← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 99

Sashe 59

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Innalilahi wa inna ilaihi rajune, wayo na shiga uku kin ga, ki yiwa huwa rahamanu kar ki sanarwa Innata maganar nan, wayo Allahna bayan cin amanar kuma yamadidi ASADEEK zai yi da ni a duniya? Oh ni jikar mutun hudu na ga rana" NADIRAH ta karashe tana riko hannun LUBNA wace ta kusan zurmawa da gudu da ta ji sunnan da ta kama da kukan da take yi

NADIRAH ta dora da fadin" Amanatul amana maganar nan, kuma abinda kika fada da yaren ko shima dai maganar wannan din dai ne?"

A hankali LUBNA ta shiga tuna kiran da ya samu SHEIK a lokacin da suke zaune shekaran jiya da dare , kasancewar wayarsa ba wani rikaken sirri ne da ita ba, domun sun sha fada masa idan zai yi maganar sirri a cikin mutane ya ringa fita, wayarsa tanada amsa amo mai dan karfin da mutun mai kaifin ji zai iya jiyo hirarsa,
Maganar da ta san ta ji daya ce kafin da hannu SHEIK ya mata alamun ta bashi waje, watau *WACECE SUKA AURA MIN?*

Sake zubawa NADIRAH ido ta yi, a hankali ta koma ta zauna tana tunani da kuma ba kanta amsa
A nutse ta sauke ajiyar zuciya tana sake duban NADIRAH
Bata jin French, bata son a san baban abinda kowace mace zata iya yin tinkaho ace itace ta wayi gari a haka, kuma ta kama sunnan UMUGHLUK ITIBEL

Ajiyar zuciya ta sake saukewa, a nutse ta yakice tunanin nan, tana karra tanatarwa kanta cewa babu ruwanta a wannan lamari, dan haka sai shiga assuring din NADIRAH, cewa babu wanda zai sani, ai sirrin likita da marar lafiya tsakanin patient da docter ne, sannan ta sake bata hankalinta gaba daya tana sake kwatanta mata girma da darajar abinda ta kawo da kuma maganar dubata, a kalla sun dauki awa ana abu guda, daga karshe ta yarda ama sallar da bata yi ba sai da ta yita kusan sha biyun rana tana ayana ba laifinta bane na maci amana ne, sannan ta zauna gaba daya hankalinta ba wani a jikinta ba, jikinta du ba a sake ba da kyar da walahauli ta iya bude jikinta LUBNA ta dubata

Da tausayawa take yi mata bayani kamar Haka" Alhamdulilah baki yi kariwar da sai an maki dinki ba, sai dai kin yi mugun jin jiki ta yadda sai kina shafa maganin da za'a kawo maki sannan kina hadiye na hadiyar, domin wajen daga ciki ya kumburo hakama daga fatar gefe da gefe sannan kin dan karru kadan ba sai an dinke wajen ba, ki samu isashen hutu sannan ku ringa anfani da ruwan dumi kina zama a ciki kin fahimta?"

NADIRAH taa gyada kanta kasa kasa ta ce" Ama dan Allah idan an kawo maganin a yi dabara kar innata ta gane"

Murmushi kawai LUBNA ta yi , sai kuma ta dauki hijabinta da nikaf dinta ta mayar tana gyara kayanta ta ce" Barana na koma da kaina na amso na kawo maki"

Itama ta ji dadin haka , dan haka ta kilacewa LUBNA kayanta a cen cikin adaka ta juyo tana tafiya a hankali sai ga Innarta ta sake faduwa hannunta dauke da kwano yana tururi , watau hanji ne aka rababaka ya samu dahuwa mai daraja yana ta kanshi da tururi

Direwa ta yi a gabanta tana fadim" Yi maza rarabakeshi da zafi zafinsa zai fi warware maki yan hanji, yauwana bayin cen akoy irin bahon bayina na wanka ko? Ko sai na dauko katuwar roba?"

Naman ta dauka, domin yinwa take ji sosai , saima da ta ganshi ta ji yinwar ta sake sheda kanta ta janyo ta yi bismillah ta fara motsa shi tana kallon miyar da tunanin dama ace ta samu nono ne, da ta morw walahi, ama abin nan idan ka ci ai nauyi zai maka a cikinka sosai

Innarta kuwa bata tsaya kulata ba ta shige tana dudubawa

Jim kadan ta fito tana kama haba ta ce" Ke bayinki ta fi tawa girma ko me yasa?"

Nadirah ta dage kafada tana raunar hanta tana kallon Innarta

Wucewa Hindu ta yi ta fice a dakin ya koma kicin dan ruwan zafi ta dora tana gadin ruwan tana dariyar Auntunta, wai daga sanar mata abu sai kawai ta katse kira ta labe🤣🤣🤣, gaba dayama ta ki yarda su yi maganar wai kunya, yo ita yau ai shagali nata walahi, abu ya fara kankama sunna shawara da matar SHEIK? Uhum,

Ruwan na fara tafarfasa ta juye a katon bokici ta kinkima ta koma dakin ta wuce ta yi tsaye tana ta tunanin yadda zata tara ruwa a abin nan kamar yadda matar SHEIK tace

Kai kawai fitowa ta yi ta koma ta dauko katuwar roba ta kai bayin ta zube ruwan ta sirka shi, ama fa da zafinsa walahi sannan ta fito ta yi tsaye kan yar cewar ta taso maza ta je ta shiga ruwa ta tara mata
A wannanma sai da aka yi da gaske, sai da HINDU ta dage sannan Indi ta tafi, haka kuma wajen shiga ruwan da kyar ta iya zama domin ya mata zafi kuma Innarta tace walahi tana sauraronta idan ta karra ruwa zata shigo ta zaunar da ita
Ziciyarta na mata suya, tana cike da tsoron shikenan, kennan Innarta ta sani? A haka ta yi ta gama ta fito da jalabiyar tasa tana kallon rigar da Innarta ta ajiye mata ta dha turare

Hanci kawai take ja ta saka rigar ta haye saman gadon jikinta da zafi zafi tana sauke ajiyar zuciya

Bata jima ba Matar Sheikh ta dawo da maganin innarta kuwa na biye da ita a baya dauke da jarka irin katuwar nan yelow tana murmushi ta ce" Ga nono Indi an turo maki "

Ido NADIRAH ta zubawa nonon, innarta ta ajiye ta fita dan dauko abin zubawa

A hankali Nadirah ta ce" Waye ya bada wannan nonon?"

Lubna dake balo mata maganin ta ce" Daga bangaren UMUGHLUK ITIBEL ne aka kawo"

Baki ta tabe bata ce komai ba, ita kuma ta bata na hadiyar ta sha da kyar sannan ta bara mata na shafawar ta tafi ta shafa da kanta tana sake jin kamar duniyar tai mata zafi ita kam, kamar duniyar gaba daya zata kifun mata ne haka take ji

Dawowar innarta ya sakata barkewa da kuka , tana jin barci na fuzgarta ama ta riga ta faka garin rigima tana kallon Innarta dake zama tana sallalami da tambayar meye kuma ta ce" Inna, walahu ba zan iya karasa aikin nan ba, ba zan iya ba, gida nake so, innata gida nake s............

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

'4️⃣1️⃣

Da sauri innarta ta zauna tana ajiye abinda yake hannunta tana furta" Subahanalah subahanalah subahanalah, Indi gida kuma? Mun gama abinda ya kawo mu ne?"

NADIRAH ta kwontar da kanta saman cinyar innarta tana wani hakin kukan tana fadin" Ba sai mun gama ba, dan girman Allah ki mayar da ni gida Innata, ba sai mun gama komai ba, kawai Allah zai kare shi, mu bamu isa mu yi masa kariyar komai ba!"

Cikin sigar rarashi innarta ta saake tausasa muryarta ta ce" Ama, me ya yi zafi haka da baa wuta ba?, Kyan alkawari fa cikawa, me yasa mun taso mun zo har mun gano wani abu a zamansa da mutanensa zamu zubar mu tafi? Ai hakan ba daidai bane a tunanina, bamu yiwa kanmu adalci ba bale shi mu yi masa, haba kema Indi, me yake damunki ne wani lokacin sai ki rikice kamar ba ke ba?"

NADIRAH ta lumshe idannuwanta domun kanta har sara mata yake yi, muryarta a cinkushe, barcin nan na fuzgarta sosai ta ce" Ban zo gidan nan dan wannan ba, Innata ban zo dan na lasance kazar cikin daki ba, kyan alatun dake zagaye da gidan nan baya cikin tsarin abinda ke iya sakani ni NADIRAH na ji zan iya zubar da komai da na gina na farin cikin rayuwata a nan ba!, Innata bana jin zan iya rayuwa a wajen dake zagaye da munafukai mafi soyuwa a zukatan masoyansu ba, hasalima irin haka ya saka nake guduwata wajenku, domin ban.........ban..........innata Aminnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnunnnnnnnnnnnnnnannnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnn
........" Sadakawar muryarta, daukewar muyarta, da sakuwar jikinta da fitar numfashinta tamkar na dan jariri ya saka innarta lumshe idannuwanta tana sauke ajiyar zuciya da dauke hannunta daga saman kirjinta a hankali tana dan karra kallon Fuskar NADIRAH

A hankali ta shafa gefen fuskar nata sannan ta mike kadan ta gyara mata kwonciya ta luluba mata abin rufa ta fice jiki babu karfi ta koma baban falo

Tana zuwa falo ta tarar da Umma zaune tana amsa waya kafarta daya kan daya cike da gadarar nan

Har ga Allah sai da ta ji gabanta ya yanke ya fadi, jiki babu karfi ta zauna saman kujera ta samu kanta da zubawa Ummar ido tanna kallonta, kallon nan mai kama da kana karantar mutun, kana son gane wanene shi a fasarar badininsa, irin girman waye shi ne a duniyar da ka ajiyeshi

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana cire dubanta ta dora a kasa
Chapter 59 · 0% Book details