← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 99

Sashe 75

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin bayaninsu ya saka shi bada umarnin a barsu su shigo, lokaci daya kuma ya zauna yana dan dafe gabak goshinsa, sai kuma ya mike ya shige bayi dan yin wanka, ko ba komai zai so ace da dan karfi a jikinsa ta yadda zai iya fuskantar matan dake cikin rayuwarsa a irin wannan lokacin

Ya dan dauki lokaci a ciki sannan ya fito da alkyaba a jikinsa mai ruwan maroon da golding, kansa caje ba hirami a jiki, daga kasan alkyanar kuwa jalabiya ce fara sol da wandonta dogo , sai lulumshe luhu luhu din idannuwansa da suke da bukatar yin barci yake yi ama abin ya gagara

Tunda ya sauko sau daya tak suka yi ido hudu, a hankali ta sinne kanta ta lalubo hannun Auta ta jimke dan har ga Allah sai ta ji tsoron kallon idannuwansa jama'a kamar idan yana ganiyar cin zalin dinta wannan lumshe lumshe kamar kwarto?☹️

Gaishe da shi suke yi, kusan a tare, gaisuwa irin wace kowace ke yi masa, kowace da kalar tata , shi kuma yana amsawa hadi da dan sakin dan murmushi har ya dawo kan UMMA dake ta huci itama ta gaishe shi a yannayin da idan tana cikin bacin rai sannan wajen ya dan dauki shiru

Umma ce ta ja numfashi tana kallonsa ta ce" Yarona, abinda ake neman yi min a gidan nan yana neman kaini bango ta yadda ba zan dauka ba, sosai hakurina na son zuwa karshe a gidan nan gaskiya, haba dan Allah, da girmana da darajata? Ina kawar da kai ama sai an nunan iyakata?"

Nanauyun idannuwansa ya dago ya sauke dubansa a kanta, gaba daya sai ya ji irin tashin hankalin da a da yake ji idan wani ya dan bata mata yau ko diz baya ji, hasalima sai yake sin ƙaryata abinda ke saman fuskarta

A nutse ya cire dubansa yana dorawa kan HUZNAH wace itama tata fuskar har wani irin kumkum take yi, ga dukkan alamu itama kalar a kumbure take
A dan sanyaye ya ce" Huznah, zan sha tea"

HUZNAH ta kalle shi, sai kuma ta kalli NADIRAH wace ta yi tsuru tsuru a dan yannayi na jin haushi ta ce" To uwar iyayin gaure gyare sai ki bani ky na kawowa mijina Tea, hajia mai kwana!"

Gaban goshinsa ya dafe da dan mamaki ya kalli HUZNAH, sai kuma ya kalli Umma wace tamkar ruwa ya cinyeta gannin ga maganar da ta yi ama ASADEEK yake maganar yana son tea?, Hala cikinsa ana gaba da ita yai kuma?

A nutse ya gyara zamansa ya dubi Umma , a hankali ya ce" Umma, me yale faruwa ne?, Wani abu aka yi ne?"

Yar ajiyar zuciya ta sauke, duda yannayin da ya yi maganar kansa bako ne a gareta , ama da sauki tunda ya tambaya, dan haka ta fuskanceshi ta ce"Dangane da matanka ne da kuma Auta, jiya mun zo a tunaninmu kana nan ashe ka yi tafia baka dawo ba, ita wannan ta nuna mana ai ka yi tafia ne, ita kuma wannan ta dubi idona tace itafa ta fadi sako ko ban samu ba? Da na tambayi wani sako fa? Sai ce min ta yi ita gaskiya ta soke cin abincin taren nan idan kwananta ne, wai ta dubi tsabar idannuwana tace min ana iya hannata sirri da mijinta?, Ita kuma wannan din ita dake baba ta biye mata harda cewa ai kwanakin nata zasu kare itama bata son gannin kafar kowa a nata?, Me kennan? Nice na zama tsohuwar banza nake gannin irin haka? Karshe sai na tambayi ita kuma Auta ina take daga shekaran jiya zuwa jiya, budar bakinta tace wai tana bangaren BAHIJA, wai ko tana som zama a cen? Bahijar dake yarinya zata iya kula da ita ne? Ka fa san Auta bata da lafia dole sai ni ke iya mata, ama haka ina ji ina gani suka tafi taren, kennan na yi abinda zan yi ko? Barci ban samu ba dan tunani , ina dakon shigowarka !"

Har Umma ta kai aya yana kallonta ne, kallo irin wanda yake son sake karantar harshenta da kuma abinda ke zuciyarta

A hankali ya kalli HUZNAH wace itace baba da Auta da kuma NADIRAH, a nutse ya ce" Ke din da girmanki ne kika aikata haka maimakun ki tsawatar? UMMA ce fa?"

HUZNAH ta sauke kanta, muryarta na dan rawa ta dago dubanta tana kallonsa ta ce" Allah ya huci zuciyarka shin yaya zan yi ne ni? Ka ga ina zamana sai ta ringa nemana da masifa, na fada mata ni bana so ama a banza, wai tace idan kwananta ne kar ta ga kafar yarinya ko ta tsohuwa a wajen, kennan ni da Umma ko???????"

Ido NADIRAH ta zarro, hakama auta, NADIRAH ta gyada kai tana sake kallonsu

HUZNAH ta ci gaba da fadin" Sai ta ringa nuna kamar ta fini sannin mijina bayan bata jima da shigiwa gidana ba, ni ban yiwa Umma rashin kunya ba, gani na yi tunda hakane nima a barni da mijina ranakun girkina ko?"

NADIRAH ta tabe baki a ranta tana ayana' mijina mijina, da acema ana son mijin naki ne malama sai a yi fadan?'

Bakinta dake musmusmus yake kallo har ta zabga harara ta tabe bakin sannan ya gyada kansa a ransa ya ayana' Hum abama yace tuzuruwar kauye'

A bayane kuwa ya ce" To ke BAHIJA me yasa kike haka ne?"

A dan zabure ta kalle shi jin sunnan da ya kireta da shi kuma yanzu, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya a kasan zuciyarta tana ayana' Kai Alhamdulilah ashe gwara da ban sanarwa innata cewar wani ya fada masa wacece ni, ta yiwu an kawo masa maganar ne ya karyata, uhum ka ji dai da shi!'

A bayane kuma Sai da ta tabe baki, wanda ya kula idan ya kireta da Bahija take aikata hakan sannan ta dube shi ta ce " Yo ni me na yi kuma a nan, ni fa ban ce kafar yarinya da ta tsohuwa ba, cewa na yi kafar baba da ta y'a, ina nufin Auta ai itace y'ata ko?"

Daga su har Autar kallonta suke yi bayan ta dire maganar ta kuma cuno baki tana gyara zamanta a dole ita ta gama magana kennan, wai Autar ce y'arta yau kuma mai gaba daya, watau ba zata daina cusawa HUZNAH haushi ba ko? Kennan Auta na kiran ASADEEK aba, ita Mama ☹️

Habarsa da ya talabe ya saki yana girgiza kansa ya ce" Uhum, Allah shi kyauta, kin ga Bahija ki kula, bana so ana raina baban mutun, Umma dai da HUZNAH sun girmeki kin ji ko? Ki daina rainasu kin ji?"

Irin yadda yake maganar tamkar yana rarasshinta ya saka daga UMMAN har HUZNAR zuba masa ido da mamaki, Auta kuwa dariyarta take ci a zuciyarta, dan dama tunda suka farka NADIRAH ke fadin kar dai ta yi barci ta san Umma tace yau zata kai kararsu ya dace a yi komai sunna nan kar a zaluncesu

Auta yake kallo, yannayin shigarta ta yau, irin yadda idannuwanta basa neman rufewar nan kamar yar maye kulun, labewar nan da tsoron nan, uwa uba irin zaman da suka yi ita da Nadirah na kugu da kugu hannunsu rike ya saka shi dubanta da kyau, a hankali ya ce" AUTA?"

Fuskarsa ta sauke fararen idannuwanta , a nutse ta amsa shi tana dan sakin murmushi

Hannunsa ya miko yana kallonta ya ce" Zo nan "

A hankali ta karasa ta zauna a kusa da shi kamar yadda ta saba, a sanyaye tana mai fitar da murmushi ta ce" ABA "

Murmushin nata ya saka shi sakin murmushin shima a hankali ya shafa habarta sannan ya kama hannunta na dama yana kallon fuskarta ya ce" Me yasa ga yadda Ummanki ke so, ke kuma kike son daga mata hankali? Ummanki ce fa?, Kin san kaunar dake tsakaninki da ita ya dace ace kina bin umarninta ko?, Kin ga saboda rashin lafiyarki take tsaye take faman ki daina fita ko?"

Idannuwanta ta sada, hannayenta na son su dauki rawa kamar yadda suka saba a da, sai dai da karfi yana jin irin yadda take son controling din tsoronta, wanda karara ya gani a cikin kwayar idannuwanta, hakan ya saka shi a tausashen ya kuma cewa" Idan kuma kina da bukatar mutane a gefenki ne ko da dare ki sanar min mana Auta?"

Dago idannuwanta da suka cika da kwallah ta yi ta saka a cikin nasa
A sanyaye ta ce" ABAHNA, NI BA MAHAUKACIYA BACE"

Dum gabansa ya buga yana kallonta, kanta ta sake sadawa sannan ta ce" ABAH ni ba mahaukaciya bace dan Allah Aba, ka barni na ci gaba da zama tare da aunty BAHIJA ko ka mayar da ni gidan SALEEF "

"Ba zaki koma gidan SALEEF kina yin abu ana bazaki a duniya ba, Gidan saleef din ba a cen kike koke koken abanki kike son gani ba?, Yaya muna magani ido rufe kina son mayar mana da shi baya? Babu inda zaki je, dakinki zaki ci gaba da zama!" Umma ta fada a kausashe da kuma dan karfi, hakan ya saka Auta jimke hannunsa kanta a kasa , lokaci daya kuma jikinta ya shiga rawa, ya salam, ta zata zata iya din kamar yadda NADIRAH ta sanar mata cewa idan ta jajirce zata iya, sai gashi tana rawa kamar farar takarda a cikin iskar sararin samaniya a gaban UMMAN, to ita ta yaya zata iya cire tsoron matar nan gaba daya a zuciyarta ne? Ta ina zata fara wannan aiki mai girman gaske ne? Aikin nan fa ya girmameta sosai, ta yaya zata fara shi ne?

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

5️⃣4️⃣
Chapter 75 · 0% Book details