Sashe 39
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri Indi ta mike tana cire alkyabar nan ta kuma warware gashinta ta cuje dan kwalin ta ce" Wa bilahilazi ki yi bakinki ya fita innata a kashe mu kafin mu yi ceton bale na komawa Aminun, Astagfrulahi ina ita ina kwartanci jama'a tsofai tsofai da ita, Umansu ce fa, ai ba zata fara ba Innata, bara na wanke abin nan kaikayi yake min a fuska bama na gani da kyau na zo mu yi carafken nan, jiya a tara na fadi ba manta ba"
Da ido innarta ta rakata, sai kuma ta sauko kasa tana cire daurin da aka kafa mata itama ta rafka tagumi a bayane ta ce" Oh ni ta Habu na shiga uku yar nan tana tune da shegen nan wuya uwa marikin lema?, In sha Allahu Indi ba ke ba Aminu, yau dai da gani ga UMUGHLUK ITIBEL?, Kai jama'a da babu abinda zai hannani fashewa da kuka, yo ni ai Adu'a nake yi kar na fada masa su waye mu mu shiga uku, Je ki dawo mu yi carafken ko na manta wannan tunani na matar nan kamar kwartuwa, dan nima ji nake yi kamar na yi sabo walahi, mace baba haka ina ita ina irin aikin nan?, Kawai itama tana magana ne tana lumshe lumshe ga wasu idannuwa kamar maya sai ta kureka da kallo, in ba wannan ba ai.na za'a yi mata wannan tunani ba sam, sai kuma wasu magangannu dai irin na yan iska, ama in sha Allahu inaga ba zata kasance kwartuwa ba sam, ai ko dan gudun kar danta ya karta zata kiyaye ai ba kyau kwartanci ".............( Allah dai ya taro ki Hindu madam)
__________________________________
Washe gari haka aka tashi da baki, kamar koda yaushe, sai dai na yau manya manyan baki ne dan yi masa barka da sabon aurensa,
Haka ya wuni amsar bakin har yama ta yi ya kowa ciki dan samun dan hutu kafin lokacin sallar magariba ta yi
A irin lokacin ne kuma ya sake samun wani lamarin na matan uku dake rayuwarsa, wani zaman, da wani shirin daban, domin da gaske Umma ta dage sai matar da aka daura masa ta zo ta gaishe shi, hakan ya sa ta ki zuwa kawota danma kar su dawo su tardo ya shige barci, sai kawai ta tura Baiwa cewar maza a rakota , idan ta fito jakadiya ta yi jagora a rakota
Sosai HUZNAH ta karra kimtsa zamanta, Auta kuwa ta bude litafinta tana nuna masa cewa zata bashi hardar wata Adu'a da ya koya mata a kauye
Baiwar ta samu shiga falon domin sakon UMUGHLUK ITIBEL ne
Tana shiga NADIRAH ta fito daga kicin, hannayenta sanye da safar hannu, kugunta daure da abin girki, girki suke yi ita da innarta, fuskarta da kwaliyar da akai mata, ama ta cire tufafin ta mayar ta ninke , gashinta a baje yake a bayanta, girki suke gwadawa ire iren WA'INDA masu gyaran nan suka koya mata
Har kasa Baiwar ta duka, kanta a kasa, domun ta tabata matar nan ko wacece ta jikin sarauniyarsu ce
Kanta a kasa ta gaisheta
NADIRAH ta amsa tana sake gyara daurin abin girkinta a kugunta
Baiwar ta sake sada kanta ta ce" Allah ya taimakeki, sako ne wajen sarauniyarmu, daga Umma uwar bayi, aka ce ta fito mu mata jagora baban Falo, a irin wannan lokacin UMUGHLUK ITIBEL na nan zai amshi gaisuwarta"
NADIRAH ta yi tsai tana ta kallonta, a hankali ta fahimci me sakon yake nufi, watau ana nufin ta je ta gaishe da shi babansun?
Baki ta yatsine tana dan waigawa dan bata so Innarta ta ji, domin a wannan lokacin da take jin zumudin su fitar da gashin cen ta dangwali romonsa ta zira a bakinta babu abinda zai sakata wanka ko cenza kaya da zuwa shirmen gaisuwa, wai inama ruwansu da sai ta gaishe shi ne? Su shafa mata lafiya, ko haka ake yiwa matan safakan ne? Dole sai an san ka je wajen miji? Shi yasa a sarauta bata ga komai ba sai tsabar wauta da rashin sakewa
Hankali kwonce NADIRAH ta ce" Idan kin je ki ce, na ce yanzu ina kicin, sai dai wani jikon"
A zabure baiwar ta dago, ba da gangan ba ta yiwa Nadirah kallon tsaf, a rashin gane me NADIRAH ke nufi ta ce" Sakon na sarauniyarmu ne ranki ya dade, sannan sakon daga UMUGHLUK ITIBEL ya fito, domin idan UMMA tace, shi yace"
NADIRAH ta saki lalausan murmushi tana gyara tsayuwarta ta ce" To dada, inaga a nan dai kice kawai matarsa a sanina, sai innata, idan kuwa ita zan kira maki toh sai naje aikar"
Da sauri ta sada kanta, wata zufa na neman karyo mata, ta sake sada kan nata a hankali ta furta" Allah ya huci zuciyarki, Allah ya karra girma, Allah ya karra daraja Sarauniyarmu, In sha Allah zan isar da sakon, A gama lafiya"
NADIRAH na tsaye tana kallon ikon Allah har matar ta fice kamar zata kifa
Ido ta kikifta kasa kasa ta ce" Allah mai alkhairi"
Daga nan ta koma tana yiwa Innarta hira wace ta yi bake bake a wajen Four tana jira abinda suka saka ya gasu su ciro
Tunda ta shigo har falo dan Umma ta bata damar shigowar a tunaninta tare suke da NADIRAH ta zube kasa, kanta a kasa ta kasa fadar sakon da ta gumtso a bakinta, domun har jikinta rawa yake yi a lokacin da ta fahimci kwarai da gaske ZAKIN SARAKAI na zaune
Umma da dan takaici ta ce" Ki fadi sakon mana kin tsugunna a waje kin mana shiru bayan kin ga ke ake jira?"
Kai ta sake dukarwa kamar zata kifu, muryarya a raunane kamar zata fashe da kuka ta ce" Allah ya taimakeki, sako daga sarauniyarmu, tace ace girki take yi, sai dai wani jikon"
Ba Umma ba, harta UMUGHLUK dake dan kallon Huznah sai da ya yi dan tsai , uwa Uba UMMA da ta kallota a zabure, hakama HUZNAH da sai da ta kusan mikewa dan tsorata, a gangaro kan Auta da ta dago tana zarro idannuwa kamar zasu fado tana kallon Baiwar, wace tuni take share hawaye, hawaye na tsoro, domun an hore su da fadin gaskiya, bale irin wannan dole zasu sanar da abinda suka gumtso, sai gashi, sai gashi ta gumtso mai karfi, kuma Umma ta saka ta fada a gabam Uban gidansu baki daya
Umma har hade harshenta take yi wajen fadin" Rufe min baki, wannan wace irin magana kike yi haka?, Na tabata wannan sako ba daga ita ya zo ba, waye zai shige kasam rigarta ya bata mata sunna run kafin ta ga mijinta? Na tabata wannan sako an yi shi ne dan a hadata da UMUGHLUK ITIBEL, maza ki tashi ki rakani wajen wace ta baki wannan sako, ko wacece na ganta, domin na tabata ba dai Sarauniyarmu ba!, Kuma ko waye a bayan haka zai bayana ne!"
Shi ihun da Umma ya fi damunsa, haka kuma kafin ya yi wani abu har Ummar ta fice kamar zata kifa
Juyowa ya yi zai yi magana dan HUZNAH a tsaye take itama , da niyar umartarta ta zauna sia ya ga wani murmushi ya kubuce daga fuskar Auta
Dan kallonta ya yi, sai ya samu kansa da yin murmushin shima
Muryar HUZNAH ce ta dakatar da shi a lokacin da ta duka kanta a kasa ta ce" Allah ya huci zuciyarka, na tabata da wani abin daban, ta yiwu bata gane sakon daga nan ya fito ba, bayan wannan me hadinta da kicin? Sam sakon ba naka bane"
Ido ya dan sake kura mata , haka kawai ya samu kansa da tunanin toh daga ina sako ya same shi haka? A masarautar nan? Ko daga wata masarauta, komai rashin da'ar Yar sarki ko matarsa, ba zasu turo da sako haka ba gaskiya, ta yiwu bata gane din bane, ko kuma ba ita aka ba sakon ba, shi abinda yake dan bashi mamakima shine, bata gane waye aka aura mata bane? Ko an mata nasihar zumudi ne? Dan kwarai ya yi tunanin a kofa zai tardota tana binsa da kallon nan kamar na mahaukata, sai gashi shiru
Murmushi ya sakarwa matarsa, hakan ya sakata suake ajiyar zuciya, domin damuwa ta sameta kar ransa ya bace abin ya shafe su baki daya, domin ba zata iya tuna bacin ransa ba, bata so, bata son tunawa, bata ga da kyau ba ko kadan, a ranar da ya yi bacin rai mai sunna bacin rai? Bata ga da kyau ba ita da kanta, bale wa'inda le zagaye da su
___________________________________
A haukace Umma ta shigo, bayan ta dakatar da Baiwar da ta tabatar mata nan ta shigi ta kuma kwatanta mata wace ta gani
Hankali tashe, rai bace ta dubi Inna dake rauda kai tana kallon TV ta zabura jin budewar da shigowar ta ce" Ashe bata da hankali? Ta san da wace irin wuta take son yin wasa? A tarihin rayuwata ko a zamanin iyayensa ban taba gannin an bashi amsa kai tsaye irin haka ba, hala bata da hankali da zata ce a cewa UMUGHLUK ITIBEL tana kicin ba zata samu zuwa gaishe shi ba sai wani jikon?"
Daga saman kujera sai da HINDU ta fado kasa warwas sannan ta dabi kai kamar mai shirin tayar da aljannu ta ce" Lah ha ila ha ilalahu muhamadu Rasulullah salalahu alaihi Wasallam, wani shegen rikaken dan iskan makaryacin ne ya gilawa Indi karyar nan? Allah na tuba yar da ko fitowa bata yi ba muna ciki muna dahuwa? Ka ga shari irin na masharanta, in itace a yau a yanzu yanzu in zama wancen TVn a ringa jona ni dan Annab............."
"Innata" Indi ta fada da dan karfi tana zarro ido dan gaskiya ba zata iya yin shiru innarta ta yi rantsuwar alkaba'i a kan gaskiya ba,
Ido ta ribga kikiftawa, hakan ya saka HINDU yin wuki wuki murya a raunane ta ce" ki bari na karasa rantsuwar nan kin ji yar indi? Ai ba kina nufin na yi shiru bane ko?, Ba zaki aikata haka wa babanmu ba ai ko?"
Indi ta yi shiru tana murza hannunta, sai kuma ta ce" Gani na yi muna girki a lokacin ne innata"