← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 99

Sashe 74

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aba da kansa ke kasa bai dago ba, dan bai taba tunanin jin sunna irin wannan daga bakin UMUGHLUK ITIBEL a gareshi ba, sai da SHEIK cikin murmushi ya sanar masa da shi yake sannan ya dago kansa yana kallonsa da mamaki da kuma girmamawa

ASADEEK ya yi dan murmushi ya ce " Ina fata zaka iya yin rigima ?, Ina nufin fada haka"

Kallons kawai suke yi su biyun dan babu wanda ya fahimci inda ya dosa
Sai fa ya yi wani murmushin ya zauna yana gannin lokacin sallar Magariba ya gabato sosai ya ce" Ina so ne na aikata aiki mai dalili, ba wanda zan bar baya da kura ba, domin a yau ba sai gobe ba zan tafi da ku"

Aba kam bashi da abin cewa sai bin dukkan umarnin da aka tsara masa
Hankalinsa du ba a jikinsa ba ya mike ya fice ya koma da sauri, suma du suka mike suka nufi bayi dan daura alwallah da kuma kimtsawa komawa

Bayan an fito daga masalaci a gaban jama'ar anguwa Aba Salihu yana dan sauri ya zo ya bankade mutumen dake gabansa yana amsa call, mutun mai jikin girma sosai domin katon jiki ne da shi irin na karfe din nan , ga tsayi ga kuma baki

Da rashin damuwa ya ce" Haba malan ka kauce a hanyata mana ka wani tsare hanya da waya a kunnenka"

Kwarai abin ya ba yan anguwar mamaki, domin babu wanda ya taba jin muryar Aba sama sama haka, hakane ya sa aka dan kalle su da bakuwar fuskar nan, dan shi wannan din gaskiya babuma wanda ya wani sanshi a nan, yannayinsama ya badu mamaki da suka ga ya shiga masalaci an yi sallah da shi

Da mamaki mutumen ya nuna kansa ya ce" Kai, kana da hankali kuwa?, Yaya zaka bigeni ina tsaye ka kuma kasa bani hakuri? Hanyar taka ce? Ka iya bakinka ko a wajen nan sai na yi raga raga da kai ba ruwana da furfurar gaban goshinka!"

Aba SALIHU ya sake juyowa yana kallonsa, sai kuma ya kalli dan gidan liman, baban magidanci ya ce" Malan Rabi'u ka ga aiki irin na banzayen samarin zamanin nan ko?, Dan Allah hanyar nan ta tsayuwa ce a gaje waje? Bismillah idan tunaninka ni banza ne ka farka domin nan da kake ganina nine sarkin dawakan mai garin nan!, Ka kuwa san ko ba a ba banzaye rikon wannan sai rikakun mutane!"

Wufffff mutumen nan ya karaso a kiftawa da bismillah ya shaki wuyan Aba ta hanyar hadawa da jalabiyarsa ya nemi cira shi sama a haka

A rikice datawa da damarin anguwa suka shiga kiciniyar rabawa ciki kuwa harda masu gadin gidan su biyu rai bace ala samu da kyar aka raba tsakani kowane na haki aka ririke mutumen nan dake karra cika kumatunsa da iska na bacin rai

Da karfi ya warce hannunsa guda ya nuno Aba a gaban jama'ar nan ya ce" Ka ci nasara tunda har ka ja a wajen da za'a lwaceka!, Ama ka sani da wanda baya yafiya ka ja rigimar!, Ina ruwana da wata sarautarka ? Banzar sarautama irin ta garinku!, Ka sani ka yi da mahaukaci domin ba kai kadai ba harta iyalanka idan kana da su sai na ga bayansu! Sai na karar da ku !"

Da karfi ya warce hannayensa ya juya ya ringa tafiya irin an bata masa ran nan

Nan f aka taru a kan ABA ana ta jajantawa da kuma yi masa Adu'ar tsari, bama kamar Liman da ya ringa mamakin furucin gannin bayan nan, sosai suka yi masa addu'a da raka shi har kofar gidansa sannan kowa ya yi tafiyarsa

A nan kofar gidan suka dora zamansu yadda suka saba, kowane sai fadi yake yi lalle saurayin nan wani dan ta'adda ne, ama ba komai ya zo din zai tardo maza zai saka kansa a uku ne, irin kurin nan na bayan ido har lokacin sallar isha'i ta yi suka je suka gabatar suka dawo suka amso abinci a ciki suka zauna sunna ci sunna dan taba hira, shi dai Aba SALIHU hankalinsa du a rabe yake , har dare ya tsala kusan karfe biyu ta yi sawaye suka dauke sai su uku a kofar gida

Mikewa ya yi yana masu salama sakamakon alamun da ya gani an masa ya juya ya shige gidan, summa sunna yi masa da fadin sai da safe su kam ba zasu kwonta yanzu ba

A nan a zaunen bayan shigarsa mutumen nan ya bayana a gabansu da bakaken kaya sidik
Kafin suke yin wani yinkuri ya riko su da hannayensa daidaya ya masu mugun rikon da ya saka su neman agaji ta nufin fara kurma ihu, sai dai basu samu damar yin hakan ba aka shaka masu wata hodar da ta bugar da su gaba daya daga duniyar mutane

Nan suka yasar da su suka shige ciki

Hankali kwonce ya fito da FATIME dake ta aukin tambayoyi shi kuma yana bata amsa a gagauce yana janta kiiuuuiuu dan sai tirjewa take yi gaba daya ta kasa fahimtar yarensa a bayane
Sai da suka fita sannan su suka shige, BAHIJA dake kwonce tana barci daidaya suka shakawa cikin barcinta ya daukota ya yarda ita a nan kan kofar shigar , sannan suka kwashi abubuwan anfaninta dukiya ne da su wayoyinta kaf masu dauke da numbobin UMUGHLUK ITIBEL, komai da komai, sannan suka je dakin su FATIME din suka barbaza nata suturun suka yayaga wasu da mumunar yaga suka zubar a kasss , na mijintama suka ringa yayafa jinnin kazar da suka yanka kadan kadan , suka fito sunna tafiya mai jan kafa sunna didiga jinnin a hanyar har suka fito sannan suka karasa daf da motar dake jiransu suka mika buhun kayayakin sannan suka tafi da sauri a kaffafuwansu wajen da Sarkin yanka ya ajiye nasa dokin dan ya kunce shi su dauki hanya domin SHEIK ne zai tuka motar su kuma su hau dokin, iyayen NADIRAH kuwa su shige bayan

A rikice SHEIK ya sake kallon ASADEEK ya ce " Ka fa san akoy Nisa tsakanin Tanut da AGADAZ, ka bani dama na daga mana kar a kama mu!"

ASADEEK da ya rufa rawaninsa a saman kansa ya dan kalli SHEIK, tsakani da Allah SHEIK a tsorace yake , zagayawarsama uku a tsayuwar nan

A hankali ya juyo wajen da Fatime ke ta dhashekar kuka , kallo daya ya yi mata ya mayar da dubansa gaban motar a tsanake ya ce" Mu je"

Motar na fara tafia FATIME ta dago hankalinta a tashe ta kalli mijinta , muryarta a raunane ta ce" Idan fa suka gane mu muka fito da kanmu suka nemi halaka Indin Hindu? Idan fa suka fahimci cewar mun.............mmmmm............."

"Inna" ASADEEK ya fada a tausashe ainun

FATIME ta yi dif da kukan ta sada kanta muryarta a raunane ta ce" Allah ya huci zuciyarka, Allah ya karra maka lafiya"

Dan murmushi ya yi yana kallon hanya
Da kamar minti biyu ya dan sake bude bakinsa ya ce" Bana tunanin dan Adam zai kuma samun wannan damar, sai dai kuma idan mutuwa ta riskeni..... ALLAH YA SANYAYAR DA ZUCIYARKI" daga haka ya kame bakinsa , hasalima carbin SHEIK yake ja bayan ya lunshe idannuwansa, SHEIK kuwa tuki yake yi dan gaske, duda rashin kyan hanya a haka yake sarafa motar yadda ya dace , ta yqdda du inda suka tardo jami'an tsaro za'a dage masu su wuce ne dan an san sun zo ana kuma sane da a yau zai dawo domin SARKIN YANKA ya fada

Direct gidan..........

😍😍😍😍😍

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

5️⃣3️⃣

Direct gidan SHEIK suka nufa , a nan SHEIK ya jagoranci wajen da zasu zauna, waje mai tsari da tsaro

Ba su su bar gidan SHEIK ba sai da karfe hudu da rabi ta yi, ASADEEK na tsaye da rawaninsa yana gannin yadda aka basu masauki mai kyau, matar SHEIK wace ke turaka a daren tana tsaye a kan kaffafuwanta dudaa bata san ainahin da wa ake tafe ba tunda ta ga Mijinta ya fitar da ita a irin daren nan ta bada dukkan kulawar da ta dace ta hanyar saukar bakin da mahinmanci

Sunna komawa fada masalaci suka yada zango , sai da duka yi sallar asubahi sannan suka yiwa junna salama kowane ya koma gidansa dan hutawa, domin tafiyar ta ja masu dogon zangon da basu zata ba, ba laifi kowa ya gaji danma jiki ya saba da wasu wahalhalun ai da ba za'a iya jurewa ba

Cikin nutsuwa ya haye saman gadonsa yana mai Adu'ar neman tsari sannan ya shiga neman barci ido rufe, ama abin ya gagara
Yinwa yake ji a cikinsa, ama ya san ba zai iya ci a yanzu ba, uwa uba damuwar da yake kaucewa tana ta so ta yi tasiri sosai a zuciyarsa har ta hanna masa yin barci

Du irin yadda yake yin karfin halin kautar da tunanin UMMA ta san tsare tsaren bafansa shin tana tare da su dan kaunar lamarin ko fin karfinta aka yi ta amince ya kasa fita daga zuciyarsa
Kwarai ya san baban burinsa ya tarbeta ya tambayeta, sai dai banzan tunani irin nasa ya hannashi hakan, ya fi ganewa bin sawayenta dan ya gani da idannuwansa domun baya tunanin a irin wasi wasin da zuciyarsa ke ciki in har zai iya yarda da kalaman bakinta, ba dan ya taba kamata da wani hali irin karya ba, sam, dan kawai zargi ya rigaya ya darsu a zuciyarsa dangane da ita lokaci daya, zargi mai girman gaske

Haka ya ringa cenza wajen kwonciyar ko zai ji dadin yannayin kwonciyar, ama abu ya gagara tamkar yaron dake laluben mahaifiyarsa haka ya dawo yi a saman bed din , ya kula wannan ya kunce wannan har kuraye kirayen wayar tafi da gidanka dake garkame ta fara damunsa ainun

Da mamakin gannin kiran masu gadinsa ya daga yana karama a kunnensa, dan ya san dai ya sheda masu barci zai yi in ba dalili mai karfi ba kar a tashe shi, sai ga kiransu ba kakautawa
Chapter 74 · 0% Book details