Sashe 6
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauro UMMA ta ce" Aa ka barta dan albarkana, ka san yannayin jikinta, ai takan min hakan sai a hankali zata daina in sha Allah, ka tashi ka tafi uzurin gabanka ka ji? Allah ya tsare , zan kula da komai nata kar ka damu ka ji? Ka san yannayin jikin da ya zamto haka sai a hankali"
Idannuwansa ya dake lumshewa cike da gamsuwa da maganarta
A hankali ya ringa bambare hannayen Auta dake kallonsa tamkar zata summa, wani irin kallo mai tafe da tashin hankali da firgici har ya gama zarewar shima yana kallonta da tarin tausayinta a zuciyarsa ya juya ya karasa ya yi gyaran murya aka bude ya fice a falon gaba daya
Jikinta ta hade, ta sada kanta tana wani irin makyarkyata da jikinta mai nuni da a birkice take
Murmushi Umma ta yi tana dora kafarta daya kan daya tana kadawa
Kai ta cira tana jan zaren alkyabar dake jikinta a kausashe ta ce" Dama zaki ba kanki lafiya, ki aminta da maganin samun lafiyarki? Ke kin san menene zaki yi ki samu lafiya, idan har kika ci gaba da naci, da nuna mini taurin kai, kina ji kina ganni yayanki da ya fi kowa sonki zai ci gaba da yi maki kallon mahaukaciya!, Ba kuma zan taba bari a fitar da ke daga masarautar nan bama bsle har wani ya kalleki da mutunci, haka zaki wulakance ki lalace har ki kashe kanki!, Ki sani mulkin wanda kike kira ubanki kayadade ne, takaitace ne!, Muna nan kamar yadda kika ganni da alkyaba bayan ban gada ba gaba da baya, zaki ji ana kirana gimbiya........ Ki ci gaba da yi min taurin kai, zaki kwashi kashinki a hannunki yarinya!"
Kanta ta dago tana kamo abin hijabinta tana dake rukunkumeshi a jikinta tana kallon Umma, abu daya take ji a zuciyarta a kan matar nan shine tsana, tsana mai tsananin gaske, sai dai abin tashin hankalin ko a cikin zuciyarta bata isa ta furta cewa Allah ya rabata da Umma ba, sai dai ta ringa Adu'ar A'lah ya rabata da wannan masifa dake damunta......., Idan ta budi baki a yau ta fadi wacece Umma ta tabbata yayanta ne zai fara soketa da ranta, bale jama'ar fada da kowa ke son UMMA saboda munafurcin da ta kware a shi ta iya siyan kowa? Bata tunanin akoy wanda zai yarda da maganar dake cikin bakinta, sai dai ta janyowa kanta balakin da ya fi karfinta, ita bama mutuwar take tsoro ba a yanzu, ta mutu ta bar matar nan a tsakanin yayanta da jama'ar garinsa!,
Idannuwanta ta sake rintsewa hawaye na zubo mata tana ji Umma ta mike ta fice
A hankali ta sake bude idannuwanta ta kankame jikinta ta budi bakinta dake bari ta ce" YA ALLAH, KAINE GATAN BAWANKA, KAI KA SAN ABINDA YAKE BOYE, KUMA KA SAN WANNAN MATA NA NEMAN FIN KARFINA YA ALLAH, SAI DAI NA SAN KANA NAN KUMA KANA AMSAR ADU'AR WANDA AKA CUTAWA, YA UBANGIJINA KA RABANI DA WANNAN MASIFAR DAKE DAMUNA, ALLAH KAR KA DAUKI RAINA A WANNAN HALI YA ALLAH....." Ta karashe tana sake fashewa da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.................
____________________________________
*Kauyen LABA, nesa da gari kadan daf da kogin garaje*
A hankali take kara yin dage a saman yatsutsanta masu dauke da dogwayen yatsu da faratunna masu dan tsayi da haske tass, haka kuma kafarta ta hagu daure da wata sarka fara kal ta azurfa
A zabure kawarta ta mike tana sake dafe kanta da hannayenta biyu, kirjinta na fokawa fat fat fat tamkar itace ta goce zata afka a kogon nan
Karkacewa ta yi tana bin yadda kawar tata ke yi ta rike igiya da sauri tana dake zarro ido
Bata daina sake dosar kwaduwar dake cen tanakula irin na kwadi ba, haka kuma numfashinta a sama yake sosai dan idan har tga afka a wannan kogon itama ta san sai ta ci ubanta a wajen nan
Ido kawar ta rintse tana sharce zufa ta ce" ki yowa Allah ki juyo hakanan, ki bar kwadin nan haka, le wai kwado halal ne kuwa?"
Dara daran idannuwanta ta sake zarrowa ta juyo tana dora yatsarta a saman lebenta ta sake furta" SHIIIIIIIII, idan kika yi na afka a ramin nan kin san Hindu sai ta karar da danginku kaf, domin ba zata iya rayuwa babu ni ba!"
Shirun kuwa ta yi, domin koda da wasa a tsakaninsu akoy kanshin gaskiya, dan kuwa a jiya har magariba ta sanyo kai ana masifa tsakanin Hindu da kanwar Babar mijinta, matar ta zo ta fadawa Hindu ta daina tura mata aljanar yarnan tata, domin mijinta idan ta shigo masu gida har ta fita bashida abin yi sai kallonta, yarinya ana neman koya mata karuwanci, Hindu ta dauki tafin hannunta mai dauke da yan yatsu biyar ta kifawa matar mari wanda nan da nan garin LABA ya dauka aka yi ta masifa da kyar wutar ta mutu, domin tace ba zata iya hakura a mari daya ba, ita kuwa tace sai dan yayarta ya saki matarsa, shi kuwa yace atafau bai ga abin saki ba a kan dan mari bayan da gaskiyar Hindunsa!
Ledar dake kugunta ta dauko ta bude tana murmushi ta dan duka da nufin kwashe kwadin dake tatare a waje guda kamar an hade su anai masu nasiha
Ta kawo hannu zata famka wani bakin maciji ya damki guda a bakinda
Ihu ta saka ta watsar da ledar, a haukace ta juyo tana takawa da wani irin sauri ba kamar na dazu ba nan da nan sai gata ta tsalako bakinta na fadin" Baki ne a cen, baki ne wawa zai hadiye kwado bai dan ajalinsa ya hadiya ba!"
Takalmansu kawar tata ta kwasa ta kwasa a guje , itama ta mara mata baya suka fala da gudu kai kace wasu yan kannanun yan mata ne
Basu zame ko'ina ba sai karkashin bishiyar da suke hutawa suka zube sunna ihu da kyakyacewa da daria
Kawar tata ta ce" Yau da jarabarmu ta haifar mana da Da da ido!, A yau sanadiyar neman soyawa Aminunki kwado da mun tafi lahira !"
Daria take yi har tans dafe shafafen cikinta , hakan ya bayanar da wushiryar dake tsakanin hakoranta na sama yar siririya da kuma dumple din dake gefe da gefen kumatunta tana numfarfashi tamkar zata summe itama ta ce" Yanzu yaya zamu yi kennan? Aminu fa a jiya a dandalin lami da idannuwana na ga yana siyan naman Habu!"
"Wai ke naman kwado halal ne?" Kawar tata ta fada tana dafe haba
Hannayenta ta watsa ta ce" an dai ce dukkan halitar dake kasan ruwa halal ne, bama a yankawa ai"
Kawarta ta kama haba ta ce" Dankari, toh shi kwadon a cen kasan ruwa yake ko yayane?"
NADIRAH ta yi tsai, sai kuma ta ce" Kin ga dan Allah kar ki hafen tunani kin ji?, Ai kawai nama nama ne, ni dai takaicina abin kauna ya siyo nama a titi, yo aikin me nake?"
Murmushi ta yi ta ce" Kin san menene? Na tabata idan kika dafa masa kwado fushi zai yi da ke, kwado fa"
Itama murmushin ta yi tana mikewa ta zauna da kyau sannan ta janyo fararen kafafuwanta da suka yi budu budu da datin farar kasa ta ce" Na tabata zai sauka da wuri, ya kuma san a kan SO NE"
Kai kawar tata ta girgiza tna dafe habarta ta ce" INDIRAH, lokuta da yawa idan na ga kunna soyewa ke da Aminu sai na ji tsoro ya kamani, ina tsoron furucin mahaifiyarsa da tace sai dai idan bayan ranta, wai me yasa suke aiki da halitarki suce idan kyau ya yi yawa masifa ne? Gaskiya ana cenfe cenfe a ruga!"
Itama murmushin ta kuma yi, murmushi mai matukar karbar fuskarta, ko an fada mata yana yi mata kyau ne ya sa take karra bashi mahinmanci du idan zata yi?, A hankali ta janye dan tsinken da ta nade nanadaden gashinta da shi ta sokashi a cikin kasa ta dubeta ta ce" To idan ta mutun ba sai a yi ba?, Ban san me yasa nakeda bakin jinnin wasu mutanen ba, kema da ba dan kin raina kaka ba da ba zamu yi kawance bafa, an ce mata ina iya dusashe tarmamuwarki in muna tare, ba za'a ringa ganninki ba sai ni kadai?, Ni dai abinda na dani a kan AMINU daya ne, iya rai muna tare, ko na kashe shi ko ya kasheni ba zan iya rabuwa da shi ba, domin tun ban iya so ba har ya koya min.......... Na tabata yana kofar godan Hindu tashi mu karasa na ga ABINCIN RUHINA kin ji? Mamansa kuwa ta sake daure kugu da kyau, idan muka buga mata muhamada a zo a kada kalangum daurin auren danta da ni!"
Ta karashe tana janyo takalmanta ta saka na hannun hagu din, da na damar ta dake wani katon kadangare da ya nufosu gadan gadan ta jefar da shi ta saka takalmin sannan ta janye abinda ta soka a cikin kasa ta sake hade gashin nata a tsakiyar kanta ta nanade ta soke sannan ta nufi wajen kawarta watau RAMA suka dauki hanyar gidan KANWAR MAMANTA watau HINDU shagali.
A tsaye suka tarar da ita, ta sha wani irin daurin zani wanda ya haura cen saman kaurinta , kanta ba dan kwali ta Barbaza gashin kan nata tana tsaye tana rike da kofar dake jikin hanyar shigowa tana leke
Idannuwanta na dauka a saman fuskar y'ar yayar tata ta daki murmushi ta mika hannu ta janyota tana fadin" Lalle da yar so yar cikin kirjina, yarinyar da zan wanke na mikawa sarki, dan walahi uban talaka ya yi kadan na bashi yata, na fada na kara, nu har an min iya shege ne a kan yarinyata? Idan da ubanda ya ga a wajen da aka ce dan ta cika kyau maya ce ita ko aljana ya kawo min wajen na karanta, iskancin banza iskancin wofi, yau sai na ci uwar maman Aminunki a garin nan!''