Sashe 19
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
UMUGHLUK ya dakata ya juyo
Lalausan murmushi ya sauke masa ya ce" Ai yarda da na yi cewa, da kai da kaya duka malakar wuya ne ya sakani baka dama, sadaki kuwa ai dama kai kake biya min Bafana,"
"Ama......?" ......
A hankali ya dakatar da shi ta hanyar fadin" Auta nake son yiwa lesson kafin magariba ta shigo, tana falona zaune, Bafa du abinda ka yanke ka sanar min ta waya in sha Allah, a sauka lafiys"
Daga wannan ya shige ciki ya barsu da kallon kallo kowa da abinda ke masa kai komo a ransa
Babu wanda ya ce uffan sai bangarensu da suka nufa , shi a gaba Gimbiya a bayansa da Umma
Sunna shiga Gimbiya ta fara cire Alkyabarta ta kuma yarwa a nan, a mugun kufule ta ce" Me yake takama da shi a duniya?
Mijinta ya kai zaune yana dane nasa bacin ran sosai ya ce" Kudi, da karfin mulki!"
UMMA ta zubawa Fadime dake tsugune nesa da su kadan ido, kasa kasa ta ce" Ku iya bakinku, ku fitar da Baiwarku"
Gimbiya ta kai dubanta kan Fadime, sannan ta maido kan Umma , a sharar fagen abinda ta yi niya ta ce" Baiwa? Ai baiwama mutun ce, balle wannan tawar amintaciyata kennan, bana darr da magana a gabanta!"
Da mamaki Umma ta zarro ido tana kallonta, sai kuma ta juya wajen Fadime wace ita dinma mamakin ya nemi kasheta ta ce" Tashi ki bamu waje zamu yi magana"
Mikewa ta yi, sannan ta rage tsayi a nutse ta furta" Ku huta lafiya"
Daga nan ta fice
Tana ficewa Umma ta juyo wajen Gimbiya ta ce" Lalle gimbiya, baki san a bayi akoy masu baban burin dake iya rikidewa su zamto matsala a tafiyar gaba ba?"
Gimbiya ta dubeta da duba irin na ki kuyayeni fa ta ce" Nice kat, domin kema rikidafiyar baiwa ce ta dawo mafi kusanci da UMUGHLUK ITIFAL!, Bama wannan ba, kema da baki zauna a kan kujera kin dauki darasi a makaranta kika iya zagaye bale ni? Idan na yi kwai da zakarana!, Allah ya karra maka lafiya aban Bahija magana nake da ita!"
Dubansa ya maida sosai a kanta, Umma kuwa ta karasa ta zauna sokoki a kasan zuciyarta cike da tunanin wannan mata , tan kyautata zaton sai ta yi da gaske a kan lamarinta!
Sosai Umma ta lakanci mijinta da sannin wanene shi, shi yasa cikin ruwan sanyi take gasa kishiyoyinta ba tare da ta bari sun san cewa itama yakan zuba mata hauka irin nasa idan ta raya masa,
A tausashe ta ce" Lalle ban taba ji hankalina ya tashi, raina ya bace irin na yau ba, ace mu tashi mu zo har masarautar nan, da mu da sauran baki du daya!, Wai yana ba WA'INDA suka yi sauka kyauta shi ga musulmi ko?, Ya bamu damar ganninsa ama a raine a wulakance? Ace kai da kanka Sarkina kana zaune yaron nan na maka magana da gadara da wulalanci da raini?, Lalle abinda ya dace da shi shine wulakanci, ina mai tabatar maka wannan yaro baban wulakancin da ya dace da shi shine mu dauki baiwa mu aura masa a matsayin yarmu!, Walahi sarkina wannan ne kawai zamu yi mu rama wulakancin da ya yi mana, duda baya iya tsinanawa mace komai ama ya zamto mun saka a tarihin rayuwarsa cewa ya taba zama mijin kaskantaciyar baiwa an gama, kafin mu gama da shi kuma sai mun bada dama ya sani sannan ta gama mana da shi?"
Wani irin zuba mata ido suka yi su dukansu
Da sauri Umma ta ce" Ama Gimbiya kin cika neman fitinar da kanki ba zai iya dauka ba!, Kina nufin zamu yarda a aura auren UMUGHLUK ITIFAL da wata daban da ba yarki ba kuma ya kasa sani??"
Gimbiya ta dubeta a kausashe ta ce" kamar da kasa in ji mai ciwon ido, ni inada yarinyar da ta isa ta amsa sunnan matar sarki!, Kuma a yadda na hangi yannayinta tana iya yin kisa a kan yan kudade kalilan, in dai ba so kike a bar maganar kisansa ba sai ki sanar da sarkina na ji!"
" Ba haka nake nufi ba, yau babu wanda ya kaini son gannin ya kauce nima na samu cikaken yancin baza abinda bake yi a boye a rayuwata!, Sai dai ina yi ne ina yi mana hannunka mai sanda, domin muna iya kai duka dubu bamu same shi ba a kawowa guda ya tarwatsamu!, Magana muke yi da ASADEEK BRAHAM!, Kuma da kika ce baya iya tsinanawa mace komai kar ki manta, shi abinda yake tare da shi da sunnan wace yake aure a yanzu kadai aka aikata masa da nufin ya fadawa wata ko shima zai samu hukuncin da ubansa yake yankewa yayan mutane dan sun kwonta da wata dan ra'ayi!, Idan har za'a aura masa wata ai dole zamu je mu nemo matar da ta bamu na farko ta sake bamu da sunnan wace za'a hada , dan kar ki aikatawa kanki aikin mugunta da kanki, watau kina gannin kashi da rana, da dare ki zo ki taka!" Umma ta fadawa Gimbiya tana cire kanta a bangarenta, dan ta kula yadda take shayin gimbiya haka itama ke shayinta
Kafarsa dake kan cinyarsa yana karkadawa da sauri da sauri ya sauke kasa, wani irin Farin ciki da hasaso nasara da jin dadi a maganar nan cewa a hada UMUGHLUK ITIFAL da baiwa na sheke duniyarsa a farin ciki ya fuskanci matarsa ya ce" Wace baiwa ce wannan kike magana a kanta?"
Gimbiya ta saki murmushi tana fuskantarsa ta ce"
🤔🤔🤔🤔🤔🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```

*https://www.facebook.com/106494781436168/*
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
_FREE BOOK_
*Na*
*SAJIDA NIGER*
1️⃣3️⃣
Gimbiya ta saki murmushi tana kallonsa, hum maza kennan, watau yadda ta lakanci bawan Allahn nan gaskiya zata iya cewa babu wanda ya sanshi irinta, ko haulan fada yake yi ta san me yake isarwa a sakonsa......, Kofa yake a da soyaya suka yi har ta kazance din nan, sun yiwa junna so irin makahon nan
Tana murmushin ta sake aro wata kalma dan sake buga zuciyarsa, a matsayinta na mace, tana cike da kishin kalmar, ama a haka ta riketa a matsayin makami dan ta kashe fitinar dake neman kunno mara kai na samun mugun sabani tsakanin mijinta da cilon y'arta mace, itafa mazan basa wani gabanta, ta sani ne sarauta tata ce zuwa gaba domin kuwa mazan manya kaf nata ne, shi yasa take tatala auta dan itama ta samu wajen da ya dace da ita, ta tabata abinda ya ruda zuciyar autarta ba karamin abu bane, ya cencenci jarida!
A tausashe ta ce" JINNIN FADIME CE!"
Idannuwansa a kan lebenta , tunda ta ambaci sunnan dake girgiza tunaninsa da rayuwarsa baki daya tsayin shekara da shekaru
Har wata zufa zufa ta nemi karyo masa a cikin kirjinsa, ya dan kawar da dubansa sannan ya sake kallonta a lokacin da ta yi kalar serius tana fadin" mun jima da rikon Fadime a hannunmu, mun san wacece ita!, A maganar halayanta mun dameta mun shanye mun san mecece ita, a maganar kyau kuwa da kira ko a yanzu da Fadime ta haura shekaru suka fara zuwar mata ai inaga ba boyayan sirri bane cewa kyakyawa ce akoy diri......., Ina mai tabatar maka yarinyarta ta girgije ta fi uwar komai, tsayi ne bai kai cencen ba, ama tsayinta daidai misali ne, ita ta dace da shi ba yarka mai daraja ba!"
Naman gaban goshinsa shi kadai ke harhadewa yana kallon matarsa yana sake jimke hannunsa dan daidaita yannayinsa da tunanin abinda ya zamto abin hangensa daga nesa
Me? Tana nufin y'ar matar Bafadensa ta fi uwarta haduwa? Lalle idan hakane kamaninta sun isa , sai dai nasabarta! Idan kuwa ya iya boye maganar wanda ya ba UMUGHLUK ITIFAL har ya auri baiwa ya rama kaskantar da shi da yaron ke yi ,
Wani murmushi ne ya kwace masa, murmushin da ya saka ginbiya sake sakin ajiyar zuciya boyayiya dan samun nutsuwar da ta gaza samu tun jiya, a hankali ta mike ta shige ciki dan shiga bayi kafin su kama hanya, domin wani abu ya rike mata kirji sai ta kakaro shi ko zata ji sanyi sanyi kar ta kumbura a hanya
Tana shiga Umma ta dubeshi da duba irin waanda idan bakinta da kumsashiyar magana sai ta yita take jin sauki ta ce" Wani irin yarda ka yiwa uwar wace kake son hada wannan abin da ita?"
Sarki ya gyara zamansa yana dage kafadunsa ya ce" Ba maganar yarfa bace, su din bayina ne"
"Ka kiyayi lamarin bayi, karamar allura na iya zamewa galma" ta fada tana sake fuskantarsa
Murmushi ya yi yana kada kai ya ce" Ki gane, ba zamu tarbi aradu da kai ba tare da mun yi tunanin abinda ya dace ba, basu da zabi a maganar, haka kuma yarinyar bata da zabi a hukuncin da zamu yanke!"
Kai ya gyada tana jira, har Gimbiya ta fito suka mimike zasu tafi
Rakiya ta masu har bakin mota, a nan ta ga wannan karron Sarki ya ba matarsa umarnin su shiga baya tare da Fadime dan ta yi mata maganar tun a kan hanya, shi fa a yanzu yake da bukatar a yi a gama da wannan yaron ko fili zai zamto nasa!
A lokacin da Gimbiya zata shige Umma ta yi saurin rike hannunta tana kallonta ta ce" Ki tabata da zabinki, ki daki maganarki da karfi, domin idan baki nuna a kan haka kowa na iya rasa ransa ba zaki ga shirme, ki kula, domin bana cikin lalatacen wasa!"
Hannunta ta fuzge sannan ta daga kafarta ta shige cikin motar Umma ta rufo ta ja baya tana kallonsu har motocinsu biyu suka tafi
Juyowa ta yi ta zubawa masarautar ido, nan idannuwanta suka sauka a kan wata baiwa yarinya wace tale bakuwar baiwa ce a masarautar
Murmushi ta yi domin yarinyar ba dai sannin hannunta ba
Da ido ta mata alamu sannan ta kama hanya ta wuce bangarenta cikin gadara tamkar itace uwa a wajen sarki!