← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 99

Sashe 86

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzu fuskarta ba alamun murmushin dazu , ta sake dubansa ido cikin ido , muryarta na crakng ta ce" Husband......., Kan nufin cutar dake damunmu, wace ta hanna mana kasancewa daya, wace muke zaune cikin kunci sanadiyarta......a jikina take? Like a jikina kadai ne kake haduwa da hakan?"

Dara daran idannuwansa ya sake saukewa a kanta, tarin rauni da duba irin na nagarta yake yi mata, hakan ya sakata jin zuciyarta ta yi bugawar da tana da hawan jini ta tabata da a yau sai ta tashi da shanyewar barin jiki

A hankali ta damki damtsen hannunsa sakamakon tareta da ya yi a lokacin da ta ji kamar za'a makata da kas sanadiyyar Juwa
Tun daga kafarsa ta ringa dago dubanta a hankali har ta kawo kan fafadan kirjinsa, zuwa zaratan hannayensa ta sauke a kan ni'imtaciyar fuskarsa mai sakata karra jin du duniya babu macen da ta kaita dacen santalelen gaye a rayuwa
Muryarta cen ciki ta ce" Yaya aka yi ka gane ?"

Bai ce mata komai ba, sai dauketa da ya yi cimak ya nufi bakin bed da ita ya ajiyeta sannan ya tsaya yana harde hannayensa yana kallonta ya ce" Ba wannan ne maganar da ya dace ki tambayeni ba, abinda nake son sani ta yaya hakan ya same ki dan mu nemi magani, HUZNAH mu ba kannanun yara bane da zamu tsaya kan wannan yar maganar mu dagawa junna hankali, inaga a yanzu kin yi girman da ilimin da zaki kaucewa hakan......, Ki dan yi abinda ya fi armashi shine yin nazarin tambayoyina dan na samo mana magani!"

Ta yaya zata iya hanna kanta fashewa da kuka, a dole ta yi kuka, a dole ne ta yi kuka idanma ana yin na jinni a yau ita kam zata yi
Cikin matsanancin kukan da ya sarketa ta zuba masa rinnanun idannuwanta, yanzu mijinta? Abin kaunarta, abin tattalinta, mafarkinta ne wata ta malaka ba ita ba? Har yake nuna karamin abu ne? Ilimin me? Girma? A gingunemiyar uwa yake kallonta kennan? Shi yasa yake iya tsayawa yace da ita ta yi girman da ba zata iya yin kishinsa ba ko me?
Muryarta na fita a hargitse cike da dacin kalmar dake fita a bakinta ta ce" Yaya zaka yi magana da ni a kan abinda ya shafeka ka auna ni a dandaja? Ilimi? Girma? Na yi maka tsufan da kake tunanin zan iya kawar da maganar nan a kiftawa da bismillah?, Innalilahi wa inna ilaihi rajune, a jikina? A ina na hadu da wannan masifar? A ina na hadu da wannan balakin?, Yaushe hakan ta sameni? Na tabata tun kafin ka fara yi min duban mace ce ni da neman samun nutsuwa a jikina na hadu da shi domin a darenmu na farkoma a asibiti ka waye shi dan tarin cutar da ta dunkule maka a mara ka kasa fitarwa, ashe tun lokacin nice rashin lafiyar nake tunanin ina zaune da kai dan soyaya ba zan iya barinka ba koda kuwa baka iya anfanar min abinda kowace mace ke anfanuwa da shi? Wayo Allahna! Na shiga uku, ita ka samu ka shigeta ama ni aa? Ita da ta zo jiya jiya ce ta samu wannan mukami ni kuma aa? A dole ta ringa yi min gani gani, a dole tace min kar na saki na zo idan kun a soyayarku, a dole ka yarda da dukkan furucinta dan ka fi sonta, to ta yayama za'a hada soyayata da tata bayan ita tana iya baka abinda ni ba zan iya baka ba, ta yiwuma itace ta gamani da cutar nan ba kow..........

"h
HUZNAH!" ASADEEK ya fada a kausashe, muryarsa da dan karfi, idannuwansa gaba daya a ware a saman fuskarta cike da mamaki yana kallonta

HUZNAH dake kuka harda majina da hawaye hannayenta bibiyu a saman kanta ta tuje gashin kanta ta bale abin alkyabarta tana jan kasa daga jikinta ta dauko dubanta a raunane ainun ta sauke a saman kansa

A hankali ya miko hannayensa bayan ya sauke raunaniyar ajiyar zuciya yana kallonta, muryarsa a sanyaye ainun ya ce" Haba HUZNAH, maimakun mu yi maganar da zata fishemu,, mu samu mafitar da zata gyara mu, sai ki dauke maganar ki zubata gaba daya kan abu guda daya tak?, Haba HUZNAH................"
Ya dakatar a hankali yana sake kallonta sannan ya ja numfashi kadan ya ce" HUZNAH rayuwar shekara goma fa ba ta kwana goma bace, kuma a yau idan a kaina abin yake zan fi so na sani dan na magance ko dan na nuna bajintata a gabanki ko?, HUZNAH yaya zaki kawo maganar soyaya ta wannan fannin kamar ita kadai ce rayuwar auren? Da ace shi kadai ke iya rike aure da mun jima da raba hannun junna HUZNAH, idan hankali ya tashi ai hankali yake nutsar da shi, kin san tun yaushe nake son na tuntube ki a kan hakan? Kar ki sako magangannun NADIRAH a matsayin wani abin, yarinya ce, kar ki ga laifinta kin ji?, Dan Allah ki sasauta min hankalina a tashe yake fa, kin ga abubuwa sun min yaw yanzu sosai HUZNAH"

Kwarai, idan hankalinka a tashe, komai ganninsa kake yi ba wai, dukkan furucin ASADEEK sai suka ringa zuwar mata a karkace, gaba daya duniyar ta fitar mata a rai a lokacin da zuciyarta ta gama sheda mata hakane mana, dole ne yace damuwa ta masa yawa, a yanzu ai basshi da wata damuwar da ta wuce ta gidan hutunsa, dole yace tata damuwar ta biyo baya tunda yana cikin damuwar an sace iyayen matarsa, yana magana da cewa ko NADIRA ko wace? Wacece Nadirar kuma?, Kwata kwata a yanzu idannuwanta banda bakin kowa ciki harda shi babu abinda take gani

Hannun nasa ta kasa kamawa, da kyar ta iya mikar da kanta, a tsayin shekaru goma da suka yi basu taba samun sabani irin na yau ba, basuma taba samun magana mai ciwo irin ta yau ba, damuwarsu kanta basa zurfafa tunani a kanta dan basu da maganinta kuma basu dora tarayarsu a kanta ba, a yanzu dole ta ji ta rikice, dole ta ji tana neman shiga uku

Tana kallonsa Muryarta na rawa ta ce" Koda baka so, dole na fada, a bayane yake a zuwanta gidan nan na hadu da dukkan damuwar duniya, ni da ita sai dai Allah ya saka min!, Maganar sonta kuwa, ka san ka fi sonta da ni, a bayane yake, takan tsaya ido cikin ido ta yi maka rashin kunya, sai dai ka ringa murmushi , karshe yau ka kirayi lamarin da yarinta, a ina yarintar? Yaan magana sun ce SO hanna gannin laifi ne......., Dan Allah ka bani dama na je Baban gida dan a nema min maganin abinda ban san da shi ba sai da matar so ta zo!"

Idannuwansa ya rintse, soai yake yi mata uzuri domin abu ne da dole ya girgiza zuciiyarta, ama kuma ya yi mamakin saurin gazawarta da saurin yanke hukuncinta, to ita tama rasa a me zata tsaya ne ai, da bakinta tace a washe garin tarewarsuma ya tashi da ciwon, sannan tace ba wanda ya dora mata sai NADIRAH, shi a ganninsa idan aka ce shine a jikinsa zai zauna ne ya yi ta bincikar kansa har ya gano mafita, ama ita ta ki a yi haka, karshema ta bige da abubuwa kamar wata yarinya karama?

Juyawa ya yi ya nufi wajen kayansa ya bude ya zubawa kayan kallo gaba daya ya rasa kayan yake kallo ko kukan da take shekawa ke hanna masa motsin kirki?

Kukanta take yi bilhaki, ta ci gaba da magangannunta, cewa take yi ba zai ce komai ba? Tana jiran amanarsa ne na ta tafi gida, watau gidan iyayenta a nema mata magani, maganin da ta kasa bashi amsar da yake tambaya dan ya sama masu mafita, maganin da a yanzu ya sani yake kuma neman makarin abin, gaba daya ta juyar da maganar ta kasa sauraronsa, cen kasan zuciyarsa sai ya ringa jin muguwar kewa, da son zantawa da wani na jinninsa, sosai kewa irin ta iyaye ta ringa mintsininsa

Yana sauraronta har ta gama ta fice da kukanta cewar ai shikenan tunda yanzu ya samu mace ita kam da take hoto ai sai a kara mayar da ita gefe dan kar ta tsare hanya

Idannuwansa dake lumshe ya bude ya bi kofar da ta fice da kallo, kkasa kasa ya samu kansa da furta" Uhum" a cikin zuciyarsa kuwa yana girmama girma da karfi irin na mace, wanda ba zata daukeka ta makaka da hannayenta a kasa ba, ama Allah ya bata damar da zata iya yi maka sal komai girmanka da jama'a suke gani ta sileka tsaf ba ko kunya da tsoron Allah,

Lalausar shada ya zarro mai ruwan hanta, dinki ne mai gari da yar ciki, kusan du dinkunnansa haka suke dan ba kasafai zai saka dinki simple ba sai irin in zai yi fitar sirri

Bai saka garin ba, rigar da wandon kadai ya saka ya dauko hular kayan da Mancheste ya balla , Hular kuwa ya riketa a hannunsa ya karasa wajen turarukansa ya yiwa jikinsa barin turaren sannan ya koma wajen takalmansa ya sakka , ya karasa wajen comand na AC ya dauka ya kashe su biyun dake dakin ya kuma kashe light din

Bai baro dakin ba sai da ya cire soket din da aka jona na turaran wuta sannan ya janyo kofar ya rufe da Ky dinsa ya fice da shi, sabon abinda ya tsira kennan, a yanzu baya barin Ky dinsa ko dan rashin yardar da aka haifar masa a zuciyarsa

Tafe yake a hankali har ya karaso kofar dakin ta baya ya dakata yana kallo,
Wayarsa ya ciro ya shiga kiran number SHEIK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

6️⃣3️⃣

Wayarsa ya ciro ya shiga kiran Number SHEIK

Bata jima tana ringing ba ya daga
A nutse ya sanar masa cewa yau za'a dauke yarinyar karfe biyu na rana, domin a lokacin take daukan doguwar hanyar dake kaita bangaren da mahaifiyarta take dan amso kule kulensu na munafurci
Chapter 86 · 0% Book details