Sashe 83
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
NADIRAH ta turo baki, sai ga hawaye shap shap shap ta shiga sharewa tana kallon innarta, da hannunta ta ce" Inna, bama wannan ya fi yi mini ciwo ba, wai sai ya ce NADIRA gatsau, ita kuma yace HUZNAH, innata me na masa da zafi? Inace in kina kirana har lumshe ido kike yi, kece kika ce du duniya bakya jin dadin sunna irin nawa ko? Wai wani Matata ko kunya baya ji s matsayinsa na abanku!, To ta Allah ba ta mutun ba, da yace kar na kuma masa maganar Aminu yanzu na fara dan Allah ya kasheni ya huta!, Yo inama dalili wai Fisabililahi ashe ya san wacece ni nake zaune tun sarai yana wani ce min Bahija, bahijar nan sai na ci uwata ni din nan innata Allah kuwa, kuma mu jira shi ya zo ya fadi hukunci na san dai bai fi saki ba, ya sakeni mu karra gaba ba cuta ba cutarwa ah to!"
Auta yadda ka san zata kifa haka take kallon salamamen tuburaran bakon iya shege a gaban idannuwanta
Bata idasa tantancewa ba ta kifa din a lokacind a Inna da zafin rai ta ce" Cuta ta nawa kuma dan ubanki da cikin ina zamu je? Ai du tsiya mun liku sai dai hakuri kaska a jikin kare?..........
Wayo udona😭🥹🥹🥹🥹
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```

*https://www.facebook.com/106494781436168/*
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
_FREE BOOK_
*Na*
*SAJIDA NIGER*
6️⃣0️⃣
A kusan tare muryoyinsu ke tambayar CIKI? idannuwansu a waje
Shiru inna ta yi tana kallonsu, bama kaamar y'arta da ta tino irin nata haukan, watau nufi irin na nata cewar zamanta da zaki na dan lokaci ne, hum, koda yake tama kyaleta ne, da kanta zata cenza ra'ayi tunda gashinan karara ta nuna bama kashe bane ya fi bakanta mata irin runanin yana kiran dayar da mene, dayar kuwa da me?
NADIRAH na kallonta a tsaye , muryarta a sanyaye ta ce" Innata ciki?"
Innarta ta fuske sosai, a maze ta ce" Ke kila wa kala ne"
NADIRAH ta sake zuba mata ido, sai kuma ta kalli Auta
Ta dan jima ta kalli wannan , ta kalli wancen, sai kuma ta juya ta nufi dakinta jiki ba karfi kwata kwata
Tana shiga Inna Hindu ta zauna tana cire zumbulelen hijabin kashe su ta ajiye carbin a gefe tana sauke ajiyar zuciya sannan ta kalli Auta dake kasa tun faduwar nan ta ce" Taso mana autata, yar karama , yan matan Hindu gajera, zo nan"
Daria ce ta kubucema Auta, a dan rarafe ta karasa dan kafafuwanta har kamar sun mutu ta zauna tana dora kanta a saman cinyar Inna
Inna a hankali ta ce" Tabas ciki ne da ita, sai dai dan Allah ku kama bakunnanku, kar ku saki maganar nan ta fita yanzu, domin cikin bai wani yi kwari ba, kai ko kwarin ya yi ku barshi ya rayu a boye, idan Allah ya budi ido du mai son ganni da wandama baya so zai gani, ke kin san a inda Abanki yake, kin san su waye ke zagaye da shi ko?"
Kuka ne ya kubucewa Auta, kuka mai tsuma zuciya, hakan ya saka ta rungume kafafuwan inna sosai tana zubar da hawaye
A sanyaye ta ce" Alhamdulilah, ko yanzu raina ya bar gangar jikina na godema Allah Mamah, na godema Allah, na kuma tafi da farin cikin gannin lalle Ubangijina shine gagara misali, Mamah, na san Abah babu abinda zai iya yi maku na bacin rai a dangane da abinda ya faru, ku din masu farar zuciya ne, shi kuma ya san talaka da mai Kudi ko mai mulki duka bayi muke a wajen Allah, talaka futuk na iya samun rabauta fiye da sarkin da ya zalinci bayi, shi yasa yake addu'a tun karfinsa tunda sarauta ta zamo masa dole, kar Allah ya dora zalintar bayi a zuciyarsa, Allah ya shiga tsakaninsa da aikata haka......, Mamah yanzu yaya zan yi da farin ciki? Mamah ina son yin waya da .......
Ina son yin waya da ............" Sai kuma ta yi shiru tana lumshe idannuwanta, domin sai ta ji matsananciyar kunyar kiran mijinta mijinta a gaban Maman, sannan bata saba kama sunnansa ba ko kadan
Inna Hindu dake share nata hawayen, muryarta a shake ainun , tana cikin yannayi ne na tashin hankali da kuma farin ciki, ita da kanta bata gane cikin Nadirah ba sai yanzu, emotion biyu sun hade mata, wani irin farin cikin hakan , domin a gidansu zata iya cewa Nadirah ce kawai ta yi dacen daga shiga sai dauka, mamantama sai da shekaru suka ja ta samu cikinta, bale ita gata cikinma bai samu ba, ama ga y'arta nan Allah ya kawo, wannan farin ciki dole ta yi ta ibada tana godewa mai sama, sai kuma tashin hankalin inda yar uwarta da mijinta suke, tabas wannan din shi zai fi disashe komai, sai fatan Allah ya bayana mata su
A sanyaye ta ce" Auta?, Shin wai me yasa mijinki ko a leke ba'a ganninsa? Ba shi babu danginsa? Menene ya sa ya barki ke daya a wajen nan baya zuwa ba kuma ya kira?"
Da farko shiru ne ya gabata a wajen, sai kuma a hankali Auta ta shiga magana kamar haka" To mamah yaya zai yi?, Da farko ya so daukeni mu gudu a lokacin da Umma kadai ce ta yi maganar kar ya kuma kirana ko a waya sai na samu lafia, sai kuma ABAHNA ya shiga maganar, domin Umma ta same shi ta nuna masa cewar dole fa sai an zabi daya, ko a barni tare da shi kulun in ringa kukan ni Abahna zan dawo, ni a kawo ni wajen Abahna, ni meye meye, ko kuma a kawo ni gefen Abahna ya hadani da likitoci a nema min magani , Abahna ya nuan ai bai ga hadin dan ina gannin mijina ko muna waya da shi ya zama matsala ba, mahaifiyarsa kanta ta tako da mahaifinsa kan maganar, a ranar Abahna ya yi tafia, Umma ta bugar da ni , sun ganni a matsayin mahaukaciya tuburan, domin shi mai gidan nawa yace sosai hankalinsu ya tashi, Umma ta hada baki da likita ya nunawa Abana dole sai an nisantani da shi mijin nawa in ba haka ba aiki ne zai ringa komawa baya, domin ba zan daina raba hankalina ba, a dole ya nemi zama da su baki daya ya gabatar masu da damuwar, ya nuna masu cewar ba zai tauye mijin nawa ba, yana iya karra aure ko ya sawaka min, duka dai abinda ba zai takura ba zai yi, shi ya nuna aa ba zai sakeni ba, ama iyayensa sun nuna dole fa sai ya yi aure, Mamah ina ji ina gani Umma ke kawo min komai na rahoton aurensa, aka yi ya tare da matar, shekara biyu ta nemi saki , wai ba zata iya ba tana rayuwa da mutun ama gangar jikinsa ta aura, ko hira take so da shi ta yi tsayi to fa sai idan maganata zata dauko, idan tana son gannin kyautatawa daga gareshi ta kyautata min, gidanta ko'ina kayana ne da hotunana , dakin mijinta hotunana, karshe dai tace ba zata iya ba, daga nan dai mahaifiyarsama ta daina zuwa, ban san dalili ba, a da takan leko lokaci zuwa lokaci, kuma du idan zata zo sai ta sanar hakan ke sakawa Umma ke makar da ni ta tsoratani, du zuwan da zata yi abinda zata tarar ya gyasa wanda ta bari...............sauki sai na Allah, a dole ta yarda na haukace, abin takaicinta danta ya ki rayuwar wani auren da wata........................"
Idannuwan Umma a rintse, cike da takaicin wata rayuwar, a sanyaye ta ce" To ke, me yasa kika zabi zuwa nan ki zauna bayan idan kina tare da mijinki duk rintsi zaki tsalake wata fitinar?"
Jajayan idannuwanta ta dago ta kalli Fuskar inna, hawayen dake diga a fuskarta ya sakata sauke ajiyar zuciya a hankali ta shiga share mata, a sanyaye ta ce" Mamah, a gabana Umma ke zuba magani a madarar Abana, sanadiyar zamana a gefensa kuwa sau bakwai ina zubar da abincin da ta zuba guba a ciki, domin wani lokacin nakan tayar da haukan karya na barar da shi, wani lokacin kuwa nakan yi summar karya ta yadda ba zai iya duban abincin ba, da addu'a da komai Allah ya sa bai ci ba, Mamah, na san ban isa na hanna ba, ama a lokacin gani nake yi ifan na matsa komai tana iya yi, har ta gane da gangan nake hanna masa ci ta tsoratar da ni da maganar mugun aikin nan da take yi, tace na jawa kaina zama a masarautar har na tsufa, kuma ta yi alkawarin idan na yi gigin sanar da maganar zata bugar da ni ta min sharin madigo, Abahna zai jefeni da kansa, shi kuwa ciwon abin ya kashe shi..............."............. Ta idasa tana mai fashewa da matsanancin kuka, kuka na samun sasaucin nauyin dake zuciyarta, tana jin yadda jikin Inna ke rawa na bacin rai, tana kuma gannin yadfa take hanna kanta sakin kukan itama mai karfi