← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 99

Sashe 10

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakin ta rufe da ky ta karasa inda take zaunen nan ta duka cike da takaici ta ce" Ina kike tunanin zuwa? Ama bakida hankali yarinyar nan kwata kwata!, To bari ki ji, idan har kika yarda kika bi yayanki tafiyar da zai yi na rantse maki da wanda raina yake hannunsa kina dawowa zan makala maki mugun sharin da yayanki da kansa zai haka rami ya saka ki kanki a fili sannan ya jefe ki da duwatsu har sai kin rasa ranki......, Ke kin san ciwon wannan zai halaka shi shima dan makahon son da yake maki!, Ta rage naki , ki duba ki ga abinda zai gyara ki!"

A hankali ta dafe zuciyarta ta silale a kasa ta dora kanta a saman akwatinta ta rintse idannuwanta
A bayane ta furta" ALLAHU AJURNI FI MASIBATI, WA KHALIFUNI KHAIRAN MINE HA....." sai kuma ta karashe tana mai sakin kuka tana jin kanta tamkar zai tarwatse gida biyu

A hankali ta sake dafe gaban kirjinta, ita ba waya ba, ita ba komai ba, an amshe , yanzun a barta ta je ta yi ibadar ko zata sake neman gafarar ubangijinta da fatan ta gama da duniya lafiyama ba zata samu ba? Lalle ta fara kulatar mijinta, shin ina yake ya bari ake neman kasheta? Ba zai lekota ya ga amanar da aka bashi ba? Ba zai nemi ganninta ba ko zai karanci damuwarta? Ko dan ta rasa cikin dake jikinta ne ya tsaneta?....... A wannan rana sallah kawai take tashi ta gabatar ta koma ta nade, har lokacin tafia ta yi, tana ji tana gani ta gilawa yayanta karyar juwa take ji ba zata iya tafiyar ba, zata je haji idan Allah ya nufa, tana ji tana gani ya mata salama ya fice tamkar zata mutu dan tashin hankali, sai dai ta sake mayar da kanta ta sha madarar ruwa ta kuma fuskantar alkibla, ta san Allah yana gani, ta kuma san idan bata ga warwarewar matsalarta a duniya ba tabas a kiyama Allah zai saka mata, dan haka sai ta ringa kai masa kukanta tana fada masa yayanta dai, yayanta dai, domin babu babar fargabar da ta kai shi a zuciyarta, idan ta tuna shi takan dimaucewa, takan rasa komai nata, sai idan ta fuskanci gabas ta yi kuka ta fadawa ubangijinta sai ta ji sanyi a zuciyarta, sia ta ji kamar komai normal ne tunda akoy Allah.

A cikin JIRGIN VIP, watau wanda ya fara daukan manyan mutane dan sada su da babar kasa, kasa mai tsarki dan gabatar da aikin Umurarsu

Cike da kasaita take tafe tunda ta shigo
Daidaikun mutanen dake dan yi mata murmushi ko su gaisar da ita sakamakon shirin da ta yi wanda ke nuna ko ita wacece take dan kallo ta amsa su da dan yatsina baki ko ta dan dauke kanta
Baiwar dake biye da ita ke dan sake gyara alkhyabarta har suka karasa daga ciki wajen VIP plc ta zauna a wajen da yake nata ne domin shine numberta ta karra gyara zamanta tana maganar karshe da kawarta wace suka yi zasu hade a cen su yi wani program dinsu na harkar auren kawar tata

A hankali ta girgiza kanta a lokacin da baiwar ta karra tambayarta ko akoy bukatar wani abin?

Juyawa baiwar ta yi ta koma nata wajen cen cikin jirgin cikin jama'a tana sauke ajiyar zuciya da tunanin ta shiga ukunta da akace ta yiwa BAHIJA rakiya, ta tabbata tana ji tana ganni zata shiga garin manzo ta fito ba tare da ta yi sallah ba, watau ba tare da ta je masalaci ba, dan kuwa Bahija kashinta ne kawai ba'a wanke mata, yadda take zuba mulki a rayuwa ko ubanta bai kaita ba!

A hankali ta dan karra gyara zamanta tana daura belt, sai kuma ta shiga dan duban gefe da gefenta dan gannin su wanenen Elhazan da duka hau VIP a wannan tafiyar?

Na farko da ta fara kallo sai da ta kureshi da ido, domin sam bai mata kama da wani hamshaki ba, sai kuma ta tabe baki ta juya hannunta na dama daga wancen bangaren

Ido ta zubawa wanda ke zaune a nan, cikin shiga yake ta simple doguwar riga fara kal kal kal , kansa baya dauke da hirami ko hula hakan ya bayanar da lalausan gashin kansa, hannayen doguwar rigar kuwa har kusan tsintsiyar hannunsa daidai da agogon da sai da ta karra zuba mata ido domin ko a ido ka kalleta ka san ba ta yara kannana bace, watau ba ta mun taso nace, ta ginanu ce har zuwa dan madaidaicin Alkur'anin dake hannunsa

Wani irin yarrrrr tsigar jikinta ta bada, a hankali ta dan cire dubanta , sai dai tana juyar da kan nata ta sake juyowa ta kuma zuba masa ido, gashin kansa zuwa na girrarsa da na idannuwansa da dogon hancinsa da bakinsa sun fi komai daukan hankalinta

A hankali ta dora hannunta daidai zuciyarta tana jin yadda take wani irin buga mata

Da sauri ta rintse idannuwanta tana jin tamkar zata summa dan wani irin yannayi mai karfi dake sake ziyartarta........
'Ya salam, wannan wanene a cikin garin AGADAZ? bako ne ko dan gari? Wani yare ne? Daga ina ya fito? Hasbunnalah..........' shine abinda take ta ayannawa a cen kasan zuciyarta, har aka gama maganar a daura belt da sauransu suka daga hankalinsa a kan Alkur'aninsa, ita kuma hankalinta a kansa......ta kasa gaskata irin dokawar da zuciyarta ke yi a kan wannan bawan Allah............ Ta yarda yau ta hadu da wanda yake daidai da ita

.....A hankali ta dan sake gyara hijabinta da kuma alkyabarta ta yi dab gyaran murya dan baban burinta shine wannan bawan Allah ya dago idannuwansa su yi ido hudu da junna, sai dai kashhh har sadaden barcin dake surarta idan tana cikin tafia ya saceta bai dago din ba,

Sai da ya kai karshen karatun da yake yi a hankali ya rufe Alkuranin ya rike shu a hannunsa ya kai dubansa kan Amintacensa yana dan masa alamu da agogo dan son sannin lokaci duda ta hannunsa dake sarkafe ama bai duba ba

Lokacin ya sanar masa yana mai girmamashi sannan ya sake aunawa idan har sun yi tafia mai kyau nan da awa biyu sunna iya sauka domin sun yi tafiyar da dan yawa

Sake komawa ya yi ya gyara zamansa ya 'unshe idannuwansa yana tunna Auta, ko yaya juwar? Ko ta saketa? In sha Allah idan ya dawo zai gayato mijinta ya zo su wuni tare ko zata ji dadin hakan, shi baya so ne idan ya zo din nan ta ringa kukan sai ta bishi, bayan a yanzu shi babu inda zai iya barinta ta je nesa da shi, sai ya gamsu da yannayin lafiyarta, ga Umma a kusa tana hakuri da ita sosai tana kula da ita, bata yadda amana ba, bata yadda zumunci ba, ya tabata wata rana Auta zata dawo normal irin na kowace mace

Dan murmushi ya yi, idan har ta dawo haka, yaya zai yi da farin ciki? Ya Allah ya nuna masa

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

0️⃣7️⃣

Dan murmushi ya yi, idan har ta samu lafia ina zai saka ransa dan murna?, Ya Allah ka nuna min.....ya yi wannan addu'a a kasan zuciyarsa

Lafiya suka sauka a baban Birnin MADINA garin Manzo

Tsakanin aéroport din da Hotel din da suka dauka da dan tafia, kasancewar ga gajiyar jiya, ga ta yau sai suka shige taxi su hudu suka nufi BABAN hotel din NOZOL ROYAL dake Abi Obaida ibn al jazrah street

A hanzarce take, karra kallon motar dake gabansu biyu take wace ke dauke da mutumen da kuma jama'arsa, Adu'a take yi a zuciyarta Allah ya sa kar Motocin su bace masu, haka kuma ji take yi tamkar ta kwace motar ta tuka da kanta ko zata samu ta sada kanta a Hotel din nan

Sunna karasowa shi fita ya yi ya yi gaba, Mutanensa suka tsaya biyan kudin, a lokacin ne itama ta fito tana mikawa Baiwar jakarta ta ce" Biya shi" da sauri ta shiga bin bayan wannan bawan Allah

Kasancewar tun daga mettre dari ake tarboka dan a sadaka da dukkan abinda ya dace a wannan Hotel idan ka sauka a cikinta ya saka bai tsaya tsaye tsaye ba ya dan zanta kadan da balaraben dake yi masa magana cikin yaren larabci yana mai tambayarsa sunnansa da kuma number dakin fa akace masa an cirar masa

Dan tsai ya yi ya dan shafa gaban goshinsa kafan dan shi kam bai san number dakin ba tunda ba shi ya cira ba gaskiya,
Dan waigawa ya yi dan gannin ko sun zo, sai ya ga ta juya da dauri daga kallonsan da take yi
Murmushin takaici ya yi yana basarwa, ya tabata bata gane shi ba, tun a cikin jirgi yake mamakin irin yadda ta lakanci kallo kamar wata bagidajiya, sannan da ya ga tana yawan kallon mutanensa ya zata ko ta ganne su ne? Shi dama gaskiya ba zata gane shi ba, dan ba wannan damar, idan ba na gi da gi dinsa ba ba wai lalle ka ringa ganninsa ba rawani ba, shima a lokacin da ta cika kallonsan nan gaba daya ya ringa ji a jikinsa an kura masa ido, da farko yaronsa ya duba ya zata ko shine ke masa kallon nan dan ya ji dalili? Sai ya gane ba su bane, asalima suma sun dan damu da yannayin kallon nata, sai ya basar ya ci gaba da karatunsa sai da ta yi barcin nan ne ya dan dubeta , kamanin mahaifinta ya fara ganni sai kuma suka karra tabatar masa itace yar gidan Bafansa ce

A tausashe ya ce"ها هو الشخص الذي أخذ هذه الغرفة من أجلنا" ( ga wanda ya kama mana dakin nan zuwa)

Ido ta zarro, a zuciyarta ta ayana 'Ya salam, balarabe ne ashe? Wayo Allahna, Ya Allah ka bani ikon tunkararsa '

Da sauri suka karaso ya fadi dakunnan, hakan ya sa akai masu jagora
Chapter 10 · 0% Book details