi mamaki ta hanyar nuna masa ta fa shigo gari ta kuma harbun dan kuwa sai da ya darji mata iya darza ya kuma san ya zowa mata sun amshe shi...................
Ba shi ya tuna a inda suka yayada manufarsu ba sai da suka fito daga wanka, a lokacin ne itama ta ringa tambayar a ina ya bar Auta fa innarta kafin ya shigo? Kiri kiri ta nuna wannan din ai laifinsa ne ya zo mata daki Fisabililahi ya sakata aikata kayan kunya

Shi dai murmushi yake yi yana binta da kallo har ta gama shiryawa, yana tsaye yana kallo ta saka zumbulelen bakin hijab ta dauko nikaf dinta da safa bakake tana fadin" Wai Aban Auta, dolene mu je asibitin? Idan mun je ai ba za'a min allura ba ko?"

Kai ya girgiza da sauri, a tausashe ya saka hannunsa cikin nata kasa kasa ya ce" Babu mai yi maki allura, zamu je ne a tabatar mana, kuma ba asibiti zamu tafi ba, gidan SHEIK ne zamu je, kin ga ni ba zan je asibiti haka rana tsaka ba ko?"

Murmushi ta yi ta saka safar sai tafukan hannayenta a waje, a hankali suka fice tanaa sando shi kuma yana murmushi yana biye da ita ta biyayiyar hanya suka bar bangaren nata suka wuce nasa

A cenma zama ta yi a falo shi kuma ya haye sama

Yana zuwa suturarsa ya cenza zuwa sasauka, ya yane kansa da sasaukan rawani ba asalin wanda za'a iya gane shi ba, domin du buzun mutun dai an sanshi da rawani ba sai sarki ba, ya saka takalmansa masu saukin tafiya

Yana fesa turare yana ta doka murmushi kira ya shigo wayarsa

Da dan mamaki yake kallon numbar, domun numbar mahaifin HUZNAH ne, sarki Muhammad, bai taba yin kiransa ba kai tsaye, hakan ya saka shi komawa ya karo dakin da kyau, ba dan komai ba sai dan baya so yana magana da shi wani abu ya katse, haka kuma ba zai so ace NADIRAH ta san cewa HUZNAH da SHI babu mu'amala irin ta aurataya a tsakaninsu, zai so ace dukkan abinda yake sirri na daya a wajenshi ya zauna a wajenshi kadai, ba dan komai ba sai dan gudun matsaloli irin na yau da kulum na mata, ba zai taba bude sirrin daya a gaban daya ba, koda ta ji to ta je ta karata da wasi wasi ba zai bata fuskar ta yi masa tambayar idan haka ne ko ba haka ba, hasalima ba huruminta bane hakkan, gaba dayansu zai yi masu wannan adalcin dan gannin ya kaucewa cece kuce da matsaloli na yau da kullum

A nutse ya amsa salamar da Sarki ya yi masa da girmamawa, sannan ya sake mayar masa da gaisuwar da ya yi masa dan bashi girmansa

A tausashe sarki MUHAMMAD mai adalci ya ce"

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

6️⃣6️⃣

A tausashe sarki Muhammad ya ce" Allah ya karra maka lafiya, da nisan kwana, ya sa a gama da rikicin mulki lafiya, ina fatan ba'a fada ? Na yi kira a irin wannan lokacin ina fatan ba'a cikin wani uzuri mai karfi?"

Dan murmushi ya yi, a duniya yana girmama datijin nan sosai, domin mutun ne mai daraja, masarautarsa ba babar masarauta bace, asalima kauye ne a da a hankali ya zama kauye ama mai shige da gari dan yana tafe da jagorancin sarakunna masu talafawa talakawa da kawo ci gaba a garinsu,
Tunda ya auri yarsa ba zai ce ga ranar da wani abu na batanci ya shiga tsakaninsu ba, haka kuma tunda girma ya same shi na jagorancin al'uma bai taba kama garinsa da laifi mai girma ba ko karami, ya iya da rikicin garinsa yana kuma kare girmansa, bai saka kwadayi a gabansa ba bale halaya na rashin da'a su aure shi, sosai ake girmama shi a layin datawan sarakunna masu mutunci, haka a tsakaninsu na sarakunta zai iya cewa Alhamdulilah
A tausashe ya ce" Babu takura, ranka shi dade, Allah ya karra kusanci da fiyayen halita Sallallahu alaihi Wa salam"

Da amen ya amsa cike da girmama ASADEEK, domin kiran nan da ya yi masa sai da ya kori kowa shima ya samu nutsuwa dan su zanta

Cike da jin nauyin maganar, da kuma kunyar abin dan bai taba fuskantar irin haka ba ya ce" Rikici ne na Mata Allah ya karra maka lafiya, koke koke da magangannu masu rikitarwa sun same mu da sanyin safiya daga mai dakinka, harda neman alfarmar a nema mata alfarmar ta zo gida a nema mata magani,.........shine na dakawa abin tsawa cewar ba dai gidana ba, sai daga baya nake ta tunani a kan lamarin, magangannunta du a sasabe ta banu shi, ta kuma ce ta gaza gane inda ka dosa.....ta yiwu bata sada kai ba bale ta fahimtan, dalilin wannan ya saka na yi kira, ba dan komai ba sai dan na fahimci shin wani hali ta dauko na rashin da'a wanda ya cencenci na kawota na yi mata bulala, ko kuwa mun yi wasa an cin matan da gaske?"

Cike da jin kunyar Sirikin nasa ya ce" Alhamdulilah, a zamana da ita zan iya cewa dukkan namijin da ya dace da uwar gida irinta zai rayu cikin salama, babu abinda ta aikata da zata fuskanci duka ko tsawa, ina fata ta gama rayuwarta a karkashin innuwar aurena na birneta ko ta birneni cikin aminci da salama.......,"

Ya dan sasauta, domin magana ce yake yi tsakaninsa da wani sarki, koda sirikinsa ne ba matansa bane, kai zai iya cewa yana zama suda sarkin zance ne idan yana gaban yan matan nan biyu da suke gannin maza a yadda suke, bama irin tuzuruwar kauye, takan shanye masa man kansa tasssss abinta

A hankali ya dora daa fadin" Akoyma maganar rashin fahimtar, domin na yi mata tambayoyi dan mu samu matsaya sannan mu san ta inda zamu hau binciken, idan baka manta ba ka yi kirana a jiya kana yi min jajen batan bafana kuma mahaifin iyalina na sanar maka yana hannuna harma nake sheda maka ba shine mahaifin NADIRAH ba na fayace maka abinda aka aikata min har ka samu bacin rai da rikicewar tunani ?, To a yanzu zan sanar maka ina kyautata zaton a zuwanta amarci tun kafin a fahimci lalurar dake tare da mu an hadata da ciwon a jikinta............, Dan kawai na dan kwatanta mata ciwon a tare da ita ne yake ba a tare da ni ba, dan mu samu mafita mu nemi magani ne ta dan rikice...........a wannan fannin takan rikice dama, sai a hankali kuma ta gane........................"

Da mamaki, muryarsa da alamun bacin rai ya ce" Subahanalah, Kana nufin lalurar nan dama a tare da ita take?"

ASADEEK ya dan yi jimmm, kafin ya bashi amsa a nutse yana dab kawar da dubansa tamkar a gabansa sarki Muhammad yake

Sarki Mohammed ya ce" Ka ji rashin hankali, aiki irin na wanda bashi da tunani!, Ita fa HUZNAH dama mahaifiyarta kan cewa sai an yi mata nema irin na kishi, domin tana da wannan matsalar sosai har aan sani, in ba rashin hankali ba abin nan da yake jikinki, namijin bai fito maki da rashin da'a ba ke zaki yi masa rashin wayo?, Ko a ina ta hafu da ciwon sunnan ciwon a jikinta ba a jikinka ba, takan mance kai sarki ne ko wani lokaci aurwn wata na iya kamaka ? Ko a rashin adalcinta da son kanta so take a tsaya iya ita kuma jiki da jinni? Sam bata yi aiki da ilimi ba, ta kuma so kanta da yawa, ka yi hakuri da hali na shirme da shashanci irin na wasu matan, manyanma wani lokacin idan suka tafka maka wani abin sai ka samu kanka da jin juwa,sai hakuri ana tafe ana taro su ne su, in sha Allah zan taso jakadiya da dan taimako dan a talafa maka, a irin wannan halin da kake ciki idan bata yi hankalin kwontar maka da hankali ba ai bata isa ta tayar maka ba, ka yi hakuri, ko aikin waye in sha Allah zai karye, domin mun sha haduwa da irin haka a kauyen nan, ka san mutane akoy son kai"

Dan murmushi ya yi shi dai bai ce komai ba har Sarki ya gama fadansa, ya kuma tabata HUZNAH ta cira bata nuna ba dan abanta bashi da sauki a kan lamarinsu, sannan ya tabata za'a sama mata maganin bi izinillah.................
Sun karra tataunawa a kan damuwar dake gabansa, dan kuwa yakan sanar masa wasu sirikansa sannan suka yi salama ya mike ya fice da wayar a aljihunsa ya sauko yana adu'ar Allah ya sa bata yi tafiyarta ba

Rarashi ya yi kafin take yarda ta mike su fice bayan Sarkin yanka ya shaida masa sunna iya fitowa gidan ya dinke da jama'a ana cakude ba lalle bane a gane fitowarsa daga bangarensa

A hankali suke tafe har kusan motarsa dake bangaren nasa

Da kansa ya zagaya wajen da zata shiga ya bude mata yana kallon idannuwanta dake cike da ruwan rigima yana murmushi har ta zauna ya dan gyara mata abin rigarta sannan ya zagaya ya shiga inda direbansa ya bude cike da mamaki da kuma kamewa gannin UMUGHLUK ITIBEL ya budewa mace mota ta shiga

Yana zama a hankali ya janyota jikinsa ya rungumeta a kirjinsa, motar ta daga ta shiga tafiya yana bin masarautar da kallo, tarin jama'ar dake kai kawo , kowa da shagulgullan dake gabansa, ama bangarensa daidaiku ne dake son ganninsa manyan mutane sunna jira har ya tashi daga barci cewar masu tsaron kofarsa
Chapter 91 · 0% Book details