Sashe 97
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Auta dake share hawaye ta kalleta itama a lokacin da HUZNAH ta kalli Auta a rikice ta ce" Dama ke ba mahaukaciya bace, dama kema tana son sai ta aikata masha'ar nan da ke?, Ashe dama abinda yake faruwa kennan idannuwana suke rufe nake ikirarin ni mai miji ni mai kishi ni mai son miji?, Mijina na cikin wannan hali na kasa gannin komai na kasa bashi talafin komai har bake ikirarin na masa adalci na zauna da shi tsayin shekaru bayan babu aurataya a tsakanina da shi yanzu ya min kishiya zai watsar da ni? Ashe nice ya ji kai yake tausayawa yake rike da ni domin Allah? Lalle babu marar hankali, marar tausayi, marar jin kai, wace banda kanta babu abinda ta sani irinta a duniya, a hankali hawaye ke zirara ta cikin idannuwanta, muryarta a raunane ta rungume NADIRAH a jikinta tana fadin " Innalilahi wa inna ilaihi rajune, tabas babu irin rikicewar da bata sameni ba sakamakon shigowarki rayuwata, ashe ke din adala ce, mai jin tsoron Allah ce, mai kuma sonmu da zuciya daya ce? Dan Allah nima ki yafe min irin abubuwan da suka ringa faruwa a tsakaninmu, ciki harda zarginki cewa ke kika min maganin rashin lafiyana bayan baki jima da shigowa rayuwana ba da ta mijinmu, Auta dan Allah ki yafe min kema, na gabatar da huldarmu a hali na ban damu da ke ba, ni in ba mijina ba babu ruwana da kowa nasa ko ke ce, son zuciyata ya min ilah, na dauki shakara da shekaru ina cutar da shi, a yanzu da ya samu lafiya nake son in kara wulakantashi da girmanshi da darajarshi? Ya Allah ka yafe min wannan kuskure nawa, yanzu da kema muguwar ce da shikenan kin gama da mu domin nu kishina bai barni na ga wacece ke ba, mijinmu kuwa a ranar farko da kika shigo matsayin matar aurensa kika tafi da dukkan wata nutsuwa ta kamewa wata macen da ba ni ba , watau ya kamu da soyayarki, wannan shinema dalilin da ya sa na sake kulatarki dan ban saba ganninsa a halin begen wata da binta da kallo bayan ni ba........"
A dole suka katse sunna sauraron hukuncin Umma, wanda ya sa ta sake saka ihun kuka tana sake zubewa kasa, ace ita Umman Asadeek yau an wayi gari za'a yi mata bulala dari a bainan nasi, sannan a wuce da ita gidan yarin gidan nan daurin shekarun da ta tabata sai dai gawarta dan bata tashi auna shekarun da nata ba sai da aka sanar mata cewa zata yi su ta gane da wahala ta maimaita su a duniyarta, itace zata je waje mafi kaskanci mafi rikita tunanin bawa ta rayu a cen tana hangen yar bayi a matsayin matar ASADEEK? Itace zata wayi gari ba uwar ba ribar,? Take ta ringa jin wani irin suka a zuciyarta mai tsananin gaske tana gannin yadda yaranta ke ihun kuka sunna kallon bulalar dake hannun Sarkin yanka tafkekiyar da ta tabata daya tak ta isa ta kunce notikan kanta baki daya ta kasheta, itace za'a zazabga masu, sai dai dama dama su, sunna da damar wata rayuwar, itace tata ta kare, ta sani ba zata taba yin tsayin rai ba a gidan yari, ba zata iya ba, idan ta je ta samu mutanen da ta aika gidan yari su kadai sun isheta UKUBA A GIDAN DUNIYA!
N asaraki aka bude, shafinsa mai tsayin gaske, wanda sanadiyar wannan aiki nasa harta rayuwar garinsa sai da ya ja aka bincika
Da aka fara zayanowa sai da ya'yansa suka ringa silalaewa daya bayan daya sunna guduwa, dan sai sukka fara jin tsoron kar aje shafi ta shafe su, wannan masifa da me ta yi kama? Lalle da ake cewa giyar mulki na haukata wasu to fa wannan ta haukatar da ubansu da kuma matarsa mai taya shi, inda Allah ya taimaketa bata san da maganar kisa ba sai da ya sanar mata a gidan yari, laifinta na taimakawa ne kawai wajen wasu munanan aikin bale wannan da ake shirin aikatawa watau kashe ASADEEK
Kuka take yi kamar zata mutu
Asaraki kuwa tamkar gawa kasa kawai yake kallo yan auna duniyar da abin cikinta yana mamakin da bata da tabas? Yaya zata ringa jan shi zuuuuu lokaci daya ta baro shi a cikin sahara tsaka tsakiya ga zafin rana ga rashin rakumi ga rashin ruwa ba tufafi bale takalmi? Sai rayuwarsa ta jagaliya ta ringa dawo masa, har zuwansa saman karagar mulki
Hakane dama, idan kace ci da karfi zaka yiwa rayuwa zaka sha kallo gannin idannuwanka......
A kausashe MAI DAMAGARAM ya fadi nasu sakamako ta hanyar tsare su da tsatsaruran kallo ya ce"
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```

*https://www.facebook.com/106494781436168/*
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
_FREE BOOK_
*Na*
*SAJIDA NIGER*
7️⃣0️⃣
A kausashe mai Damagaram ya fadi nasu sakamako ta hanyar tsare su da kakausan kallo ya ce" Kisa ta hanyar rataya a gidan duhu ne ya hau kanka Asaraki!, Matarka kuwa gidan kaso na shekara goma sha bakwai da horo mai tsanani da kuma tara ta makudan kudi dan ya zamo ishara a gareta da dukkan mai hali irinta!"
Tabas waje banda kabara da hawaye da rikicin matasa kan su a basu macutan Aban datawa su yi masu gunduwa gunduwa babu abinda yake tashi
A hankali ASADEEK ya saki sandar nan, sannan ya shiga warware rawanin dake kansa, wanda hakan ya saka kowa hankalinsa tashi
Me yake nufi da warware rawanin kansa? Ba dai sarauta zai ajiye ba?
Hakan ya sa kowa yin dif yana kallonsa har ya karasa warwarewa sannan ya sauke rawanin gaba daya saman wuyansa yana kallon mai Damagaram da jajayan idannuwansa a hankali ya ce" Na tuba aboki, a kai Tuzuruwar kauye gida kar ta summa, yaron ciki ne da ita kar na shiga uku na rasa wajen hutu............"
Kasa kasa ya fadi abin, sosai kasa kasa, mai Damagaram din ne kawai ya iya ji, hakan ya saka shi sakin murmushi hawaye na zuba a gurbin idannuwansa kamar yadda ASADEEK shima nasa idannuwan ke zubar da hawayen
A hankali mai Damagaram ya ce" Alhamdulilah, Allah kennan, mai kawo sauki cikin zafi, Allah ya buda ido lafiya.........."
Sannan ya kalli wajen Sheikh a tausashe ya bada damar a je a mayar da su gida su dukansu, dannan dukkan wanda ba zai iya kallo ba ya tafi an bashi dama
A zabure ASADEEK ya juyo sanadiyar jin tsinkewa da mari mai karfi da fasa ihun muryar mace ya zuba masu ido, BAHIJA ce ta dankaro da gudun balaki, sai dai bata idasa zuwa jikinsa ba yaronsa ya dauketa da gigitacen mari dan ya farkar da ita daga mafarkin da take na son rungumar UMUGHLUK ITIBEL, hakan ya saka ta saka tartsatsin kara ta zube a kasa, a haukace muryarta na rawa ta ce" DAMA KAINE UMUGHLUK ITIBEL?, KAINE WANDA IYAYENA SUK CE ZASU AURA MIN NA KIYA NA CE NI AKOY WANDA NAKE SO, ASHE KAINE WANDA BAKE HAUKA IDO RUFE? KAINE WANDA NAKE JI KAMAR ZAN MUTU IDAN BAN AUREKA BA? KANA SANE KA KYALE NI NSKE HAUKA? TO AMA NI MENENE LAIFINA? INA CE KA SAN CEWA NA BIJIRE MASU SABODA KAI, KAINE KA ZO GIDANA KACE KA ZO SABODA NI, DAN ALLAH KA DUBE NI, BANI DA RUWA BALE TSAKI A SHIRYE SHIRYEN SU, BAN SANI BA, BABU RUWANA, NI DAI NA SAN INA SONKA, KODA MATA HUDU NE DA KAI KA SAKI DAYA KA AURENI, BALE SU BIYU NE BABU RUWANA DA WANI LAIFINSU, NI KAI NAKE SO ZAN KUMA RAYU DA KAI, DAN ALLAH KA TAIMAKENI KA AURENI IDAN BA HAKA BA ZAN IYA MUTUWA"
Turus suka yi, su biyu da ake neman rakawa, suka juyo sunna kallon ikon Allah da kuma shi din dake tsaye yana kallonta
HUZNAH ta sake kallonsa da kyau, kasa kasa ta ce" NADIRAH, kar fa zuciyar tausayin mijinki ta hayo shi yanzu, ina mai tabatar maki yana iya auro wancen ya kawo mana mu shiga uku, ke kin ga alamun zata barmu a dakunnanmu kuwa?"
Nadirah dake ta shashekar kuka ta yi tsuru tsuru, kasa kasa ta ce" Me zai hanna ya zo mu je ya yi barci? Ni fa du ganni nake yana iya summa, in ba haka ba babu inda zamu je, kin san Asadeek zai iya aurotan kuwa? Wace ta bijirewa iyayenta saboda shi tsaf zata ci mana uwa Aunty"
Ikon Allah Jakadiya ta tsaya kallo dariya na cinta, Auta kuwa kawai dolema ta saka yar dariya tana rungume hannayenta tana kallon tsayuwar da suka yi suka harde hannaye
Sheikh shima dariya ya yi yana girgiza kai, ya bada umarnin a tafi da ita gidan baki, a bata dama t dawo hayacinta sannan ta koma gidansu na familly , domin sarauta ta sauka daga kansu tuni, an dora ainahin dan sarkin mai adalci, jinnin sarauta mai mutunci, da kyar aka cicibeta tana dirari tana ihu tana waigo shi aka fitar da ita, shi kuwa ya sauke ajiyar zuciya yana dawowa wajen mai Damagaram a zuciyarsa ya dauki niyar in sha Allah zai taimaka mata, zai saka a sakata a hanyar da idan ta yiwa kanta adalci zata ji dadin rayuwa ta tubarwa Allah, in kuwa ta ki shikenan, shi dai yanzu kuma gaskiya matan cen biyu da suka juya bayan an tafi da ita baya tunanin zasu bari ya karro wata, to tuzuruwar kauye har ba zata ce a rabu bs? Ta aika tace a rabu ya shiga uku
Sai da komai ya tafi yadda ake so sannan baki kowa ya kama gabansa, matasa kuwa sai da ya yi magana da babar murya cewa babu su babu tarda ahalin asaraki, su barsu su rayu yadfa suke so, du wanda fa ya tada doka koda da sunnansa ne sai doka ta taka shi!, Da wannan ya shige gidansa, bangarensa ya tarda matan rayuwarsa, su uku an yi girki na gani na fada abin mamaki ana zaune ana hira harda wasa da dariya