← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 99

Sashe 37

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta kifa kanta a saman abin kujerar tana hadiye kukanta, ita abinda ya fi damunta irin ya bari su ringa wasan da za yana taimaka masu wajen rage masu sha'awama baya yarda, kwata kwata baya yarda, abin ya masa yawa jama'a, ita fa da sauki, walahi da sauki ita, shi ya fi bada tausayi, baby gaba babu baya, matsalar ta masa yawa jama'a, kuma ya bari irin abinda take koya a karance karance ta ringa yi masa sai ya kiya, sai yace shi ya san kansa, ba zai taba bari ya aikata haka ba, domin cutar zata koma ta kwonta a cikinsa, a yadda ya giga ya fi karfin a matsashi ya rabu da malati, ya fi karfin haka

A hankali ta dago fuskarta, muryarta a raunane ta ce" Ka san menene UMUGHLUK?, Ta yiwu idan ka gwada da wata macen fa ka kai ga ci"

Idannuwansa a lumshe suke, a haka ya dauki minti kusan hudu da yin maganarta bau bude ba, haka kuma bai bata amsa ba,
Har ta cire rai ta ga ya dan daga hannunsa kadan sannan ya mata alamu da tana iya tafia

Sosai ta ji zuciyarta ta sake karye mata, a hankali ta mike ta fito daga dakin nasa tana tafe a hankali a hankali cikin duhu zuciyarta na sake tsintsinkewa har ta karaso kofar AUTA

Samun kanta ta yi da kama kofar ta bude ta shiga da salama cen cikin makogwaronta

Auta dake saman salaya ta dago a hankali tana kallonta, shafa'i da wuturi ta gabatar tana jan carbi ne, dan haka ta dan zuba mata ido na dan lokaci sannan ta dauke idannuwanta

Huznah ta shiga dan kai kawo yatsarta yar karama a cije a bakinta, a hankali ta kasa, kasawa mai tsanani har ta silale ta fashe da kuka tana hade kanta da gwuiwarta

A hankali Auta ta shafa fatiha ta mike ta sake zuba mata ido, daga nesan nan tana kallonta, har sai da ta ji ta ringa sasauta kukanta sannan ta bude baki, kasa kasa, da murya mai sanyi irin na mahaifiyarta ta ce" Ki amshi sakinki mana, wannan zama ai bashida anfani ko?"

Kanta ta dago da idannuwanta dake zubar da hawaye ta zubawa Auta ido
Muryarta na rawa ta ce" Me me ya hanna ki amshi naki sakin bayan naki zaman ya fi nawa rashin anfani?"

Auta ta yi dan tsai sai kuma ta juya ta koma saman gadonta da carbinta ta haye tana ja ta lumshe idannuwanta

HUZNAH ta karra jan numfashi ta ce" Mijina ne, wanda na ba yardata, nake dakon jiran ya yarda da ni shima, ke ba yarinya karama bace domin kin dauki ciki har ya bare, kuma sarai kin san damuwar yayanki, me zai hanna ki bashi shawarar ya sasauta mana ne? Babu wace yake jin maganarta a duniya irinki, koda kina abu like baki da tunani wani lokacin a haka ya fi yarda da maganarki fiye da ta kowa, yaya zaki ce wai na amshi sakina, dan ba ke bace a wajena? Aure ne ya karra, ta yiwu nice rashin lafiyarsa? Idan haka ne yaya zan yi kennan ni?, Shine zaki ce wai na amshi sakina? Mema na yi maku da zafi ne?"

Auta ta bude idannuwanta dake lumshe ta juyo ta zubawa Huznah ido, a hankali ta ce" To ki yi hakuri kin ji?"

HUZNAH itama ta zuba mata idon, sai kuma ta dauke, dan sai ta ji ta fara tunanin anya Auta ba lafiyarta kalau ba kuwa?

Ture zancen ta yi ta mike ta bar mata dakinta, dan ta kula Auta a duniya ba cika son hayaniya ta yi kwata kwata, bale kwana biyun nan wata nutsuwa ke nuna kanta a tare da ita

Washe gari, tunda safiya ta waye yannayin Auta ya fara dawowa irin na da, tunda sako ya sammeta cewa ta shirya zasu koma gida gaba daya take neman ficewa a hayacinta
Ta rufe kanta ta yi kula, ta yi kula tsoro da fargaba sun dawo sababi fill a cikin zuciyarta
Sai dai tana kan ra'ayinta, da ta sauko ta ba matar nan abinda take nema gwara a wayi gari a ga gawarta, gwara ta mutu a haka nesa da mijinta, gwara ta mutu yayanta da kowa na yi mata kallon mahaukaciya, in sha Allah ba zata daina addu'a da kokarin isarwa da yayanta sakon da take so ya gane dan kankin kansa, in sha Allah ta san wata rana za'a dace, domin sau biyu tana gannin yana yin tsai da tambayarta kamar bata son Fada?......, Tana so ya fahimci ba faɗa bace bata so, abinda ke cikin fadar ne da kansa

Da kyar ta iya shiryawa, dan ta san ba jira yake yi ba koda itace kuwa

Alkyabarta ta dora a saman suturarta, domin su saka Alkyaba ya zame masu tamkar saka hijab ne, idan babu ita a jikinsune suke jinsu tamkar tsirara

Bugawar da akai mata ya sakata mikewa jiki ba karfi ta sake kallon dakin nata ta sauke ajiyar zuciya ta bude ta nufi motar ta shiga itama ta zauna ta hade kanta da abin motar tana kallon kofar da du ake jiran Yayanta ya fito

Cike da kamala, tafia t kasaita, jikinsa dauke sutura shiga ta albarka, mai dauke hankali mai matukar daraja, Alkyabarsa mai ratsin golding ce hakama takalminsa irin na saraki mai ratsin golding din ne, kansa dauke da rawaninsa, hannunsa na dama rike da Sandar girma

Yanaa fitowa wani bafade daga duke yana gyara rigarsa da kyau, wasu biyu kuwa na rike da lema , daga gefe wani na yi masa barka da fitowa a duken shima hannayensa a jimke yana ta faman yi masa kirari

Wajen mai garin garin ya ja ya tsaya wanda ya zube shima cike da farin ciki yana sake gaisar da shi,

Mikewar ya yi, domin damar hakan ya bashi da hannunsa

Yana mikewa kasa kasa ASADEEK ya ce " Jiya waye ya min allura?"

Mai gari ya karra sada kansa cike da girmamawa ya ce" Baban yarona ne Allah ya karra maka lafiya,likita ne ai a cen baban gari ya yi karatun"

Kai ya gyada a hankali ya lumshe idannuwansa, ba laifi Allurar ta taimaka masa sosai domin kafin ta fara aiki a jiya ji ya yi kamar zai ci babu, a kasa yake a yashe hannayensa damke da mararsa baya cikin hayacinsa, a dole mafadensa ya kai maganar wajen mai gari, shine suka zo da yaronsa baban likita ne, shinema ke kula da asibitin kauyen ya duba sarkin, nan ya fice da sauri a motarsa ya fita ya shiga gari a daren nan da balakin gudu ya je ya samo allurar ya dawo ya yi masa a lokacin fadawansa sun gama rikicewa harda mai kuka, sun kama da kyar sun mayar da shi saman gado
Bayan allurar ne ya samu barci , wahalalen barci mai cike da mafarkai,

A hankali Mai gari ya karra sada kansa, muryarsa a mutunce, a tausashe ya ce" Yama ce da zai samu ganawa da kai, akoy mahinmiyar maganar da ya dace ya sanar maka, sai nace sai na tambayi izini"

ASADEEK ya karra cira kansa yana bin mutanen da suke ta jifansa da kallo da dago hannu, wasu muryoyin na faman ambaton UMUGHLUK ITIBEL, sannan ya sake duban mai garinsu

A hankali ya furta" Ka sanar da shi, abinda yake son fada na sani ba yau ba, idan shi yanada wani maganin da zai karra kashe min cutar ina maraba da haka, idan babu, ka sanar masa cewa Haka Allah ya hukunta"

Mai gari ya dago ya dan zubawa fuskar ASADEEK ido,.duda rawaninsa ya tare komai, ama idannuwansa da girarakinsa na fili, ko a yanzu idannuwansa jansu ya wuce misali, haka kuma girarsa a hade take alamu ne na ransa a bace yake

Kai ya sada, shi kam da zai bashi dama da ya gwada nema masa magani, irin na hausa na gida, to matsalar tsoro yake kar aje ba zai yarda da magungunnan nan ba, kar yace ba kyau, ama wannan matsalar ai ga dukkan alamu samu ne, shiga gaba ne, tunda karara a jiya ya fahimci matsalarsa, kuma a halin jigatuwa muryarsa na fitar da magana a ciciren da ya dan fahimci wani abin, sai dai ba zai yi gigin kawo masa maganar ba, sai ya karra sada kansa a tausashe ya ce" Allah ya baka lafiya ANNEMOKAL ITIBEL"

Kai ya gyada a hankali ya juya dan nufar motar da zai shiga,
Daga dab nesa kadan da motar ya tsaya yana hangen Huznah da Auta

Huznah kallonsa take yi, irin kallon da ta saba koda yaushe, idannuwanta dauke da bege da girmamawa,du irin turetan da ya yi a hankali ya hango murmushinta sannan ya hango jimke hannunta, irin tana mai aiko masa da gaisuwa, yana sane da zuwanta da safe bata samu ganninsa ba

Kai ya dan gyada a hankali sannan ya dan sada dubansa alamun ya mayar mata da gaisuwar itama, sannan ya sake kure fuskar Auta da ido

Yannayinta ya saka shi jin jikinsa ya karra mutuwa, a nutse ya cire dubansa ya karasa wajen da aka bude masa mota ake jira

Yana karasowa aka shiga gyara masa rigarsa har ya shige ya gyara zamansa aka gyara rigarsa aka tsaya da jiran umarninsa na a rufe a dauki hanya

Motar dake gabansa wace Auta ke ciki ta fi daukan hankalinsa, hakan ya sa a hankali ya dan yi alamun zai yi magana

Sosai bafadensa ya kawo kunnensa yana sauraro

A takaice ya furta" Fatima ta dawo nan"

Kasa bafaden ya kara dukawa yana fadin" An gama" sannan ya je ya sanar aka bude mata ta fito ta karaso da dan sauri tana dan sakin fuskarta kadan

Shiga ta yi gefe aka rufe sannan ya bada damar a tayar su tafi

Sai da suka dauki hanya sosai, a hankali ya rike hannun Auta yana kallonta, muryarsa a nutse ya ce" Menene?, Bakya so mu je gidan ne?"

Auta ta kalle shi, a hankali ta shagwagwabe fuskarta, irin wannan kulawar sai idan Umma bata kusa take samu, idan tana kusa komai tarewa take yi , komai
Chapter 37 · 0% Book details