← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 99

Sashe 61

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaunawa ta yi cike da isa ta gaishe da Sheikh bayan ta gaishe da ASADEEK tana cire kanta a barin SHEIK din
Kwata kwata a duniyarta ta tsani wannan malamin walahi, mutun ne shi mai shegiyar akida da dan banza iya yi wai shi SHEIK, ta yi kisar, ta bi ta kasan kasar dan ta hadasa masu fitina har ya kore shi ama ya gagara, akoy lokacin da ta so kakaba masa sharin zina karshe ya aure matar ta zama sirri a gareshi, idan ta shigo wajen da yake gaba daya sai ta ji ta tsatsamta da shi, kwata kwata ta tsane shi walahi, wannan fa shine mai yin shahada idan za'a kashe mai aikata laifi irin nata, shine mai jawo masa ayoyi kala kala yana bashi fasara shi kuma yana zartarwa

A dan gagauce ta sanar da adadin kudin da take da muradi saboda kicin , domin kiri kiri HUZNAH ta nuna ta amshi kicin din MAI MARTABA, shine ya sanarwa Umma idan tana sha'awar girki bayan na HUZNAr da dayar matar, tana iya fadin dukkan bukatarta a je a siyo ko kuma ta yanke adadin kudin da take da bukata ta bude kicin din bangarenta, dalilin zuwanta kennan har ta biyo masa da rubutun da ta saka ake yi masa na malaka ne wanda cijn ttsafe tsafenta ne dan ta malakeshi tsaf

Mikewa ta yi da shek din kudin dake hannunta cike da gadara ana yiwa SHEIK tunkaho ta juya zata tafi, sai kuma ta dawo da kula kula ta ce" Yarona, gaba daya yau sai nake gannin kamar kana cikin farin ciki mai yawa? Ko nice ke tunanin haka?"

Murmushi ya yi yana sasauta rawaninsa a hankali ya furta" Alhamdulilah Umma"

Sake zuba masa ido ta yi, sai kuma ta ce" Allah ya karra kawo abinda zai kawata fuskarta da murmushi na farin ciki irin wannan"

Murmushi SHEIK ya yi bayanane yana gyara zamansa sannan suka amsa su biyun a nutse,

Wani kallo boyaye ta sakarwa SHEIK, sai kuma ta fice tana ji kamar ta dawo ta tambaye shi to me ya saka shi farin ciki haka? Sannan ta tambayi Sheik shi kuwa murmushin da ya yi na meye?

SHEIK ya ce" Ina fata ka fahimci alkiblata?"

Asadeek ya tabe bakinsa yana gyara zamansa a nutse sannan cike da fitar da harufa a tausashe ya ce" Ban san dalilin da ya saka kake karra nanata maganar nan cewa ta zama sirri ba, duda abu ne da ba zan falaso shi doron duniya ba domin sirrina ne, ama kuma abu ne da ya dace ace na wuni ina sukuwa a saman doki a garin nan a wunin yau baki daya dan nuna tsantsar farin ciki da samun yanci, ya dace ace an wuni ana sadaka a bayane ba a boye ba,.....SHEIK ka san na rasa me ya dace ace na kaamanta mata a matsayin karamawa?"

SHEIK ya yi yar daria ya ce" Kyauta?"

Asadeek ya dan gyada kansa kadan yana cijewa kadan dan yau gaba daya SHEIK bai barshi ya huta ba

SHEIK ya ce" To ama, idan aka yi kyauta abin ba zai yadu a fada ba?"

ASADEEK ya koma ya jingina, cike da tarin lamari irin na sarautar dake yawo a jinninsa, cike da basarwa tamkar ba zai yi magana ba, ya sake bude bakinsa ya ce " Gaba daya ban ga wanene ya dace mu ji tsoro ko shakun ya ji ba, "

Ya dan saurara yana shafa daidai kirjinsa yana jin wani irin yar yar yar a dukkan gabobin jikinsa sakamakon tuno lamarin yarinyar da ya yi, subahanalah wani irun daukaken abu ke ratsa shi ba ji ba gani, a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya dora da fadin" Du yadda zaka yi, kana da dama, abu daya ne na sani shine ta cencenci karamawa domin koda kowace mace nada damar yantani ita ta kai ga ci,, Ban sani ba, ita din makashina ce, ko mai tona asirina ce? Koma mecece ita na san tana da baban matsayin da ba kowace ta samu ba, shine zamtowa sirrina, sauran maganar kuma a hannunka ne in sha Allah " yana kaiwa karshe ya mike ya nufi sama dan gaba daya a yanzu sai ya ji yana son tsayuwa a gaban gadon da ya turmusana daren jiya

Da kallo SHEIK ya rakashi sannan ya maido dubansa saman cafet yana tunanin me ya dace ya yi, idan ya tuna ba ita bace ainahin Bahija yakan ji tsoro a kasan zuciyarsa, ama yana fadawa Allah ya haska masu lamarin sannan ya kare su da boyayen rikicin dake iya jigata UMUGHLUK ITIBEL

Har zai fita ya dawo a hankali ya zubawa gorar nan ido , a nutse ya duka ya dauka ya sake zuba mata ido, sai kawai ya mike ya yi gaba da ita yana dan jujuyata a hannunsa

Ficewa ya yi ya nufi gidansa dan Matarsa ta fita, ta je maza maza ta hado abinda ya dace, yana tafe yana ta tsara dukkan abinda ya dace din

Daga cen masalaci ya koma ya ja sallar Magariba sannan suka shiga karatu har isha'i ta yi suka gabatar sannan ya koma ya daukota da kansa ya kuma shige falo yana bada umarnin kar wace ta shigo yau UMUGHLUK ITIBEL zai kwonta barci da wuri

_________________________________

A falo take a zaune, dadadan turaran wutar da ya gama dakin yana ta fitar da kanshi, gefenta kuwa danyar madarar shanu ce dauke da maganin zahi in ji innarta, ama ta ki sha tana dai kallon TV bakinta a cune tamkar za'a saka masa ribom , ga dukkan alamu a sama take, rigima take ji,jifa jifa kuma sai ta makawa madarar harara ta dauke kai

Hindu na murmushi ta karaso hannunta dauke da abin shayi ta ce" Aa, yaya baki sha madarar ba indina?"

Madarar ta sake kallo, haka kawai wannan maganin zahi da innarta ke bata ya fara saka mata tunani kala daban a ranta, to wai zahin mema? Kai ina ba zata sha ba, ta yiwu harda gudunmuwarsa wajen neman kasarata da wancen sadaukin ya yi!

Shayin ta amsa ta shiga dan kurba bata cewa innarta komai ba, dan gana daya sake nanata hirarsu take yi a cen kasan zuciyarta tana ji anya zata iya kuwa? Baban burinta ta ganta a gefen iyayenta da innarta sunna rayuwarsu a gefe hankali kwonce

Innarta kuwa dan murmushi ta yi boyaye tana godiya da Allah da yarta ta sha shayin, uhum NADIRAH kennan a tunaninta a shayin ba komai, bata san shi ya fi daukan abinda zai rikitata ba,da zarar namiji ya tabata kuwa, domin kakarfan maganin tayar da sha'awa ne a cikinsa ama wanda sai an tabata dole sha'awar ko zata tashi, dan kuwa haka kawai ba zai motsata ba

Kafarta take dan kadawa tana kallon allon TVn dake karra bata mamaki, TV bango guda jama'a

Sukur sukur da kaya alamun ana shigowa ta doguwar biyayiyar hanyar nan ya saka su zubawa hanyar ido su dukansu

Bayanuwar matar SHEIK dauke da akwati mai dan girda da kuma karama ya saka Inna mikewa tana yi mata barka da zuwa ta tayata janyo akwatunnan har suka karaso falon suka ajiye sannan matar SHEIK ta duka har kasa cike da girmamawa tana tasbihi ga ubangijin da ya halici wannan halita, watau NADIRAH zaune take da yar riga marar nauyi ta kuma daure gashinta a tsakiyar kanta

A tausashe ta furta" Barka da hutawa Gimbiya, Barka da wannan lokaci, Yaya karfin jiki? Ina fata da sauki?"

Innarta ta saki murmushi da kafarta ta zunguri NADIRAH dake daf da kafar tata tana fadin" Amsata mana"

NADIRAH ta girgiza kanta tana sada kanta kasa dan bata san amsar da zata ba mace mai daraja irin wannan da ta duka tana gaisheta ba

Inna ta ce" Tashi mana hajia ki hau sama mana wanna fa kamar ta hadiyi kwado yau, maganar sam bata fitowa daga bakin"

Da sauri Matar SHEIK ta girgiza kanta tana fadin" Aa, aa hajia, ba zan iya hawa sama ba, ai idan tana kasa babu wani dake iya hawa sama sai UMUGHLUK ITIBEL "

Inna ta dan zarro ido ta ce" To fah Au au au haka abin yake? To bara na diro nima, ke dan kauce kadan na zauna....." Ta sauko din tana dungure kafadar NADIRAH dake sake zumburl bakinta a ranta tana ayana yanzu Innata du wajen nan bai isheki zama ba sai a nan

Murmushi Matar SHEIK ta yi, gaba daya yannayinsu sai yake birgeta, har jin abin take a cen ranta

A nutse ta gabatar masu da sha tara ta arziki, watau galeliyar alkyaba irin ta manyan matan sarakai da suka amshi sunnansu, sai sarkoki uku na zinari manya da awarwaraye, sai takardun tagwayen gida fa kys din motocin dake cikinsu su biyu
A nutse ta furta magana kamar haka" Sako ne daga UMUGHLUK ITIBEL, an ce na gano yaya saukin jiki, sannan na sanar idan ba damuwa gimbiya ta je bangarensa

Ido NADIRAH ta zarro ta maida dubanta kan innarta wace karara farin cikin kayan nan suka bayana a fuskarta har kamar ta bushe da daria take yi

Baki ta turo ta mika hannu ta dauko dan tuntum din kujerun mai kyau ta yar ta kwonta tana juya masu baya ba tare da tace uffan ba a ranta ta sake ayana' Sai ku daukeni ku kaini na gani'

Da mamaki su dukansu suke kallonta

Innarta ta sauke ajiyar zuciya tana duban Matar SHEIK ta ce "

🧐🧐🧐🧐🧐🧐

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

4️⃣3️⃣

Tana sakin murmushi ta ce" Ki yi hakuri dan Allah, yarinta ce"

Ajiyar zuciya ta sauke tana sake duban NADIRAH
Muryarta ce ta nuna alamun abinda take son fadi daga zuciyarta zai fito
A sanyaye ta ce" Dan Allah, ki yi hakuri idan har abinda zan fada zai bata maki, sannan ban sani ba ko hakan ba daidai bane?, Abinda na sani shine dubanmu hakan shine a zuciyarmu, kuma a bakinmuma haka ne"
Chapter 61 · 0% Book details