← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 99

Sashe 72

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fada ne na mamaki, fada ne da duka rasa dalilinsa, hakan ya sa suka yi shiru gaba dayansu babu wanda ya furta koda A ne har suka karasa bakin jejin wani a rakumi ya yi masu ja gaba suka karasa boyayen gidansa na garin TANUT din wanda ke zagaye da dakarun buzaye a saman rakumansu sunna zagaye kowane shirye yake a mutu idan ta kama, dan babu wanda baya dauke da takobi mai kaifin balaki da kuma bindiga ta zamani

Fita ya yi ya karasa cikin falon ya zauna ya zubawa waje daya ido kansa na sarawa, lokacin sallah da saura shi yasa ya dakata a nan

Ya dauki lokaci a nan a zaune SHEIK ya shigo da salama a bakinsa cikin nutsuwa ya ja ya tsaya har sai da ya budi bakinsa a hankali ya amsa a saman lebensa sannan ya sauke ajiyar zuciya ya karaso ya zauna face da shi

A sanyaye ya ce " KISHI?"

ASADEEK ya yi tamkar bai ji abinda ya fada ba, har sai da SHEIK ya maimaita kalmar yana kallonsa

Fuskarsa da yannayin rikicinta ya dube shi yana kausasa kallonsa ya ce" Me kake nufi da kalmar KISHI?"

Sheikh ya sauke dubansa a cikin na ASADEEK, sai kuma ya dan girgiza kansa a hankali ya ce" Bana nufin komai,, gani na yi tunda muka taso yau jinninka yake kan Akaifa"

ASADEEK ya juyar da kansa bai ce komai ba

Sheikh ya sake sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Shi din wannan mutumen shine wanda aka barmu a cikin masalacin mu hudu , a gabansa muka tatauna da sarkin garin nan, kuma yana cikin shedun da suka sheda daurin aurenka da ita, haka kuma ba zan manta fitarsa a lokacin ba, ana gama daurin aure ya fice da sauri , da ba dan ba kar nace hawayen me zai fito daga idannuwansa da nace har kamar hawaye na bin kumatunsa, ka ga dai yannayinsa ka san bashi da karfi, kusan shine marar karfi a wajen domin ko a ranar ba wata sutura mai tsada bace a jikinsa, sai dai yana tare da wata boyayiyar nutsuwa da sadadan kallo, a yanzu haka ganeka da ya yi kai ka san akoy wajen da ya sanka, da zaka amince idan ka huta ya shigo mu zauna da shi mu ji ta bakinsa, ta yiwu ya dan wani abu a cikin wannan kulli"

Bayan Sheikh ya dire maganarsa ASADEEK ya dauki minti uku a kalla yana sauke ajiyar zuciya yana ta korar abinda ke cizo shi
A hankali ya gyara zamansa ya ce" Ban gaji ba, a shigo da shi"

Sheikh ya sake kure shi da kallo na yan sekwani, gaba daya da zai ji tashi da ya hakura har ya samu nutsuwar zuciya , sai dai tunda ya kiya babu yadda zai yi , a dole ya mike ya fice ba wani kwarin jiki ya fita dan sanyo bakon

Su uku suka shigo, SHEIK a gaba, mahaifin NADIRAH a baya, sai sarkin yanka a baya hannunsa saman takobinsa dake jikin tsatsonta, fuskarsa kuwa sam ba alamun sasauci

Sheikh kadai ya zauna saman kujera, Sarkin yanka ya ja ya tsaya ta hanyar wara kafafuwansa rawaninsa na sake rike zagayayiyar fuskarsa, Mahaifin NADIRAH kuwa a kasa ya duka a nesa sosai kansa a kasa ya yi shiru, domin ba'a bashi damar da kawo da gaisuwa bama bale ya kawo din

Dan shiru wajen ya dauka har sai da SHEIK ya gama karewa ASADEEK kallo zuciyarsa cike da mamakin rashin hakuri a abinda ya shafeta wanda kiri kiri yake turewa ama bai san a bayane yake a fili bs SHEIK ya dubi bawan Allahn nan da haka kawai yake jin yana iya sauraronsa ya ce" Bismillah, ka yi hakuri ka sanar mana wanene kai? a ina ka san UMUGHLUK ITIBEL?, Yaya aka yi ka gane shi?"

Mahaifin NADIRAH ya dago fuskarsa a sanyaye ya kalli SHEIK, sai kuma ya sake mayar da fuskar tasa muryarsa a sanyaye ainun ya ce" Allah ya taimakeka, a gafarceni, tunda na ga ABAN DATAWA a wajen nan hankalina ya gama rugunzuma ya tashi, gaba daya tsoro ya darsu a zuciyata, na tabata tunda na ganshi a wajen nan ya san yarinyar dake gidan ba ainahin ita bace aka .............mmmmm"

"Yaya za'a baka umarnin wani abin daban, ka ringa yi mana bayani a kan wani daban!, Ka kama kanka!" Sarkin yanka ya fada a kausashe

Hankalin Mahaifin NADIRAH sake tashi ya yi, ya rasa me zai ce yanzu kuma, ko dai rikicewarsa ce ke neman saka shi aikata abinda ba'a nufi cen da shi ba? Kar dai ba abinda yake tunani bane ya kawo su shi kuma ya bude baki yake sanar masu abinda ba'a tambayeshi ba?

"Ka barshi ya yi bayanin abinda yake son fada ITBAL!" Muryar ASADEEK da ya dago daga jingine jin kalaman dake bakin wannan bako

Dubansa ya maida kan Aba , ya zuba masa ido Ainun, daga irin tsugunnon da Aba ya yi a kasa kaffafuwansa a tankwashe a jikinsa da irin hade hannayensa da ya yi ya saka shi kallon saman cafet din nan a nutse ya ce" Bismillah ka dawo nan ka zauna"

Aba ya sake sada kansa, cike da girmamawa ya ce" Allah ya huci zuciyarka, nanma daraja ne a wajena idan har a gabanka nake, a yafe min, a gaffarceni, na aikata kuskuren budar bakina a yi mib afuwa , zan sanar a inda na sanka, sanadiyar iyalina a lokacin da aka so yankewa mahaifiyarta hukuncin kisa, nine nan ka bayar masarautar Tanus cewar na zamto sarkin dawakai a bisa adalcinka da kuma tausayinka, na tabata ka manta kamanina, sunana SALIHU daga kauyen LABBA"

ASADEEK ya Sake fuskantarsa, tabas an yi haka da jimawa, asalima a lokacin ba shine zai yi shara'ar ba, mahaifinsa dai ya saka shi ya bashi umarnin zuwa da yanke hukunci yadda ya dace

A nutse ya ce" Bayan wannan , me ka sani dangane da maganar BAHIJA"

Kansa ya dago, irin duban da ya yi masu babu wanda bai ga tashin hankalin da zuciyyarsa take ciki ba, ya yi hakan ya kai sau uku, ama a cikinsu babu wanda ya fahimci da ace zasu taimaka masa su ce da shi ba sai ya fadi komai ba da sun rufa masa asiri, baban tashin hankalinsa iyalinsa, yaya za'a yi da su? Wani irin hukunci zai hau kansu? Subahanalah yaya za'a yiwa NADIRAH?, Innarta fa?

A dole hawaye ya shiga bin gefen kumatunsa
Sosai ya karra sada kansa hankalinsa na tashi

A sanyaye ya ce" RANAR talata ne, FATIME ta dawo min hankalinta tashe kan maganar, UMUGHLUK ITIBEL babu laifin iyalina a ciki, hasalima baki daya laifin nawa ne, nine na ce dole zamu bi, nine na nuna dole zamu aikata......."
Ya ajiiye maganar hawayensa na sake balewa , sai kuma ya dago yana kallonsu ya ce" Na san kana shara'a ne idan kowa na gabanka a zaune ta yadda kowa zai kwaci kansa, haka kuma na san cewa kama fada a tsaye a kuma zaune cewa baka shara'a ka ware na gida, ko ka ware mai arziki, takobinka zata sari du wanni wanda ya kama ta sara, domin ka san zaka mutu , zaka tsay a gabam Ubangiji a matsayin bawa , zaka yi bayanin dukkan abinda ka aikata a duniya koda tsakaninka da tumbinka ne........."

"KAI DIN MENENE DIN NADIRAH?" muryar Asadeek a sanyaye ya katse Hanzarin mahaifin NADIRAH

Aba Salihu ya dago jajayan idannuwansa masu zubar da hawaye a sanyaye ya ce" Yata ce, ita dayaa tak na malaka a gidan duniya, INDI yarinyata ce"
Kai ya sada yana tukar kukan da ta yannayin girgizar jikinsa zaka gane kuka ne yake shekawa abinsa

ASADEEK kuwa baya ya koma ya jinginar da bayansa ya lumshe idannuwansa yana tasbihi ga ubangijinsa

SHEIK ya kalli sarkin yanka ya masa alamun ya fita

Fita ya yi, SHEIK kuwa ya fuskanci Aban NADIRAH a tausashe ya bashi umarnin dawowa ya zauna a waje mai kyau

Da kyar da wala haula ya yarda ya hau kafet din, ama firr ya ki hawa kujera wai ASADEEK na waje ba zai hau sama ba

Sheik ya yi murmushi yana kallonsa a tausashe ya ce" Bawan Allah, ka dubi girman Allah, ka yi kokari ka shinfida shinfida mai kyau a tafiyarka ta hanyar sanar mana abinda ka sani a kan auren nan da ya juya rana tsaka, kamar yadda ka sani a duniya idan bawa yanada hankali ba tsoron kowa zai ji ba sai na Allah, Akoy ranar fitar rai, akoy kwonciyar kabari, akoy tsayuwa a gabam ubangiji, ka yi kokari kaa tuna su sai ka zabi abu guda a ciki, tsoron dan Adam a duniya, ko na ubangijinka"

Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya girgiza kansa, a nutse ya shiga magana kamar haka" Umarni aka bamu, cewa zamu bayar da yarmu a matsayin gimbiya BAHIJA, aka kilacemu aka shiga shiryata dan kasancewa mata a wajen UMUGHLUK ITIBEL,"

Sheikh ya kalli ASADEEK, yana nan a yadda yake, kansa na kallon sama, sajensa da bakin gemunsa lufluf a Kwonce, yannayin da hannayensa suke zai nuna maka a wanu hali yake mai girman gaske

Sheikh ya sake sauke ajiyar zuciya ya ce" Ama, ko ka sam dalilinsu na aikata haka?"

Sosai yake jin girma da nauyin dalilin da suka sani, ama ya zala wajibi ya sanar koda hakan na nufin mutuwarsa ne

A sanyaye ya ce" An hada haka ne dan a kawar da UMUGHLUK ITIBEL daga doron kasa"

A zabure Sheikh ya sake fuskantarsa, muryarsa har tana hadewa ya ce" Kar ka yi furuci dan ka fitar da kanka , ka san girman laifin da ka ambata kuwa?"
Chapter 72 · 0% Book details