← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 99

Sashe 43

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Umma ta mata alamun kar ta mike daga tsugunin nan, a dole ta sake gyara tsugunin nata tana girgiza kai irin abin nan fa ba zata iya ba walahi!

A hankali ya dago kaansa dake jingine idannuwansa a lumshe y bude su y fara sauke dubansa a kan Umma, wace ke gurfane kanta a kasa

Tambaya ce ke saman lebensa, wace take daf da fitowa daga bakinsa, itace wannan din kuma wacece?
Sai kuma ya ji wani sashi na zuciyarsa na yi masa wata tambayar, shin UMMA bata san Bahijar bace aka miko mata wannan a matsayin Bahija? Wannan din wacece? Me yasa aka ce za'a bashi auren Bahija aka bashi na wata? A sanninsa bafansa y'arsa mace daya tak ce, itace wace suka yi tafiyar nan tare, bayanta a ina ya samo wannan?, Alamun wannan sun nuna ita din ba yar gidan sarauta bace, domin dan gidan sarauta ko yaro karami in dai ya fara iya hada magana ya iya gaisuwar sarki

"Allah ya huci zuciyarka, yarinta ke dawainiya fa ita, a yafe mata, tana tuba in sha Allah ba zata kuma aikata makamancin wannan gangancin ba" Umma ta sake fadi a tausashe tana sake sada kanta

"Yarinta?, Ganganci? Wannan din ai ya fi karfin ganganci ga mace ɗaya tilo da aka bashi a matsayin BAHIJA, lalle sunne suka yi ganganci wajen manta abu mafi mahimmanci, to shi a yanzu tamabayar da ta maye gurbin wacece wannan din itace....menene dalilin yin hakan? Ko yace menene mission din da aka ba wannan din?, Shi sai yake gannin kamar fitsarariya ce yarinyar, jama'a wannan kallonsa da take yi ido cikin ido fa?, Ga kuma gaisuwa irin sako da sako

A hankali NADIRAH ta sake satar kallon Umma, to wai ita a ina du ta fadi magangannun nan da ake cewa ta ce?, Uhum, wai yarinta ganganci, zaki ga aikin ganganci kuwa

A hankali ya gyada kansa yana sake dauke dubansa ya sake mayarwa kan Auta

Ido hudu suka yi da Auta, sai yake karantar kamar ta afka a tunanin son gane yarinyar nan a cikin mahaukatan ita baba ce ko?

A hankali ya sauke dubansa a fuskar HUZNAH
Idannuwanta cike da lamari irin na rarashi da girmamawa, shigarta ta birge shi sosai, itama HUZNAH leshen ne yanaga a jikinta, kuma dinkinta sakake sosai , Huznah kam akoy hankali
Kan matar dake duke, wace yake kyautata zaton baiwarta ce ya sauke dubansa, tun dazu take duke haka, sai ya samu kansa da yin gyaran murya yana duban matar

Shirun da ya gani bata tashi daga gurfanawarta ba ya saka shi sake dora dubansa a kan Umma
Lalle matar nanma ba ta gidan sarauta bace, ba kuma baiwa bace

Da sauri Umma ta mike, kafafuwanta har sunna neman yi mata nauyi, rabonta da shiga dimuwa irin haka tun wani lokaci da mahaifiyarsu ta tardota tana zane Auta,

A hankali ta dafa Inna kasa kasa ta ce" yana nufin kina iya tashi"

Inna ta dago tana jan hanci ta saci kallon y'arta, oh duniya yau ga abin jibga Indi ta yi ba halin ta zauneta ta jibgeta? Innalilahi ita HINDU ashe zata ga wannan rana irin haka? Dole yau ta Jibgi Indi walahi!

Kanta a kasa ta shiga kokarin kamanta gaisuwa da neman afuwa kamar yadda ta ji matarsa da kanwarsa da Umma na yi, sai dai itama bata san a yi masa maganama masu wannan yancin kai tsaye makusantansa ne

A hankali ya jimke hannunsa jin kamar bacin rai na neman hadasa masa mijirya a gaban jikinsa

Umma ta salami HINDU fuskarta har tana gyatsine dan rikicewa

A hankali ya budi bakinsa maganar farko ya ce" Umma, kina iya tafia"

Umma ta kalle shi, hankalinta a tashe ainun, sai dai ba damar jan maganar dan an masa laifuka a jejere sosai

A hankali ta karra neman afuwarsa sannan ta nemi da NADIRAH ta mike su tafi

Da mamaki Auta ta kalleta, hakama HUZNAH

HUZNAH ce ta yi karfin halin fadin" Aa umma ki je zata zo, bamu gaisa ba fa"

Umma ji ta yi kamar ta karasa ta shaki wuyan HUZNAH ta gaura mata tagwayen mari, sai dai ba hali, a hankali ta saki.lalausan murmushi sannan ta kafe NADIRAH da ido, wace ke duke ba'a bata damar tashi ba, ita gaba daya bama fahimtar wannan magama kamar masu ciwon baki take yi ba, kamar ta yi kisa ? Wai shi sarkin adalci? Walahu harda zalunci a jerin sunnayen nasa , in ba wannan ba me ta masa daga haduwa? Koda yake mutumen da ya tsofi su Inna ai sai hakuri da hali, itafa kowama ya kama kansa fa, itafa bata zo wajen nan dan komai ba sai dan ceto, ceton kuwa zata yi shi ne ta hanya daya tak, idan sun tashi karshi ta fada masa, dan ba zata iya kayan takaici ba,wani zuwa gaishe gaishe da sauransu gaskiya bata so, ita da ta so ta fita bayan magaribar yau ta zazaga masarautar babu alkyaba? Ta gaji da zaman dakin ya fara hadasa mata ciwo

Jiki ba karfi Umma ta juya ta fice, ji take dama tana iya zama kuda ta lane a jikin NADIRAH ta ringa daidaitata?, Ya Allah!

Tana fita Auta ta sake kallon Yayanta

A sanyaye ta ce" Abah, ta mike daga tsugunnin? Ta tuba a gafarceta"

Baki NADIRAH ta turo kai kace zaa saka mata ribom ne a daure ta kalli Auta da kallo irin na harare harare wanda hakan ya saka Auta zarro ido tana kallonta

Bai ce komai ba ya mike a hankali ya juya ya shiga haurawa sama, wanda hakan ya saka Matarsa mikewa da dan sauri ta bi bayanshi

NADIRAH dai da ta dafe kugu sannan ta kai zaune a fili ta furta" A gayasssss" wanda sam bata san ya fito fili ba

Auta ta sake wangale baki da zarro idannuwa kamar zata fado dan mamaki tana kai hannunta daidai bakinta ta furta " Lah "

NADIRAH ta dago tana kallonta, samun kanta ta yi da karra kallonta itama , sai kuma ta ce" Yo tsakaninki da Allah me na masa ni, tun dazu kuke cewa na tuba kuma bakwa fadin laifina, shikenan dan nice bakuwa sai a cuceni? Haba dai"

Da mahaukacin mamaki hadi da wani zarro idon Auta ta ce" Aban ne zai cucekin ko wa?"

NADIRAH ta yi shiru tana kallonta, sai kuma ta mike tana kabe Alkybarta kamar ta yi kasa din nan ta ce" Babanki ne kennan?"

Auta ta girgiza kai tana murmushi itama ta mike tsayen tana kallonta ta ce" Yayana ne"

NADIRAH ta kama haba da mamaki ta ce" To fah, shi kowa Aba yake ce masa ne?"

Auta ta dage kafadu tana jin mamakin yadda Bahija ke magana a sake, irin ba abinda ya shafetan nan

NADIRAH ta ce" To sai an jimanku, bara na koma na san ana cen ana jirana"

Auta ta yi saurin fadin" Da wuri haka zaki koma? Ga fa abincin da aka tara mana saman table"

NADIRAH ta waiga wajen abincin, tsarin kwanonin kadai abin birgewa ne, sai dai a ranta ta ayana' kai ina, aje an zuba gubar a ciki' a bayane kuwa sai ta ce" Aa a koshe nake fam da kika gani a nan, a ringa bismillah dai in za'a ci abinci......
.."
Daga haka ta yi ficewarta hankali kwonce, ta bar Auta cikin tatauna maganarta
Haka kawai sai Auta ta ji kamar da wata manufa tace a ringa yin bismillah

Sai kuma ta koma ta zauna tana murmushi, rabonta da ta ga rikicewar Umma haka an jima walahi,
Ama wannan matar ko wacece ta birgeta, sai ta ji kamar kar ta tafi , kamar ta yi ta zama da su a nan din, tunda ta shigo wajen ake haba haba gwanin dadi

A tsaye take a gefensa, bayan dogon hakurin da ta bashi har ta rufe bakinta bai bata amsa ba

Sai da ya gama yanke shawarar abinda zai yi ya dubeta yana murmushi ya ce" Ba komai fs, ki je ku ci abinci"

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta juya ta tafi

Wayarsa ya dauko yar karamar ya zauna a bakin bed yana warware nadin Rawanin dake kansa

A hankali ya shiga wajen tarin uban miscall din da yake samu na number da aka duba masa aka tabatar ko ta wacece

Number ya dauka ya turawa yaronsa sannan ya rubuta masa mesage cewar a yi gagawar yi masa tracen number nan zai yi kira a sanar masa ina mai number take?

A nutse ya gyara zamansa sannan ya danna kiran ya ajiye wayar a kusa da shi yana dan shafa gemunsa idannuwansa sun kada sun cenza launi

Wayar na fara kuka aka daga, ringin ko na biyu bata yi ba aka daga hafi da sauke wata nanauyar ajiyar zuciya murya a birkice da kukan dadin gannin kiransa ta ce" Asalamu alaikum yah habibih"

ASADEEK ya sake murza sajen habarsa cike da takaici a takaice ya amsa salamar da lalausar muryarsa da karyewar harshensa tamkar balarabe

BAHIJA ta kai zaune tana kashe TVn dake kida ta dora hannunta daidai zuciyarta ta ce" Ina ka shige? Dan Allah ina ka shige? Har na cire rai, na yi kukan har na hakura, kulun cikin tunaninka nake, ka bani number na kira na kira ba amsa, tun bata shiga ta zo tana shiga, mamana tace ta yiwu aiyuka sun maka yawa, dan Allah ka fada min a wani gari kake a NIGAR zan zo, idanma baka da lokaci ni zan zo"

'innalilahi wa inna ilaihi rajune, ya Allah ya Allah me yake faruwa da ni ne? Wace aka daura min?...........'
A kala ta dauki minti daya tana ratabo zance na rashin kamun kai, har ya tabata ko menene sun gama masa a sanyaye ya furta" Zan yi kiran ki, zan je na dawo"

Muryarta a sanyaye ainun ta ringa magiyar dan Allah kar ya manta ya yi kiranta dan Allah tanada wata mmagana mai mahimmanci da zata sanar masa

Uhum kawai yace ya katse kiran,

A nutse ya mike ya shiga cire kayansa dan ya fara jin sun masa nauyi

Ya rage daga shi sai karamar rigar ciki da wandon shadar da ya cire
Chapter 43 · 0% Book details