← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 99

Sashe 7

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ido ta zarro a haukace ta idasa shigowar tana kai hannunta ta rufe bakin Hindu tana sake zarro idannuwanta ta ce" Innalilahi Inna me dangin abin kauna suka maki kuma kike zagi so kike ta karra cewa ba zata bani shi ba?"

Ido suka zuba mata, daga innar tata har kawar tata, ba za'a bata shi ba? Innalilahi wa inna ilaihi rajune, yau sun ga salwatacen bakon iskanci a wajen NADIRAH!

"Ke indirah Hindunta , kar ki ce mun a kan namiji kina iya kuncen zani a kasuwa?, Dan ubanki yanzu uwarsa ta fita ta zo ja min kunne wai kar ki kuma shiga sabgar danta, itafa ba zata taba bari da ranta ki aurar mata da ba , salon ki saka ya manta wacece uwarsa a duniya? Wai sam bama zata iya bari ki shiga ahalinta ba , domin yayansama sonki yake, ke bari ki ji ni kuwa nace ai ubansama yana iya sonki dan kin keru, kuma nima na ja mata kashedin danta kar na kuma ganninsa a kofar gidana ya zo zance, ya kiyayeni ya kiyayi yata, dan walahi a kanki sai na nada mata duka, muma bama so!" Hindu ta fada tana zarro ido da sake gyara tsayuwarta

Silalewa Nadirah ta yi a kasa tana cire abin dake soke a kanta ta fadi" Shikenan, na shiga uku na lalace, ku ina ruwanku da soyayarmu ne wai? To guduwa zamu yi idan kuka shiga ciki, mamansa kuwa ai kyaleta na yi idan da rabo ba dai ta je kiyamar ba a yi? Haba Innar Indi ke da kanki? Gaskiya wucewa zamu yi a je a basu hakuri"

Kamar an gaurawa Hindu mari a kuncinta haka ta dafe kunci a zabure, sai kuma ta kai hannayenta saman kanta ta fashe da kuka tana fadin"

Asalamu alaikum.......fatan kunna kalau? Yaya ake ciki? Yaya kuke gannin ake ciki? Yaya kuka ga salon?........ Shin me yake boye mai zai bayana a rikicin tafiyar labarin UMUGHLUK ITIFAL?

WANENE UMUGHLUK ITIFAL ASADEEK BRAHAM?

ME YAKE FARUWA DA KANWARSA

YAYA LAIFIN DAKE CIKIN GARIN TANUT? YAYA ZAI WARWARE?

ME KE TAFE DA ZUCIYARKU DANGANE DA NADIRAH, WACE AKE KURA DA INDIRAH, YAR GIDAN FADIME DA INARTA HINDU? .............. BAN FARA DAN NA DAINA BA IN SHA ALLAH KUMA FREE NE.......LADAN BIYANKA KAWAI COMMENT NE 🥰🥰🥰🥰🥰🥰

*Yar uwa, shin kin sayi labarin kwatena mai taken CARBIN KWAI?, idan bali siya ba lalle zan iya kiranki mai wasa da dama, carbin kwai shine ke tafe da abubuwan da zaki iya fadowa daga saman gadonki dan dariya da farin ciki, akoy abin tausayin, uwa uba cakwakiya............CARBIN KWAI akoy ilimantarwa, tunatarwa, nishadantarwa, ke harta motsin gado😁, ki dai garzayo kawai hajiyata tuni mun fara posting a naira 300 kacal ki samu naki ki more*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

0️⃣5️⃣

*Wai kun siya kuwa? Ku fa zo ku samu naku, takensa shine CARBIN KWAI na KWATENA, kawata , maman jariri, wannan marubuciyar BADAKALA na AMMAR dan aljannah, da kuma BAIWATA mai lulube da baiwar alkhairi......., Ba zigi a ciki ba kuma kodawa irin ta mai siyarwa, idan ka siya sai ka ji tamkar ka karra ninka mata kudin dan farin ciki da jin dadi.....MALAMAR hazika ce mai baiwa a lulube a tare da ita....... MAZA GARZAYO KA SAMU NAKA A FARASHI MAI SAUKI 300 NAIRA*

Hindu ta fashe da kuka tana kallonta ta ce" La ila ha ilalahu muhamadu Rasulullah salalahu alaihi Wasallam, yanzu Indin Hindu ni zaki tisa mu koma na baiwa matar da na gama yiwa alkawarin yata sai saraki? Ke wannan yarinya ki raba kanki da lamarin maza, ke yanzu wace irin soyaya ce zata saka ki gudu da kato ki barmu da abin kunya a NIJAR? Kar ki manta wanene ubanki a gidan sarkin garin TANUT, kar kuma ki manta wacece mahaifiyarki a fadar matar mai Garin TANUT!, Ni din nan kin san wacece ni, kuma ki wulakantamu haka? Ko dai magani ya yiwa y'ar nan ne wannan shegen langayayen yaron?"

NADIRAH ta kwabe fuska, sosai ta nuna daf take da yi mata kuka ta ce" Ba zaki je ba dai ko? Imnata ba zaki je ba? Ai shikenan Innata ki yi zamanki, ki zauna idan Aminu ya tsaneni duniya zan bi Innata, ki zauna, kuma kin sani sarai a duniyata ba ni ba maganar ratse ta hanyar da sarki ya bima bale wai ni na kasance a innuwa daya da sarki, Innata ko sarkin yan iskan garin nan aka aura min in dai sunnansa sarki in sha Allahu ko gawata aka mika sai ta yi fatalwa ta dawo da kafafuwanta, me ake da rayuwar sarauta rayuwar matsi rayuwar rashin barkatawa kai abin kirki? Kana zaune tamkar duwawu komai sai an yi maka? Innata ki daina yi min mugun fata kin san fa uwata ce ke ko?" Sai kawai ta karashe tana mai fashewa da kuka harda kwonciya a nan wajen ta dora kanta gashinta du ya shige cikin kasa

Tsuru tsuru suka yi, daga innar tata har kawarta sunna kallonta

Innarta ta sake dantse lebe, ita kam jarabawarta a rayuwa kaunar yarta ne, a duniya bata iya cewa NADIRAH aa, walahi tana iya yin ba dadi da mijinta ta kwonta kalau abinta , ama idan hankalin NADIRAH a tashe ko ruwa bata iya sha, tunda yayarta ta haifi yar take jin tamkar ita ta nakudo abinta ta haifo, shi yasa harta sunnanta yan gari suka hade suke kiranta INDIRA wasu suce HINDIRAH, domin a bayane soyayarsu take ba a boye ba, soyaya irin ta uwa da d'a, a kan Nadirah fa ita sai ta zagi mai rabo walahi ko uban wanene!

A hankali ta dubi Kawar NADIRAH ta ce" Ki kamata mana kema kina kallonta?"

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" Inna kin san halinta sarai fa, bafa zata saurareni ba"

Inna ta sake sauke ajiyar zuciya ta kunce mayafinta ta yafa a saman kanta ta duka tana rike hannun NADIRAH ta ce" Shikenan, tunda so kike a raina maki uwa salon gobe idan an zo taron auren naki ace uwar taki wacece ita yo a wajenki tashi mu je, ama kar ki manta bafanki bai san zan fita ba, kuma kin san ba kyau matar aure ta fita mijinta bai sani ba ko?, Sannan kuma idan muka je na bada hakuri an kama maki gori kennan, Haba ta Aminu, haba aminar Aminu?, Idan kika yi hakuri da kaina zan raka ki dandali na ba Aminu hakuri ku ci gaba da hirar tsakiyar ranarku kin ji yar arziki irin albarka?, In kuwa kin fi so mu je din mu je kawai sai na dukama na bata hakurin ai ba komai rayuwa ce dan an min gori an zagi innarki ai ba komai"

Kukan nata ne yaa rage tana kallon Innarta

Innarta ta ce" Yi shiru tashi ki daina kukan, in dai dan tisa keyar uwa ne a kaita ta bada hakuri ai ba yau ba kika fara, yau kika fara kaini na bada hakuri idan mun yi fada da mutane ne? Tashi mu je Allah na tuba mai bada hakuri ai shine dan aljannah!"

Manyan idannuwanta ta kikifta, sai kuma ta sada kanta bayan ta dago shi tana kakabe kasar dake kanta, haka kuma ta yi shiru da kukan da take yi

A sanyaye sosai ta ce" Innata, baki yi tatsa ba?"

Hindu ta yi murmushi ta ce" Haba dai ai ba zan zauna har ki dawo ban yi tatsa ba, bayan na san shine abincinki, gayacen cikin kwaryar cen a lulube da saki dan ya kara sanyi"

Murmushi ta yi itama ta mike ta karasa wajen kwaryar ta zauna ta bude tana sake sakin murmushi, domin an shake mata kwaryar sosai
Gaskiya ba zata kai innarta ba innar Aminu hakuri ba, matar bata son zaman lafiya, me yasa ba zata yi hakuri bane wai? Kulun sai ta zazageta , da a iya ita ta tsaya lafiyar Allah ba zata fadawa Innarta ba, ama ta taso ta tardo inna? Bayan in dai a kanta ne inna batada hakuri? Sam bata kyauta ba walahi, ama ba komai zasu hadu da Aminun ne, bara ta sha ta koshi ta yi shirin dandali, ta tabata bawan Allah shi yau bama zai iya cin komai ba, ai idan suka yi fada tamkar zai muti yake dawowa, aminu kennan aminin arziki abin kaunarta!................

___________________________________

Tafiyar jirgi suka yi, zuwansu da dawowarsu, hakan ya sa dudu basu wuce awani biyar ba a tafiyar tasu da zamansu da sarkin garin da kuma dawowarsu garin AGADAZ, domin tafia ce ta takaitacen lokaci a jirgi

Kana gannin fuskar Mai garin Agadaz zaka fahimci yana cikin wani hali, domin fuskarsa ba alamun ya taba yin daria, duda a cikin rawani take, ama haka zaka iya fahimtar hankalinsa ba a tashe ba

Sallar la'asar suka gama a baban masalacin fadar, ya zamto kusan kowa ya watse sai shi sai Sheik

Kansa a sade yake yana jan carbin dake hannunsa a hankali ya sake duban Sheik dake magana a sanyaye

Ajiyar zuciya ya sauke a nutse ya ja rawanin dake saman fuskarsa ya dake mayar da dubansa saman makarar dake ajiye a cikin masalacin sannan ya sake duban SHEIK a nutse ya ce" Wanene ni, da za'a ringa maimaita min cewa Mulkina takaitace ne? Da ni din wanene da zan shagala cewa mulkina dawamame ne? In ba shirme irin na Bafana ba da ya fitar da maganar nan wace tale sirrina ce har ta fito daga cikin gidansa ta yadu a wajen da ban shirya jinta ba dama me zai sakani ni bawa da Allah ya halita dauka cewa zan zartar da mulki a doran kasarsa dawamame? Wai su basa tuna mutuwa ne? Ko sunna manta wanene mai Mulki? Mu jagoranci ne muka samu na talakawa, mai mulki shine ALLAH, Yah SHEIK, dan kawai ina kamanta adalci sai na zama abin farauta?"
Chapter 7 · 0% Book details