Sashe 15
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A haukace Yar ta budi baki zata sake kurma wani ihun ya dake saka bayan hannu ya kai mata ............
Asalamu alaikum wa rahamatullah 🥰🥰🥰🥰
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```

*https://www.facebook.com/106494781436168/*
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
_FREE BOOK_
*Na*
*SAJIDA NIGER*
🔟
Wani bahagumen duka da bayan hannu ya sauke mata a gefen bakinta wanda ya sakata kusan summa a zaunen da take ta kwala wani ihun ta nemi jirkicewa kasa tana sakin tawul din gana dayansa, domin ji ta yi kamar ranta za'a raba da gangar jikinta
Sake binta ya yi ya maka mata kafarsa ya sake dagawa zai kuma dima mata wani dukkan mahaifiyarta ta rukunkumeshi tana ihu da kuka tana sake rikeshi idannuwanta waje tana fadin" INNALILAHI WA INNA ILAIHI RAJUNE, KASHETA ZAKA YI? KASHETA ZAKA YI?"
Jajayyen idannuwansa ya sauke a kanta, da karfi ya hankadeta itama gefe sannan ya nuno masu yatsarsa gaba dayansu muryarsa a kausashe ya ce" A kan mulkina, ina iya kashetan , ke koda ita daya na malaka idan har sakaken wawan bakikin mai jaza min masifa ya sake furta mata sirrina da hannuna zan shaketa sai na kasheta sannan na saketa!, Ke ba sakarya bace? Ke ba mahaukaciya bace? To ki sani wahalar sai dai ta kare a kanki, ba dai ni kadai ba, wato ke baki iyawa bakinki ko? Jira kike na zo na fada maki sirri ki bazani ko? Sai dai mu lalace baki dayanmu dan na rantse maki da Allah tare zamu rufta!, Kin sakata a gaba dama har na koma na dawo na san sakaran son da kike mata komai na iya faruwa, ki saurareni da kyau, walahi, walahi bilahilazi ki iya da ita, ki san yadda zaki yi da ita, a gobe gobe zamu sauka a garin AGADAZ mu kai maganar nan, kuma ta zaunu idan har kika yarda wani abin ya bilo daga ke har ita kunna jan numfashi ta bakinku kunna kallona sai na kashe ku!, Har kiyama zan aika ku!, Kin ji na rantse maki, sha sha sha, bakinta ya saki ya fadi wani abin....zaku kwashi kashinku a hannunku walahil azim!"
Ga mamakinsu, ga baban mamakinsu, idannuwanta ta dago tarr ta saka dubanta a cikin na mahaifinta, duda idannuwanta sun rine sun yi wani irin ja sanadiyar marin da ta sha ta budi bakinta tana kallonsa ido cikin ido ta ce" ABA, kan nufin idan ban yarda aka aura min mutumen da ka fi tsana a duniya ba sai ka kasheni?"
Babanta ya gyada kansa yana sake tabatar mata
Wani irin murmushi ta yi mai tsauri ta taka tna daura tawul dinta ta nufi wajen bayi, sai da ta kama bayin ta rike kofar tana kallonsu ta ce" Lalle kuwa da ka jima baka kasheni ba, domin na rantse maka da Allah ba zan auri Sarki ba, bana cikin tsarin wahalarku ku duka, ba zaku sakani a ciki ba, idn kuwa ka nace ka aura min din ka gani, dukkan abinda kake tunanin ban sani ba na sani kuma ba uwata ta sanar min ba!, Kar ka manta da ni kake yawo?"
Bam ta shige ta mako kofar tana dingishi
Wani irin kukan kura ya yi ta karasa ya ringa jijiga kofar yana fadin ta bude masa,ama firrr ta ki budewar
Juyowa wajen mamanta da ta yi mutuwr tsaye tana kallon taurin kan da yarsu ta yi irin na ubanta ya ce" Lalle yarki bata sanni ba, ama ina mai tabatar maki zata sanni kwana kusa in sha Allah, ki tabatar kin sameni a falona!"
Fuuuuu ya juya ya bar dakin, ya fice yana sake kallon FADIME dake rabe cen kanta sade, da sauri ta daga kafarta dan ta bishi sai dai ganin kamar ya juyo yana kallon Fadime sai ta tsaya tana sake kallonsa
Har ya wuce Fadime din ya dawo ya tsaya , a kausashe ya ce" Ina fata halinki na rashin saka kanki a inda bai shafeki ba yana nan?"
A tsorace ta dago ta dan dube shi, sai kuma ta sake sada kanta tana gyada kanta
Huci ya sauke ya juya ya wuce a falon gaba daya
Ita kuwa Gimbiya dake tsaye tana kallon Fadime juyawa ta yi ta koma dakin wajen Bahija
Bayi ta nemi zarcewa, sai dai abin mamaki sai ta ga Bahujar a saman gadonta a dukunkunne tana rawar sanyu
Da sauri ta karasa saman gadon da Bahija take dukunkunne tana rawar dari ta hau ta kuma talabota tana kallonta a tsorace da halin da ta nuna ta ce" Bahija? Abanki yau kika kalla kika yiwa wannan furuci? Bahija Abanki?"
Bahija ta dake fashewa da kula tana mayar da kanta saman cinyar uwar
Mamanta ta ce" Bahija, ki yi shiru haka kin ji? Ki yi shiru Bahija kin fa san idan ran mahaifinki ya bace babu abinda baya fada, ransa ne kawai a bace kin ji? Ama kuma wannan abu da kika yi ya tsoratar da ni, Bahija abanki ne fa, kin fi kowa sannin irin soyayar da yake yi maki, dan yau ya nuna yana so ki masa wannan yar alfarma ta takaitacen lokaci dan kema ki karra samun kwonciyar hankali a rayuwa sai ki kiya? Ina cewa abin alfaharinki ne ko cikin kawayenki a ga waye mijinki, ina cewa sai kin fi kowa farin cikin wannan hadi fa Bahija?"
Bahija ta dago rinanun idannuwanta tana kallon mamanta, a hankali ta budi bakinta muryarta a shake sosai ta ce " Mama, ransa a bace? Na masa alfarma? Kennan ni na kashe kaina ko? Ai alfarmar da zan masa shine na bijirewa auren nan, Mama ni fa ban damu ba, da gaske ko da wasa yake duka ba sunne a gabana ba, abinda na sani shine ba zan taba yarda da auren wani da ba wanda na gani a cikin jirgi muka yi hotel daya da shi ba, mama kina maganar kece raini, akoy wace zata fito da mijinta na fito da nawa a cikinsu ta isa daga kai? Mama kyan, ajin, kudin , hutun, tsarin, ilimin ya fi su walahi, Mama bara na karasa maki magana domin Allah, ni fa ba zan auri Sarki ba, ga wanda nake so zan nemo shi ko a ina yake, zan kuma kawo shi gidan nan a aura min, idan ba haka ba kafin ya kashenin sai na tona waye shi kuma na kashe kaina da kaina, ni fa a kan wannan mutumen ba mutuwar nake tsoro ba, tsoron rasa shi ya fi mutuwar karfi! Ba zaku fahimci me nake ji a zuciyata ba? Taba kirjina ki ji? Ko menene na hadu da shi mai zafi ne, kuma ina shirye da samama kaina shi ko ta aure ko ta wanin aure, ni dai sai na raba wannan mutun da kowa ya zama nawa ni kadai!"
Tabas mahaifiyarta bata taba haduwa da tashin hankali irin na wannan rana ba, kanta ya coshe, ta rasa me zata tuna , ta rasa wani irin tunani ya dace ta yi, gaba daya hankalinta a tashe yake
Da kyar ta ringa rarashin yar tana fada mata ta fauna maganar zata kashe kanta, mahaifintama ransa ne a bace, ita kuwa ta tsaya a kan bakanta bata da niyar ja baya, a kan mutumen da ta hadu da shi tana iya yin fito na fito da mahaifinta! UMUGHLUK ITIFAL kuwa su da shi, ba zata taba aurensa ba, ita inama zata iya zaman aure da mutumen da kowa ke tsoro, mahaifinta kansa tsoronsa yake yi kamar ya mutu, ama ita zai mikata ko? Aa walahi ta san ciwon kanta idan kowa bai san mata ba
Da kyar ta rarasheta ta sha maganinta sannan ta rufo mata dakin t tafi da ky din da kanta dan ba zata bari ba aje ya dawo su halaka junna, tana so mijinta ya gane idan me y'arsa ta zama halinsa ne kuma shi ya kaita ya nuna mata, a yanzu bashida kaico walahi!
Wajen fa FADIME ke zaune ta karasa ta tsaya rana karra kalle mata kallo
Ta sani sarai, a duniya idna akoy matar da mijinta ke rakawa da ido wannan matar ce, ko me yake yi idan ta zo waje sai ya dakatar ya bita da ido, koda bai fada ba ita ta dade da sannin begen Fadime ya cika zuciyar mijinta, shi yasa take kafa kafa sam bata wasa da sakacin da zai saka UMUGHLUK ITIFAL jin labari ya kashe mata miji a kan baiwa!
A kausashe ta ce" Kina iya tafiya "
Ajiyar zuciya Fadime ta sauke ta mike tana sake dan dukawa ta ce" Allah ya tashe mu lafiya Ranki ya dade"
Gimbiya ta tabe bakinta ta rakata da muguwar harara har ta fice tana tafiyarta cikin sanyin hali
A nutse take tafia, duda dare ya yi ama da fitilu haka kuma da mutane dake yan shagulgulansu jifa jifa
Tana karasowa bangarensu ta kunna tocila domin a nan din akoy duhu , haka kuma a zuciyarta sai Adu'ar tsari take yi
Da sauri ta dakata da tafiyar a haskawar farko sakamakon kan fuskar mutun da ta haska
Sai da ta sake haskawa ta zuba mata ido da mamaki muryarta kasa kasa ta ce" Kamar INDI?"
NADIRAH ta turo baƙi tana sake shagwabe fuskarta sai soshe soshe rake yi
Hindu ce ta fito tana fadin" Dan karbi wannan shafa mu gani? Haba tar autana ki bari mu musu kwana daya jal sai mu tafiyarmu kin ji?"
Da takaici Fadime ta ja dan tsaki ta karasa tana janyo tabarmar kaba ta yada masu a nan tana amsa gaisuwar Hindu dake mata marhaba da gaisar da ita a mutunce tana murmushi
Fadime ta ce" kun ci abinci kuwa?"
Hindu ta ce" Aa so nake na lalabata, kin san ita daga mun sako kafarmu masarautar nan sai tace ita ranta baci yake, kaikayi masarauta ke sakata, ita ji take kamar ta je ta mari Gimbiya, shine nake mata yan turarw turare kar aje iskarsu ce bata hadu ba"
Kwaryar da Inna ta dauko da ludayi dan dama masu furar da ta tarar mijinta ya kawo mai yawa ta dan dakata ta kalle su daga ita har innar tata