← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 99

Sashe 34

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe tara aka yi za'a daura aure, sai dai abin bai kasantu ba sai kusan karfe goma na safe, a cikin masalacin da aka yiwa Sheik iso cewar a ciki za'a daira, bayan ga dumbin mutanne a waje da suka zo dan a daura da su

Dayan abin da ya dan bashi mamaki gannin an ware mutanen da zasu kasance sheda basu fi a irga ba an ce sauran su zauna a waje dan AC baya yi, idan waje ya cinkushe hakan zai zamto takura ga mai martaba

Shi dai ya gabatar da sadakinsu, sadaki mai daraja, sannan ya amshi auren da aka basu

Sun daura aure cikin daraja da mutunci,sannan Sheik ya ja Adu'ar da har sai da Mai martaba ya fara tsitsine masa a ransa, gani yake wannan din ai iskanci ne, ina dalili wannan uban shishigi da janyi ayoyi haka?

Daga nan SHEIK ya bude Alku'ani ya nemi da mutanen da suka zo tare su shigo, suka shiga gabatar da saukar alku'ani mai girma wanda hakan ya dake kular da sarki ya koma gefe yana sauraro ama hankalinsa ba a wajen ba, ya fi daukar hakan da wata fuska daban, su kuwa cikin nutsuwa suka yi, kuma kasancewar sunnada yawa nan da nan suka gama aka sake yin watga fatihar sannan aka shiga bayar da sadaka wa mabukata, wace wannanma kokarin Sheik din ne

Bayan abubuwa sun lafa SHEIK na murmushi ya dake mikawa Mai martaba hannu a tausashe ya ce" Ashe sunnanta ba bahija bane?, Domin sai na ji kamar UMUGHLUK ITIFAL ya furta cewa sunnan yarinyar BAHIJA?"

Wani irin murdawa da cikin Sarki ya yi sai da ya dan karkace zama,haka kuma idannuwansa sai da suka zarro lokaci daya ya shiga tunanin a ina UMUGHLUK ya san sunnan y'arsa?

Lokaci daya kwakwaluwarsa ta tuno masa ai maganar ta farko su da kansu suka fada masa yarsu BAHIJA

Wata boyayiyar ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Ai Bahijar kiranye ne, asalin sunnan NADIRAH ne, Bahijar mahaifiyar ke so sai ta saka mata har kowa ke kiranta da hakan"

Murmushi Sheikh ya yi yana daj sake kallon abin zufar da yake kokarin jike turkudin Sarki, sai kuma Sarkin ya mike yana fadin" Bara na je da kaina na ga shirin fitowarsu, sai na fito SHEIK"

Fatan fitowa lafiya ya yi masa, sannan ya shiga buga numbar ASADEEK yana ayyana ' bawan Allah ko ka kira ka ji an daura lafiya? Gashi har karfe daya zata yi'

A birkice ya shige bangarensa yana sake buga numbar UMMA, domin kwata kwata hankalinsa ya kasa kwonciya, so yake yi ya sake jin gaskiyar lamari cewa ASADEEK bai san y'arsa ba!

Tana baza kanshi da sabuwar suturar da ta saka dan ta yagawa matan da suke takamar sunne darauta ta karaso ta rufe kofar tana sakin murmushin gannin ai kamar har hakarsu ta cinma ruwa tana fadin"

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

2️⃣3️⃣

Ba editing 😁

Tana murmushi ta ce" Barka da idasa aiki mafi hatsari Sarki, burinmu, farin cikinmu ya kusa tabata, baka ji yadda raina yake fari ba idan na tuna mun fara kaskantar da darajarsa kennan, duda mun dauko yarinya mai kyau zamu bashi, ama sai dai ya kalleta, domin na tashi daga shawarar cewa ba za'a bata abinda aka ba matarsa ta farko ba, dan kar aje ya yi ido hudu da ita ya nemi shafarta har ya kwatanta shigarta abu ya tabata mu bani!"

"Asadeek ya san BAHIJA. Waje ne?" Ya fada yana tare numfashinta

Ido ta zuba masa kafin ta ce" Wani abu aka yi ne?"

A dan kufule ya ce" Ki bani amsa, ba ki maido min da tambaya da wata tambayar ba!"

Kai ta girgiza tana fadin" Meye hadinsa da ita? A ina zai ganta? Mutumen da babu abinda ya shafe shi da harkar yan matan zamani bama, haka kuma yarka ta tsane shi ta yadda bata zuwa garin nan ta sauka a Fada, babu ta yadda za'ayi ya santa, menene dalilin tambayar nan?"

Sarki ya ce" Wannan malamin nasa, wanda ke wakiltar aurensa ne yace min wai Ashe ba sunnanta bahija ba, wai Asadeek ne yace masa Bahija sunnan yarinyar?"

Dan tsai ta yi, sai kuma ta yi murmushi tana fadin" Kai kam ka cika sarau, da bakinmu muka sanar masa sunnan nan, nima da bakina na sanar masa ya kai sau biyu, ina fata baka rikice ka tona kanka ba?"

"Ni dai na ce masa Bahija kiranye ne da Mahaifiyarta ke yi mata, ama duda haka maganin nan da na baki bani shi nanna ajiyeshi a wajena, sai maganar aurensa ta lafa sosai za'a fitar da shi a kai mata, kar a bata shi yau" ya fada yana miko mata hannu

Itama murmushi ta yi, domin a gaskiya idan aka ce daga zuwan yarinyar har ta aikata aikin nan an kamata itama ba zata ji dadi ba, haka kawai take jin bata taba gannin macen da ta dauki hankalinta irin yarinyar nan ba, ciki harda wancen uwar taurin kan da ta zabi hauka a kan hankali,
Maganin ta lalubo a cikin rigarta ta miko masa, tasakashi a ledoji ta masa wani irin dauri,shi kuma ya juya ya kai shi ya boye sannan ya dawo ya tsaya still idannuwansa ba daidai ba ya ce" Idan kuka bata magani me kennan?, Ai zan so ya gwada tashin jarabarsa a kanta,ya ki zuwa inda take da tsoron kar ya je abu ya kwonta, da wannan damar nake so ki saka masa ido, ta yadda zaki turamasa baiwa tsirara, ko waye shi zamu gani ai, idan ya aikata abinda a kansa yake jefe mutun har lahira sai mu gani, jefe shi za'a yi ko gubar macijin nan zai ci?, Ki barni in sha dadin kallonsa a mazinaci mana kema"

Ido ta kankance tana kallonsa kafin ta ce" Bam taba gannin mugu irinka ba, ama wannan tunani ya min , lalle lalle idan haka ya tabata ni nan nice zan tunasar da shi shine fa mai yankewa wani hukunci, yaya kennan?, Uhum ka hango shi a cikin rami kansa a waje, idan na tashi daukan dutsin da zan jefa masa sai na dauko rungumeme na zafta masa ta yadda zai makance kafin ya mutu!"

Wani irin murmushi ya yi yana hangen komai a idannuwansa, a matsayinsa na wanda ya haura shekaru sittin a duniya, yana hango wasu sittin din ne a gabansa? Fa karfinsa? Da hankalinsa? Wai idanma mutuwa bata ratso a lamarin ba, gigita irin na tsufa fa? Wanda ke saka bawa ya dawo tamkar jariri fa? Tsufan da ya zo maka da tsoron Allah da zikirima yaya kake dawowa idan shekarun sunna dauko da yawa? Bale tsufa irin nasa? Allah, kar ka hadamu da makantar zuciya Ya Allah, Allah idan har munada rabon yin makanta cikin biyu gwara mu rasa ganninmu da zuciyarmu ta rufe, domin idan muka rasa ganni irin na hasken musulunci idannuwan namu zasu hasko mana gigitacen ganni a duniya da kiyama!

Agogo ya duba sannan ya kalleta ya ce" Ki je ku fara shiryawa, ki kula da WA'INDA zasu shiga motocinku, da zararan fito daga sallah zaku dauki hanya saboda ku samu shiga da duhu duhu dan kiyaye dokar shiga da Matar sarki da hasken gari"

Kai ta gyada da murmushi ta fito ta sake ratsawa ta nufo bangaren GIMBIYA

Tana zuwa ko Gimbiyar bata kula ba ta nufi dakin BAHIJA wanda aka sauki su NADIRAH da HINDU

Tana kama kofar zata shiga ta ringa jiyo kuskuskus, irin magana ake yi kasa kasa sosai

A hankali ta dan labe sannan ta karra kunnenta, dan gaba daya ita bata wani yarda da marakiyar yarinyar nan ba,

"Kina jina Indin Innarta, ki sani su din sun isa da ke, sarakunan ki ne, da mu baki daya, su muka sani, kuma dole mu masu biyaya kin ji? Ki tabatar kin masu abinda suke so fa?, Idan yau akace ki aikata ki aikata shi, mu mun yarda da su, kuma ko me suka sakamu zamu aikata masu ne dan kauna"

NADIRAH da ta ci kukan jin ana fadar cewa an daura aure an daura aure ta sada kanta , domin bakinta ba zai iya furta komai ba, haka kuma rarashin da Innarta ke yi mata ta jiyar da maganar gannin innuwar mutun ba zata iya amsa ba a yanzu, batada karfin amsa maganar nan gaba daya, shin yaya zata yi da ranta ne? Yau an wayi gari an daura mata aure da wanda batama sanshi ba, shima bai santa ba, bata taba ganninsa ba, Aminunta yana LABA baima sani ba, daga ce masa zata rako innarta biki su dawo, an dora mata alkyaba, an nadeta, an dora mata igiyar da ta fi kowace daraja da nauyi a wuyana, wai a yanzu ita matar wani ce, waninma sarki, ta yiwu tsoho ne takwaf bawan Allah tunda ta ji su ummanta na kiransa baban kowa?, Ta yiwu shiruftar tsufa ta kama shi, ta yiwu kuma wani kasurgumin azalumin boye ne, mutumen da ya saka a kasshe baya ce masa komai? Shikenan an daura aurenta innarta bata saka dinkin da tace zata yi ba, sannan ba'a siya mata gadon karfe mai rumfa ba, shikenan za'a kaita wajen da bata san me zata tarda a cen ba, shikenan za'a yi bikinta babu mahaifanta a gefenta,ko innar birni tana tunata? Ko ta manta da ita? Abanta ko ya dangana ? Ko yana cike da tunaninta?, Haba ta yayama zata iya bada amsar wani wasan kwaikwayo na innarta? Bakinta ba zai iya ba sam!

"Ki daina hawayen mana na ce kin ji yar gidan Indinta?" hHindu ta sake fada tana sake satar kallon kofar

Shigowa Umma ta yi ta mayar da kofar ta rufe ruf ta karaso ciki sosai tana kallonsu daya bayan daya

A nutse ta ce" Kukan me take yi ita kuma?"
Chapter 34 · 0% Book details