← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 99

Sashe 33

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ta yi tana kare gaban fuskarta tana kallon Gimbiya, a tsanake ta ce" Ki tambayi mijinki girman darajata a zuciyar UBAN GIDANSA!, ki kiyayi hawa kan abinda baki sani ba, ba kowani bori ake yiwa dirar mikiya dan a sauke ba, wata jarabar ta fi karfin mutun sai dai Allah, Ki tsoraci baiwar da ta zamto Uwar sarki, ki sani kafin ta kai matakin sai da ta kawar abubuwan da ba zasu irgu ba......., Ta saka zuciyar sarki tafarfasa kuwa abu ne mai sauki GIMBIYA!"

Daga nan ta koma wajen zamanta ta harde kafa tana jiran dawowar mai gidan

Gimbiya haka take huci kamar zata fashe dan bacin rai, itama ta koma ta zauna tana sake cije lebe, wai wannan matar ce zata ce a kan me aka bar y'arta a cikin garin nan kuma aka barta da waya? Lalle itama bata san me take iya aikatawa a kan y'arta mace cilo ba!

__________________________________

Da sauri ya karra shigowa ya kuma kallon matarsa dake tsaye a kofar bayi, a tausashe ya ce" Fisabililahi Innarta ace tunda asubahi nace ta zamto a shirye sai yanzu da mai martaba ke filin gidan nan ace min ta shiga bayi? Mai martaba ne ya zo daukanta ba aike ya yi ba fa"

Itama yannayin fuskarta a dan rikice ta dube shi, ta sake komawa kusan bayin ta tsaya ta sake kwonkwasawa a hankali ta ce" Indin innarta, shin ba mun gama maganar nan bane da ke? Ki fito mana Indin innarta ko cikinki ne ya kunce?"

NADIRAH dake tsaye ta sake hade bayanta da jikin kofar ta yi shiru, bata amsa su ba

Mahaifiyarta ta fita da sauri ta janyo hannun HINDU dake kuka kamar zata mutu dan rabuwa da NADIRAH ta dungurota ta ce" Ba mun gama magana ba? Ban san me kuka tsara ba ki ce mata ta fito Sarki ke jiranta fa?"

HINDU ta ja hanci ta cire kai ta ce" Ace, kamar yar da aka tsinto a jejin sambisa? Kowa na tsoron kar aje yar oga ce ta giga ta zama oga? Haba dan Allah ku ce masa a je da ni mana, fin karfin a ya yi yawa, banfa ce zan bita gidanta ba, ama a je da ni har a daura auren azaluman su tafi da ita mana ina tsaye ko?"

Da takaici FADIME ta budi baki zata balbaleta da fada Abanta ya dakatar da ita ya ce" Ki je ki ce gatanan fitowa bara na bambare kofar tunda ba zata fito da laluma ba, ke kuwa Hindu Allah ya shirye ki"

Kasa motsawa ta yi, ta je wajen sarki ita?, Har sai da Aban NADIRAH ya sake waigowa sannan ta fice da dan sauri ta fita

Wajen motar ta nufa tana ta addu'a a cikin zuciyarta ta dan tsaya daga wajen direba zata buga sai gani ta yi an bude bayan da wannan kallon nasa na wuce gona da iri ya yi mata murmushi ya ce" Bata son rabuwa da ke ko Fadimata?"

Da sauri ta ja baya sannan ta duka kasa gaba dayanta kanta a kasa ta furta" Barka da warhaka Allah ya karra maka lafiya"

Ido yake kallonta da shi kamar zai cinyeta, sai kuma ya yi murmushi ya kada kai ya ce" Ban taba jin bana so a min kirari ba sai a kanki, tashi dan Allah ki sanar min bata son zuwa ne ko?"

Fadime ta sake sadda kanta ta girgiza kanta da sauri ta ce" Allah ya karra maka lafiya wace ita zata ki bin umarninka? Allah ya hucii zuciyarka za'a fito da ita yanzu in sha Allah"

Kai ya karra cirawa ya ce" Ta isa ta kiya, kuma ina mai tabbatar maki babu abinfa za'a yi, yarki ce fa Fadimata, yanzu sanar min, shin ta san abinda zata je yi kuwa? Kuma tabbatar min ta yarda da hakan kuwa? Jaddada min ai ba zata kiya ba ko?"

Karra sada kanta ta yi gabanta na karra faduwa da irin girman zaluncin mutanen

A sanyaye ta ce"Ba zata kiya ba, in sha Allah zata gabatar da komai bisa tsari"

Murmushi ya yi yana gyada kansa ya sake duban hanyat, sannan ya karra kallonta ya ce" kin sani, abu ne da zai zamto farin ciki ma kowa, ciki harda ke da ita, domin yana kasancewa nine zan zamto mau mulkar AGADAZ, Fadimata hakan na nufin kema kin zama gimbiyar Agadaz, kuma ba zan taba bari wani abu ya sameta ba ai kin fahimta ko?, Ci gaban kowa ne da izinin Allah"

Fadime ta lumshe idannuwanta, tana mayar da hawayen da ya taru a gurbinsu, bata ce komai ba, hakan ya daga hankalinsa, harma ya dan fitar da kafarsa ya ce" Ko akoy wata damuwa ne?"

A hankali ta girgiza kanta ta ce" Dama, akoy kanwata, wace ta raini NADIRAr, Ita NADIRAH din ce ke kukan zata je da ita, ba cen bavan garin ba, iya Fada Allah ya taimakeka, da zarar an daura an tafi da ita, ita kuma sai ta dawo, shine tsaikon da aka samu, ama zasu fito yanzu in sha Allah "

"Ita kanwar taki, bata da magana? Kuma ta san me ake nufi da maganar?" Ya fada yana sake kallon Innar birni

Fadime ta gyada kanta ta ce" Ta san komai, sannan ta iya bakinta, hasalima tana tare da komai"

Lebensa ya cije yana tuna irin rikicin da ya barro Umma tana ta masifar sun cika sake da abu da suka bari wasu suka san maganar bayan su biyu kadai, to idan ta ji ga wata ta karru yaya kennan?

Baki ya tabe yana dage kafadu, domin a sanninsa shi ba sa'an yinta bane, sai dai ta nemi wasu daban

Dan murmushi ya yi ya ce" To ai da kin fadi tun dazu da an jima da yi Fadimata, su zo mu je, kin ga dare na karra yi ,karfe tara za'a daura auren bana so hanya ta san da wucewarmu"

Wata ajiyar zuciya ta sauke mai sanyi sannan ta mike ta juya da sauri, shi kuma har leke yake yi yana binta da kallo, sannan ya koma ya sake zaunawa a ransa yana ayana' To ko ke kika ce zaki je ai babu ubanda zai hanna Fadimata, ke dai rai da lafiya Gimbiyar Agadaz"

Bata jima da shiga ba sai gasu sun fito

A hankali ta tsaya daga dokin kofa tana hangensu har mahaifin NADIRAH ya gyara mata alkyabarta bayan ya sakata a motar, sannan Hindu ta shige gaba ta hakimce tana sake raya abinda ta yi niya, ai bataga ubanda zai hanna ba Walahi!,

Fadime na tsaye har motar ta bacewa ganninta, a hankali ta dago idannuwanta ta sauke a fuskar mijinta, a hankali ta dora kanta a saman kirjinsa tana jan numfashi a hankali ta ce" Na hakura Abanta, Allah ya bata nasara"

Kai ya gyada a hankali yana shafa bayanta shima a sanyaye ya ce" Allah zai rakata a dukkan motsinta, in sha Allah ba zasu sakata a uku ba"

Da wannan suka shige ciki, a daren nan ma banda niyar kai goshinsu kasa babu abinda suka yi, haka kuma Fadima tana cike da zulumin lamarin Hindu, ita dai bata so ta aikata wani abin

___________________________________

Shigowarsu, bai saka daya daga cikin Umma ko Gimbiya motsawa ba, hasalima HINDU dake rike da ita suka fi tsarewa da ido su dukansu biyun

Da waya a kunnensa ya shigo yana amsawa ya dube su da hannunsa ya masu alamun gatanan fa

Gimbiya ta cire kanta gefe, Umma kuwa ta ciciba ta mike ta nufi inda suke tsaye sai yatsina take yi irin na raina bayin nan

Tana zuwa HINDU ta koma gefe kanta a kasa, ita kuwa ta saka hannayenta cikin isa ta dauke Alkyabar da aka luluba a saman kan NADIRAH

A hankali NADIRAH ta dago lumsasun kwartayen idannuwanta masu katon karfi a kan mai kallonsu sannan sun dauki kwali ga santsi da fuskarta ke nunawa koda babu maganar hoda ko makamanciyarta, lebenta kuwa banda walwal babu abinda yake yi na abin gyaran lebe da ake dan shafa mata,tamkar leben jarirai

Gaban Umma sai da ya kwonci kwonci ya fadi, lokaci daya zuciyarta ta wani irin mahaukacin bugawa sannan ta saki alkyabar da sauri tana ja baya

Jikinta har rawa rawa yake yi, da sauri ta juya ta damki hannun Sarki a gaban matarsa da kuma Hindu da ta zarro ido ta bisu da kallo ta ja shi cen ciki ta rufo kofa

Hindu ta hadiye yawu a ranta ta ayana' Toh fa'

Sunna shiga Umma ta dube shi kamar yadda yake kallonta ta ce" Cenza wace kuka ce zaku hada kuka yi? Wannan din wacece?"

Murmushi ya yi ya kai zaune yana kallonta da kashe ido ya ce" Ke fa mayar mata ce,wannan dai ai kin san kamar guba take a wajenki ko?, Koda yake............lamarinki sai ke, ita dai ce yar bayin, yar Fadimata"

Zaunawar ta yi itama tana mayar da numfashi ta ce " Lalle mace ce ita!, Ama ina fata ta yarda?"

Kai ya gyada yana sake lumewarsa dan barcima zai wuce shi daga nan , dan da wuri zai farka saboda nadi da hawan da za'a yi kafin su wuce da amaryr

Mikewa Umma ta yi tana sake daidaita numfashinta ta ce" bara na je na sauke su, ba za'a barta ta kwana a kasa ba, zata hau saman bed din ne"

Kafadunsa ya dage, ita kuma ta fice

Irin yadda ta ringa haba haba da su sai da abin ya basu mamaki gaba dayansu

Shinfida mai kyau harda abinci mai kyau, sannan ta ringa jadadawa NADIRAH ta saki jikinta ita din ummansu ce, ita dai HINDU kiri kiri tana zaune dar tan kallonta , har sai da ta tsargu ta fice dan jin wacece wadda suke tare wai?, Tana fita Hindu ta zauna tana sake bin dakin da kallo NADIRAH ta kalleta ta ce"Innata matar nan warin munafukai take yi"

Da sauri HINDU ta rufemata baku tana mata alamun ta yi shiru a kusa da su suke sannan ta sakar mata murmushi ta mata alamun ta zurra ido

________________________________

*Ranar dorawa budurwa daraja*
Chapter 33 · 0% Book details