Sashe 58
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri Hindu ta girgiza kai ta ce" Wane mutun, ina ni ina wanka, rasa yaya zan na saka atampar nan yanzu nake cewa na je wajen Wancen matar na nemi alfarmar ta rakani wajen Aban bayin Allah na fadi cewa kin bata, innaliwa shigana bayi ya fi a irga yar nsn, tashi mana" ta karashe tana lelen kafafuwan Indi
NADIRAH ta sake barkewa da kuka tana kawar da kai ta ce" Ki daina ce masa Aba, walahi bai haifeki ba, ba aban innar birni bane, ba kuma na Aban birni bane?"
Wayo dadi, wayo duniya da abin dadi take, da kyar innar Indi ta iya juyar da kanta gefe ta ringa sakin murmushi, yo jama'a in dai Indi ta ga fuskar UMUGHLUK ITIBEL ta yiwu komai ya faru, yanzu baban burinta ta mike tsaye ta dan taka, ta tabata komai kankantar halitar namiji idan ya ziyarci budurwa sai ya nuna, ah to, dan haka burinta ta ga aiki a bayane
Da harare ta ce" Ke ba zaki daina yiwa Aban marayu rashin kunya ba ko?, Taso min mana wai daga zaunen nan, yaya aka yi kika biyoma ta nan, ko wancen matar ta rako ki? Kukan me kike yi? Wai wannan rigar ta waye, kuma yaya aka yi ta zo jikinki?"
Kukan da take yi ne dif ya dauke, ta zubawa Innarta ido
Yanzu Fisabililahi ina ruwan innarta da son sannin yadda aka yi rigar nan ta zo jikinta? Gaba daya sai take gannin kamar Innarta na yi mata wani kallo daban, irin na ta lalace din nan? Kai innalilahi wa inna ilaihi rajune
_________________________________
Matarsa ya raka har kofar da ASADEEK ya kwatanta masa sannan ya dawo ya zauna yana ta murmushin da ya gaza barin lebensa
Asadeek dake zaune yana dan shan tea din da aka kawo cikin breakfast ya dube shi ya ce" Sai watsa hakora kake yi SHEIK"
SHEIK ya yi yar dariya yana gyara zamansa ya ce" Kai kuma dariyar tawa ce take damunka?"
Dan shiru ya yi, sai kuma ya yi murmushi shima yana girgiza kai kasa kasa yace" Ban taba haduwa da tsageran da nake jin zan yiwa biyaya ba sai a kan yarinyar cen, cewa fa na yi ba inda zaki, ko irin tace min in barta dan Allah ta tafin nan, kai tsaye ta tunkaro hanyata idona cikin nata, gaba daya bata da kunya SHEIK"
Dariya kam yanzu Sheikh ke yi tsakaninsa da Allah, shi dai a haife ya haifi ASADEEK, girma ne ya dame shi kai tsaye bawan Allah, hakan ya saka shi aron halaya irin na manya gaba da baya, ga halin datako kamar wani mai manyan shekaru, bawan Allah bai taba ganninsa da yannayi irin na fara'a haka ba, tunda yake,
Haba ya dan dafe ya ce" Kuma kana ji?, Yawanci fitsararun nan sun fi tsaye mana tak a rai, ka duba ka ga maman Safwan, ranar nace kar a min wake a gida bana so, ta yi ta kwaliye shi na rangada, sai da na gama take ce min shine, kuma idona idonta kurrrr sai ni na kawar da kai, kuma har ga Allah na fi jinta a raina"
ASADEEK ya yi dan tsam, sai kuma ya yi murmushi ya girgiza kai ya ce" Aa, ni dai ba zata kamo min mar'atusaliha ba, haba dai ai mai jin magana da marar ji ba daya bane, SHEIK yaya maganar nan take ne?, Cewar kar kowa ya sani"
SHEIK ya ce" Ka yi hakuri, ka karra bani lokaci, kar wanda ya sani, ciki harda Ummanka na roke ka"
Bakinsa ya dan tabe ya ci gaba da shan lipton din nan yana jin yana sake sakar masa jijiyoyin jikinsa ................................................................................................
A hankali ta bude ta shiga tana salama
Turus ta yi sakamakon abinda idannuwanta ke ganni
HINDU tsaye tana salalami tana bin NADIRAH da kallo wace ke Kwonce tana birgima bihaki tana ihun a kan me innarta zata ce sai ta fada mata rigar nan ta waye
Hindu ta bi matar da kallo, mace mai cike da kamala, yannayinta akoy kamala, sai dai duda haka ba zata yi gaggawar sakin jiki ko fuska ba, dan haka ta ce"
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```

*https://www.facebook.com/106494781436168/*
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
_FREE BOOK_
*Na*
*SAJIDA NIGER*
4️⃣0️⃣
Fuskarta ba yabo ba falasa ta ce" Bakuwa muka yi?, Sannu dai....."
Sai kuma ta kalli Indi a kausashe da yaren buzanci ta ce" Dan ubanki zaki daina burgimar da iface ifacen nan ko sai na tatakaki ne a gaban wannan, wacece ita ne na ga ta biyo ta nan itama ko hanya ce da kowama zai iya bi?"
Murmushi matar ta yi tana dan sake dubansu, zuciyarta ta cika da matsanancin mamaki mai masifar girman gaske, haka kuma Hindu ta bata daria, ko dan ta ga fatarta baka tana tunanin bata jin yaren? Abinda dai ya fi dan cika mata zuciya da tunani shine, Sarauniyar garin Tanut ce akace, kuma uwa ga yayan Agadaz ke burgimar nan ko yaya?
Gannin ta ki bada amsa ama kuma ta dakatar da burgimar ya saka Matar SHEIK yin murmushi ta ce" Ki yi hakuri Hajia, dama ni din Matar SHEIK ce, kuma likita ce, na zo dan na duba Uwar Agadasawa ne"
Dan shiru HINDU ta yi, matar Sheikh? Wannan kamilalen mutumen da akace sunnansa SHEIK, na gefen UMUGHLUK ITIBEL? Lah ha ila ha ilalahu muhamadu Rasulullah salalahu alaihi Wasallam, yau gata ga matarsa
Murmushi ta saki tana kikifta ido, sai kuma ta kalli NADIRAH dake kallonsu fuskarta na nuna dukkan wani tashin hankali da Rigima a tare da ita yake
Yawu ta hadiye, kwarai kuwa abinda take tunanin ya faru fa da gaske ya faru
Wayo Allah ga abin rangada buda da dimar rawa ama ba hali Nadirah ta mata tsuru da ido
Da sauri ta karasa inda take ta duka ta kamata tana fadin" Tashi mana, mu je ciki, baiwar Allah Bismillah shigo shigo, dan rikici ke damunta, zo mu je dakinta ai in dai dubawar da nake tunani ce sai a daka ko?"
Ita dai Matar SHEIK biye take da su, baiwar Allah NADIRAH da kyar take takawa, wajen ne ya karra yin tsami, ga rikicin dake damun kanta mai yawan gaske
Bakun makeken gadonta mai kalar gidan sarauta ta zauna tana sada kanta, Inna ta yi murmushi kasa kasa ta ce da Matar SHEIK " baea na barku, zan zaga bayi cikina ya fara murdawa"
Da ido ta rakata sannan ta maido dubanta Kan NADIRAH
Dan murmushi ta saki ta cire hijabinta da nikaf dinta hakan ya bayanar da nutsatsiyar kamilaliyar fuskarta
Jakar ta bude ta dauko safar hannu ta likitoci tana kallonta ta ce" Bismillah Allah ya karra maki lafia"
NADIRAH ta dago tana kallonta, Bismillah me?
Matar SHEIK ta karasa tana fadin" Baya zaku kwonta sai ki cire wandon ki janye rigar baya na duba da kyau kin ji?"
Ido ta zarro da matsanancin faduwar gaba da tsoro
Bakinta har yana rawa ta ce" Na cire wandona kuma? A kan me za'a wani dubani? Babu abinda ya sameni fa ni"
Ido ta zuba mata itams, karara ta fahimci ko me yake damun Yarinyar
A hankali ta zauna cikin yaren French ta ce" Excusez moi, je ne me suis pas présenté, je suis LUBNA MUHAMMAD, je suis la 4eme femme du Cheikh, et je suis médecin gynécologue je suis enchanté de vous connaître et je serais honoré d'être votre médecin " (Ki yi hakuri, ban gabatar da kaina ba, sunna na LUBNA MUHAMMAD, nice matar SHEIK ta hudu sannan ni docter ce a fannin mata, ina farin cikin sanninki, sannan zan kasance cikin farin cikin zamtowa likitarki)
'kan ubancen kayasa' shine abinda zuciyar NADIRAH ke ayannawa a lokacin da ta kure bakin wannan yar gayun dake yi mata yaren aljannu tana makokwaltu da baki tana hirar da sam bata san me take nufi ba har ta dire maganarta tana sake kallonta
Wannan lamari ya saka LUBNA dan sake karantar Nadirah
Magana ake a kan matar da aka ce ya ce a wajen sarkin Tanut, ba zata taba kawo cewar bata ji yaren da ta yi mata ba, sai dai ko kawai bata yi mata bane
Sake sasauta muryarta ta yi a sanyaye wannan karron da hausa ta ce" Allah ya huci zuciyarki, idan har na bata maki ki yi hakuri dan Allah, idan kuwa wani likitan kike so a kirawo bara na koma na sanar sai a kirawo ko wani likita kike so in sha Allah"
Kasa kasa NADIRAH na rage girman idannuwanta da sansanyar muryarta ta ce" Likita kuma? Ya min me?"
Matar SHEIK ta fuskanceta da duba irin na tsanaki, a hankali ta dan kara matsawa kusa da ita kadan ta ce" ki yi hakuri Hajia, kin san wajen nan waje ne mai matukar hatsari, waje ne da ba'a so a yi wasa da shi, bale ke da iliminki da hankalinki, idan har ya zamto an yi wasa da wajen nan kuma ya raunata akoy katsala, kin ga a wannan fannin ba maganar ka ji kunya, domin ciwo ne, idan ya giga kaine ka shiga uku, idan ya zama gagarare kaine a babar matsala, zai iya gagaraka shiga mutanema bale har ka anfana da shi, yana iya hannaka zaman aure gaba daya, shi yasa nake so ki bada hadin kai a duba ki, a duba wajen dan kowace mace da kika gani ta haka ta girma, wata bata samun matsala kwata kwata, wata kuwa tana samun matsala kadan ne da ruwan zafi kadai ya isa ya warkar da wajen, watan kuwa har tsagewa take yi watau ta damu karuwar da sai an yi mata dinki kin fahimta?"
A tsorace ainun, a matukar tsorace NADIRAH ta sake rage amon muryarta tana sada kai irin bata son hada ido da Lubnar nan ta ce" Hala kin san abinda ya faru da ni?"
Itama LUBNA sai ta samu kanta da kafeta da ido, a zuciyarta kuwa tana ayana wai me yake faruwa ne?,
Turewa ta yi ta fito mata a mutun ta ce" Ba shine sanadiyar kirana ba? Ko ba kin kawo budurcinki bane?"