← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 99

Sashe 93

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana katsewa ya kalli ASADEEK wanda harta da bugun zuciyarsa tsayawa ya yi tsakkkkk yana kallonsa

Murmushi ya sakar masa tatausa, hadi da mika masa hannu yana kokarin furta kalmar dake saman lebensa ya ga ya mike tsaye gaba dayansa, sai kuma ya ga ya duba ya kai sujada goshinsa a kasa, ya dauki dan lokaci Sannan ya dago ba wata wata ya rungume Sheikh gaba dayansa idannuwansa a lumshe, kirjinsa na wani irin dokawar da ya saka SHEIK sauke hawayen farin ciki, muryarsa na rawa ya ce" Alhamdulilah ASADEEK, ka ga hukuncin Ubangiji ko?, Shine mai karewa, shine mai badawa, shine mai hukuntawa, kana raye, kana tafe, ana hakarka ba ji ba gani, ta hanyar masu hakar taka Allah ya sako sandiyar farin cikinka, ta sanadiyar masu son gannin baka duniyar kwata kwata Allah ya sake dasa dasshen da zai tabatar da kai koda ka gushe a duniyar....., Ka gani ko? A lokacin da baam zato bama tsamani, ka ga karfin addu'a da kaiwa Allah kuka ko? Shin mutun ya isa ya yi maka wannan kuwa? Babu hanyar da za'a iya kaiwa gareka irin ta matar nan, sai Allah ya ringa bata damar, ta cikin damar kuma ya sako damar kareka..... ALHAMDULILAH "

A hankali ya ringa sauke ajiyar zuciya, zuciyarsa na yi masa rauni da tarin soyayar dake neman fin karfinsa, yana ji tamkar ya cirro ransa ya mika mata , yana ji kamar ya ringa ihun murna har sai ya zagaye garin nan
Yana hangowa shima nan da dan lokaci idan Allah ya bara masa za'a wayi gari ya ga dan jariri da sunnan nasa............., Shi kuwa idan bai bautawa ubangijinsa ya kuma gode masa ba , me zai yi? Y ALLAH

Muryarsa a matukar sanyaye da sanyin soyaya ya ce" SHEIK........, Sheikh...........ina zan kai farin cikin nan?"

SHEIK da shima muryarsa a dan sanyayen take ya ce" A zuciyarka zaka adana har Allah ya fitar maka da danka ko yarka lafiya, domin ka sani ba zaka taba rayuwa babu makiya ba, wadinnan da suka bayana sunne na fili, akoy wasu wa'inda ba zaka taba sanninsu ba ta yiwu har ka koma ga ubangijinka, ka ci gaba da godiya ga Allah, sannan ka koyi taka tsantsan, ka ga, ciki ba'a yi shi dan abinci kadai ba, dole mu boye maganar cikin nan a tsakaninmu........."

Ajiyar zuciya ya sauke yana sake matse Sheikh ya ce" Sai nake ji, kamar na fitar da ita har ta haihu......."

Sheikh ya saka hannu ya bambare jikinsa yana cewa " Malan sasautawa tsoho mana meye haka?.............."

Sasautawar ya yi yana murmushi yana kallon SHEIK dake duku duku wai ya karya shi, ya zauna yana kallonsa ya ce" Garinka fa?, Ka san idan ka fitar da ita binta zaka yi, ka sani ko a ina ne Adu'a ce zata tsareta da abinda yake cikinta, kawai aduarmu zamu nin'ninka........."

Murmushi ya yi ya karasa ya zauna shima a gefen Sheikh din , a sanyaye ya ce" Sai nake jin tsorron furucin HUZNHA, da ta ce na fi son NADIRAH a kanta........., Abinda ke min yawo a zuciya na son tsoratar da ni domin ba da wasa nake jin abin ba"

Sheikh na kallonsa a sanyaye ya ce" Dama, akan iya wayar gari, ka tsinci a irin wannan yyannayi, yan Adam muke, zuciyyar dake cikin kirjinmu bata da kashi, wani da sauki sauki fa, wanin fa wadda zaka ga ya dawo yana haukan so din ko girmama shi bata yi, lamari ne na zuciya da hukunce hukuncenta, abu daya zaka yi kokarin yi shine ka fi karfinta, sannan ka kamanta adalci a tsakaninsu, babu wace bata yi maka rana ba, babu wace bata sonka kaima ka sani, dan haka kowace ka rayu da ita da kulawa da gwargwadon kyautatawar da kake iya bata , kana yi kana tuna gobenka, ka ga kamar likita ne da yan uwanta, har cewa suka yi idan ranar likita ne ina tarda ita dakinta, ni kuwa ban taba kula da haka din bama, abinda ya sa nake dan zuwa wani turare ne da ita mai kanshi, bana so ta manta shi idan zata zo, kuma ita bata fiya damuwa da waya ba idan na shigo, sai na yi ta kiranta bata dagawa, a dole nake lekawa na tuna mata na koma"

Murmushi ASADEEK yake dokawa, gaba daya fara'arsa ta girmama, da kyar ya iya hakurin har suka yi sallah kafin suke shigewa cikin

Bangaren sirikansa suka fara nufa dan ya gaishe su

Sunna shiga ya tarar da ikon Allah, tuzuruwar Kauye ta ajiye abayar da nikafin tana shan hira da kyakyata daria a gaban Innar birni
Sheikh kam dakatawa ya yi daga waje dan ya san ana iya samun hakan, shi kuwa ya zauna kansa a kasa yana gaishe da Fatime, wace kunya ta sakata kamar zata nutse da girmamawa tana rankwafawa tana gaisar da shi, hakan ya saka NADIRAH sakin murmushi tana kallon Innar birni, har ya gama ya mike kansa a kasa ya fita

Daria ta saka tana tafa hannu , tana juyowa suka yi ido hudu da innar birni wace ke watsa mata harara, a dole ta kama kanta ta hadiye dariyarta , ta karra fuskantar Innar Birni tana fada mata irin marin da Innarta ta watsawa Umma, da irin darun da innarta ta yi a gaban ASADEEK

Du idan tace ASADEEK sai mamanta ta zabura, ama sai ta ga yar ko a ka , a dole ta cire dan ta kula Nadirah kam sauki sai na Allah kawai, ba zat kirayi Aban datawa da Aba ba!, Yanzu ta gama cin alwashin idonta idon Aminu sai ta zazabga masa mari wai ashe shi bashi da amana? Hum, ta dawo kan Auta ta ce sai ta zaneta tsoronta ta yi yawa, ita dai tana biye da ita tana wankwta daga ta yi bara baranma har ta dire kan Aban datawa
Gannin dai abin sai a hankali sai kawai ta ringa binta da ido ita kuma tana daria ta ce" Allah innar birni baki ji ba da aka ce an sace ku, kamar zan summa haka na ji, kamar na haukace fa, dan kuwa a ranar na je na fada masa komai, su inna har an yi jiran rataya sai Allah ya taimakemu bai rataye mu ba"

Da wannan hirarakin suka karra jimawa har Aban Birni ya shigo ya sanar mata ta fa tashi mijinta ita yake jira, nan ta nuna zata kwana a gidan, harda su neman yin birgima

Innar birni a rikice ta mike ta ce" Ke kar ki jiwa abinda ke cikinki ciwo mana, Indi sai fa kin daina burgimar nan yanzu dan walahi zaki jiwa abinda yake cikinki ciwo......."

Dif ta dauke wuta, a ranta wata mahaukaciyar kunya da ta sauko mata sai ta ji kamar zata nutse
Ba shiri ta mike tana mayar da rufarta ta wuce zungui zungui ta bar bangaren su Innar birni bata ce komai ba, fatanta ta yi nisa dan an riga an tona mata asiri sai hakuri

Yanzunma shi ya bude mata, har Allah Allah yake su koma gida ya dorata saman cinyarsa ya bata dukkan lokacinsa a haka

Ta waya ya cewa Sheik matarsa ta yi masa dukkan bayanin abubuwan da ya dace a kiyaye da wa'inda ya dace ta ringa ci dan samun ingataciyar lafiyar abinda yake cikinta

Innar birni kuwa kira ta yi ta dokawa har ta samu inna Hindu, ta shaida mata to fa sai an karra yin taka tsantsan, sai fa an dage da addu'a da kuma kiyayewa, daga yanzu girki idan ba ita ta yi da kanta ba sai ko in ita inna Hindun zata yi mata ko auta, kar a bata abinci ta ci daga hannun kowa, daga karshe ta shaida mata Aban birni yace UMUGHLUK ITIBEL ya bada umarnin a kawo HABU Masarautar zai gana da shi, da wannan farin cikin suka katse wayar

Tunda magariba ta yi suke zaune a falonsa, a kasa watau saman cafet sun saka salak gaba

ASADEEK kallon abunda take nufi da abinda zasu ci yake, salak ne da kwaki da yankan tumatur da yaji da ruwa ruwa wai mai ruwa , har fadi take ya tsaya ya dandana zai ji dadin abin

Allah ne ya taimake shi kira ya shigo daga bangaren Umma, nan ya samu ya mata wayo ya silale da yajin ya rufe ta waje ya tafi da kY din bangaren Ummar

Yana zuwa ya tarar da ita zaune , cikin shigarta tun ta safe, ta yi wani firi firi da ita a saman kujera yan fadar tata uku a kasa a zazaune kowace alamun tashin hankali ya gama bayana a fuskarta

Kuka ne ta fashe masa da shi, bayan sun gaishe shi sun basu waje tana saukowa kasa hankalinta tashe ta ce" Yarona, ko dai ka samu matsala da wani ne yake harin dukkan wani dake gefenka dan ya halaka?, Ka ga babu bafanka da matarsa , dama tunda na ji haka hankalina ya ringa tashi ,na san daga su sai ni kake da shi a duniyar nan iyaye, ka ga dazu na aiki babar hadimata , har yama bata dawo ba , sai na saka a bi min sawu, aka sheda ai an ga an dauketa, wayo na shiga uku yanzu nice ake hari kennan?,dan Allah ka baza min masu tsaro ta ko'ina dan kar a dauke maka ni"

Da kyar ya iya ba kansa hakuri ya danne abinda ke taso masa, sai yake ji har wani karni take yi walahi, ko yaya aka yi a da baya ji?

Cike da nuna damuwa ya ringa salalami yana kama bakinsa, ya mike yana kai kawo ya fuskanceta ya ce" Umma, ni ban samu matsala da kowa ba, hasalima ni na fi tsoron ko su bafa ne suka samu matsalar da wani? Ama ai karya ne a shigo a dauke ki, hana dai,an dai tarbi na waje , ba dai Uwata ba!"

Yannayinta a tashe ta ce" Yarona, cewa aka yi wani irin katon mutun ne ke dauke mutanen fa, kar dai aje yan garkuwa da mutane ne, ko yan yankan kai, tunda ai Revell namu ne ko?"
Chapter 93 · 0% Book details