← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 99

Sashe 24

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonta ya yi a kausashe ya cire idannuwansa da kansa ya mata alamun kwarai haka yake nufi

Zuciyarta sai da ta yi wani irin tsale ta daki kirjinta dan buguwa da faduwar gaba, sai dia bata yi magana da karfi ba dan ta kula ya fita hawa sama yanzu

A tausashenta ta ce" Ama gidan Bahija fa ka ce Aban Bahija?, Gidan da ka kashe makudan kudi million na gugar million la ginna shi?, Gidan da ka yi masa hawa hawa hawa ka zuba gazon ka yi masa ginnin a zo a gani kace na Bahija ne saboda ita daya ce mace cikin yayanka itace abin tausayi, sauran su nemi nasu maza suke shine zaka saka sunnan wata a sama?"

A kausashe ya ce" A da ba, a da da nake tunanin na isa da ita, a yanzu gaskiya kowa ya yi ta kansa kawai tunda har ni zata duba ta yiwa rashin kunya!"

"Aban Bahija, ka kiyaye, kar son zuciyarka ya fi karfinka wannan karron, domin ka san abu ne da ba zai taba yiwuwa ba, kar girma ya fadi a kan abinda bai kai darajar haka ba!" Ta fad a dan kausashen itama, domin abin ya fara bata tsoro, gidan Bahijarta? Gidan da take takama da shi a cikin kishiyoyi? Bama a lokacin da ake kan ginninsa basu isa su hadu da ko daya ba sai ta yankawa mutun magana, bale a yanzu da aka gama? Da gadara gadara take dauko maganar gidajen sarki tace kaf ciki gida uku ne ya fi na Bahijarta? Lalle akoy tashin duniya a garin nan!

Zamansa ya gyara da shauki irin na yan duniya ya ce" Kina tunanin da abinda kike tunani ne gidan nan zan malaka mata?"

Kai ta juyar ta sake kallonsa ta ce" To nima shi na gani, me zai hanna ka saka sunnan Uban yarinyar idan ya so idan aka daura aka tafi da yarinyar sai ka maido sunnan Bahija a sama?"

Habarsa ya kama da mamaki ya ce"

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

1️⃣6️⃣

Jinjina da ban girma zuwa a gareku masoya, Allah ya karra lafiya da nisan kwana da rufin asiri amen

Habarsa ya kama da mamaki ya ce" Ke maman Bahija ki ji tsoron Allah, in ba abinki ba yanzu ai ba'a wannan kasadar, mace itace uwar ya'ya, itafa ba zata siyar da gida ba yayanta na ciki, shi yasa fa ake fada maku ku daina makahon so dan idan kuka ringa mika mana kudadenku da yan kadaririnku mun ga damar a kan gardama mu batar da su a dawo a shiga uku, shi yasa na saka sunnan maman yarinyar dan kar a je a dawo mijin ya siyar da gidan, sannan ke in banda abinki in kyautar abinda kike tunani ne ai ba dai wannan gidan ba, dan gaskiya na raina shi wa FATIMA, sai dai wancen gidan na nan gaba kadan , kuma da kuke cewa abu ba zai taba yiwuwa ba lamarin na Ubangiji? Da na zama sarki gadon Ubana ne? Sai ki ga abu ya zo da karar kwana, Sarkin dogarai ya tafi, a cikinku ke ko daya ta tafi, kin ga sai in kawo Fadima malan, mata su ringa tafe maza na rakiya da ido, Allah dai ya sa da sauran karfin yin aikin da ya dace a jikin maza"

Bata taba jin cin fuska da rikaken iskanci irin na yau ba, a matsayinta, da kimarta, da isarta, da kyanta mijinta ya ringa magana irin wannan a gaban idannuwanta? Ashe haka abin yake da ciwo? Idan zata tuna shekarun baya da ta hada matansa da lalurar rashin anfanarsa a saman bed a gaban idannuwansu yake kodata da mata kirarin da sai dai ta ga sun sada kai, ashe haka abin yake?
Mikewa ta yi tana gyara alkyabarta, domin ba zata iya ci gaba da maganar nan a yanzu ba,

Har ta juya ta jiyo muryarsa yana fadin" Ki tabatar WA'INDA zasu bata kula dan gyaran mu'amalarta sun iya kuma sun iya rike bakinsu, gyaran amaryarnan da ake yi ai ita yar nan inaga bama ta bukata, yarinya da ace a gidan hutu ta tashi har an shiga uku da kallonta, ni da kaina saura kirissss nace alfarma aka yi masa yaron cen!"

Zuba masa ido ta yi, gashi dai shekarunma sun ja fa, ama tatacen iya shege a gindin bawan Allahn nan,
Murmushi ta karkaro mai daci a ranta ta ayana' Lalle baka san kaidin mace ba, da ka wulakantani da kula baiwarka ko a dadironka ce gwara na kumsa maka shinkafar bera ka ci ka kumbura ka fashe a dakinka, dan walahi mutuwarma ba zan bari ka yi mai daraja ba tsohon najadu!, Gida kuwa karya kake ka ba wata katuwa yata a raye a zaune ita ta tashi a banzar bazara kennan?"

A bayane kuwa sai ta yi murmushi ta ce" Du ka rikice Aban BAHIJA, bayan baiwa sunnanta baiwa"

Murmushi ya yi yana janyo abincinsa ya ce" Hakane, sai dai wata baiwar cike take da BAIWA, abin saima an dangana da room din ciki"

Da sauri ta yi gaba, ta fahimci yau banda yan wulakancin harda yan iskan ke kansa

Tana zuwa bangarenta ta saka aka mata kiran masu gyaran jiki da lamura na gidan sarauta, bata haye bangarenta ba sai da ta ja masu rikaken warning ta kuma sheda masu aiki tukuru, kar su ringa hutawa sai na cin abinci ko yin sallah idan sunna yi, kar su barta ta huta sai sun gamsu da yannayinta, gyara na waje kadai ba sai sun yi mata na ciki ba domin ba bukata, sannan su iya bakinsu, sai nan da kwana goma za'a dauko su

Tana shiga sama ta bude whatsup dinta ta masa magana a kan matansa da kuma ya'yansa, sosai ta tuna masa me suke son boyewa sannan ta sheda masa cewa ya yi da gaske idanma ba hali kawai ya fitar da su waje, sannan ta kashe ta ringa kai kawo zuciyarta na mata daci, da gaske fa magangannunsa sun mata zafi fiye da tunanin bawa, haka kuma maganar gidan nan ta daga mata hankali, sai dai ba komai zata bi abin yadda ya dace, idan ya yi wasa sai ya wayi gari ya ga wata gagarar ta gagareshi! ( Ku dai kuka sani ku kashe kanku )

________________________

*AGADAZ*

Lulumin da aka wuni da shi jiya har aka kwana da shi wayewar yau ya saka yawancin jama'ar garin hutawa, idan har ba aiki nw da kai a cikin masarauta ba to fa kana hutawa ne, domin sanyin garin ya hadu ya bada wani irin sansanyan ni'ima mai tada tsumin mai mata, ya rikita gwauro

A irin wannan lokacin, a cen cikin dakinsa ya gaji da murmususun tashin hankalin dake jikinsa ya mike cikin nutsuwa ya watsa ruwa sannan ya sha lipton mai zafi ya saka sasaukar sutura ya fito daga dakinsa yana duban agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yana tunanin Anya yau zai samu zaman da yakan yi da Auta kuwa? Ya tabata itama tana cen daki ta labe dan bata son sanyi, gashi irin ranakun nan da baya fira fada, baya amsar korafin kowa yake samun zama da ita su yi hira da wasa da dariya

Karar TV ya saka shi dakawara daga sama ya dubi kasan dan gannin wa yake kallon a falonsa? Ya tabata ba zai wuce cikin mutun ukun nan ba, dan su kadai sukeda wannan damar a masarautar, ta shigowa Falon nan kansu tsaye

Ido ya dan zarro gannin abinda yake hange, watau su ukun ne gaba dayansu a zaune a falon, harda su TV? Ikon Allah

Kasancewar jalabiya ce mai ruwan milk colar a jikinsa sai dan ta karra haska farar fatarsa sabbaj ta lafe a jikinsa kadan har ana iya gannin farar rigar dake ciki da kuma wandon rigar da bai idasa masa har cen idon kafa ba

A nutse ya idasa saukowa, dukkan hankalinsa akansu , a lokaci daya kuma Umma da matarsa suka mike dan girmama shi da yi masa barka fa saukowa, Auta kuwa ta sauke ajiyar zuciya murmushi na wanzuwa a saman fuskarta ta dago daga rubutun da take yi da larabci tana kallonsa

A tausashe ya amsa gaisuwarsu da murmushi kawatace sannan ya zauna a kujerar da take tasa ce, dama babu wanda ya hauta yana duban Umma cikin fitar haruma kamilalu ya ce" kin jima a nan ba Umma?"

Umma ta yi murmushi tana kallon Matarsa da ta dawo dauke da abin sha mai sanyaya zuciya ta tabe bakinta a boye sannan ta budi bakin tana kallonsa ta ce" Ban jima sosai ba Yarona, ai ko wuni na yi ba zan gajiya ba tunda magana ce da ta shake ka, ka ga kuwa dole na bada hankalina dan gannin na tsaya tsayin daka a kan komai"

Kopin ya amsa dauke da jus na Tataciyar Kankana uwar ruwa ba siga sai madarar peak da aka kwalala ta zamo mahadin markaden kankannar ya sakar mata murmushi a saman lebensa ya furta" Allah ya maki albarka"

Murmushin ta mayar masa itama tana jin wannan Adu'a har kasan zuciyarta sannan ta mayar ta sake dawowa ya zauna a daf da kafafuwansa ba ruwanta da wata Umma bale Auta da sam hakan ba damuwarta bane ta kamo kafarsa ta dama ya dora a saman cinyarta dake dauke da tufafi fati irin shigar mata, watau lesh mai tsarin kwaliya fa kyau a hankali ta shiga dan mamatsa masa yatsunsa wanda hakan ya saka shi dan sake kureta da ido sannan ya dauke dubansa a hankali ya maida kan Umma da mamaki ya kusan kasheta da tunanin lalle tana sake fa da yarinyar nan, itace har ta samu damar taba kafar ASADEEK? lalle wannan din wani shinfida ne dake nuna mata cewa gaba ana iya zarce haka

Lebe ta dantse a ranta ta ayana' Sakarya, babu anfanin haihuwa ama sarauta da kudi sun zaunar da ke shekara tara, haka zaki kare in dai ba zaki tafi ba, barama na cusa maki bakin ciki'
Chapter 24 · 0% Book details