Sashe 96
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A tausashe ya dago yana duban kowa , daya bayan daya
A matukar tausashe da girmamawa ya bada umarnin a daukowa ASADEEK kujera, domin shi dake tsayen nan har juwa ke kwasarsa, ina ga ASADEEK? zuciyarsa ta girgiza ainun, hankalinsa ya matukar tashi, a sanyaye ya kai dubansa kan Bafan ASADEEK, ya dora kuma kan UMMA, sai ya samu kansa da sada kansa a hankali yana furta" Innalilahi wa inna ilaihi rajune........" Ya yi haka ya fi a irga sannan ya dago ya fara magana a hankali, sai kuma salon maganar ta dauki zafi, har ya zamana ya dane takardar da hannunsa na hagu yana bayani a kan girma da darajar zumunci, tamkar zai kife abin ya je ya kikifawa masu laifin nan mari, da irin girman amana da laifin wanda ya ci ta!
Sannan ya dawo wajen da muryarsa ta yi rauni ainun, laifin kisa, ya kuma gangaro kan aiki mai muni irin na zina da LUWADI DA MADIGO....., Karshe dai dole muryarsa ta ringa rawa har sai da ya sada kansa ya dauki tissu din da aka bashi yana dan share hawayen da suka gangaro masa, sannan ya dago a kausashe yana duban jama'ar dake wajen ya ce" Dole zamu zartar da hukunci daidai yadda adinin musulunci ya tanadar, domin tun kafin a kawo zamanin hukunci na gwamnati ake yin na shara'ar musulunci, mun yarda cewa babu makawa sai mun mutu, idan mun mutuwa kuwa zamu tsaya a gaban wanda ya halicemu, sanadiyar wannan na tsaya a yau a gabanku sannan ina mai rantsuwa da wanda raina yake hannunsa, babu wanda za'a cuta mu ji mu kyale dan yana dan uwanmu, mahaifiyarmu, mahaifinmu, matarmu, yayunmu, kannenmu, aminanmu, ko wani mai fada a ji mu tauye hakin wanda aka cutar saboda shi ba, domin mun san cewa akoy ranr da zamu mutu, mu yi kwonciyar kabari, mu kuma tashi gaban wanda ya halicemu, ya umarcemu da mu yi adalci babu wanda zai saka mu a uku ya lalata mana kiyamarmu ko wanene!"
Gaba daya sai da wajen ya dauki muryarsa, hakan ya sa aka karra rikicewa, bama masu laifin da danginsu
Takardar ya janyo ya sake budewa
A kausashe ya ce" SHARA'AR da UMUGHLUK ITIBEL ya gabatar shekaru bakwai da suka shige na dan gimbiyar Tanut, aka wati gari basa nan, yanzu an same su, shara'ar da ya zartar zamu zartar da ita a nan a yau, a kuma yanzu! Ita kuma da ta take mana doka ta dauke shi ta gudu da shi alkali ya yanke mata hukuncin kaso na tsayin shekara biyar a gidan yari dan horonta da kuma horon masu hali irin nata kan kiyayewa da yi mana haye a kan lamarin shara'ar, idan da mai magana bismillah muna da minti biyar ana iya ja da haka ama babu maganar daukaka shara'ar domin tsohon hukunci ne da aka yarda da shi, bisa laifinsa na haikewa matar dan uwansa ya yi mata fyade ya kuma kasheta!"
Shiru ne wajen ya sake dauka, sai kukan gimbiya da ya cika waje tana kallon wajen da mijinta ke hakimce, wanda ya dauke kansa ya mayar wani wajen, domin ba zai taba cewa koda A bane a kan hali irin nata, ya yi mata uzuri na farko, ya yafe mata na biyu a yanzu kuma ta yi abinda babu huruminsa a ciki, tabas gaskiyar mai damagaram ne, ko me suka shuka fa zasu je su girbe shi ne, idan suka yarda wani ya lalata masu goben su me suka ci riba kennan? Allah ya sa hukuncin nan ya zamo sanadiyar yafewarsu a wajen ubangijinsu, sannan ya zamo ishara ga sauran al'umma
Lokacin da ya dauka na shigewa ya sake bude takardar ya sake dagowa ya Kalli ASADEEK, ga kujerar nan an kawo masa ama ya kasa zama, a tsaye yake hannunsa daya a bayansa a jimke, dayan kuwa a saman sandarsa yana kallon mai Damagaram din shima
Da ido ya masa alamun ya zauna mana?, Shima da idannuwansa ya lulumshe masa sannan ya dan girgiza kansa
Numfashi ya ja ya sake daukan magana kamar haka" Muna da kara, shigowar kara, ta bawan Allah, wanda aka cutar, ya rubuto kara da kuma hujojinsa a bayane, WA'INDA idan wa'inda ake kararsu sunna da musu a kan haka sunna iya yin magana a kowani irin lokaci su musa, sai dai su sani munna dauke da vidios, da kuma recoding muryoyinsu wa'inda ke tafe da tabacin karar mu, in sha Allah zamu fara daga kan Laure sannan mu karasa da Asaraki"
NADIRAH da jikinta ke rawa, zufa na keto mata ta kalli Auta, muryarta na rawa ainun ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi rajune, kar ya fadi Auta, dan Allah a zaunar da shi, ban san in har zai iya jurewa ba, yana yi kamar ba komai ama ki dubi yannayinsa , Auta ki dubi yannayinsa......"
Sai kuma ta kalli Huznah, a rikicenta ta ce_ Aunty, ki saka mijinki ya zauna, dan Allah ki dauki maganana da mahinmanci, ki kuma yafe min abubuwan da na ringa yi maki, ban maki su dan na wulakantaki ko dan na nuna maki iyakarki ba, hasalima ni din ba kowa bace face wace nima kadara ta biyo ta kaina, ban zo rayuwarki dan na tarwatsa maki farin ciki ba, ki sani na shigo ta rayuwarki ne dan Allah ya kadarta min, Aunty na ringa yi maki abubuwan nan ne dan ina maki hannunka mai sanda, dan ki farka daga irin mu'amalarki da mijinki ki karra kusanta kanki da shi, ama a yanzu ba zan iya jurar gannin wani abu ya same shi ba, idan har aka shige shara'ar cen komai na iya samunsa, Aunty ina iya mutuwa a kan damuwarsa....." Ta idasa kuka mai tsuma zuciya na balewa daga bakinta, wanda du yadfa ta so rike shi sai da gunjinsa ya kawo inda ASADEEK yale tsaye
Idannuwansa dake da nauyi ya daga ya dora a inda suke, a hankali zuciyarsa ta buga da bugu mai tsananin gaske,
A tausashe ya kai dubansa wajen Mai Damagaram, so yake ya ce da shi a shigar da Indi cikin gida,ama ya gaza, domin bakinsa ya masa nauyi sosai
Shi kuwa Mai Damagaram a hankali ya dauke dubansa, domin ba zai yiwu a shigar da ita gidan ba, sai dai a yi hakuri, dole a gabatar da shara'ar tana wajen
HUZNAH kuwa, lokaci daya magangannun suka ringa dukkan kirjinta da hayacinta baki daya
Kukan da NADIRAH ke yi kanta a saman kafadarta ya rikitata har ta rasa me ya dace ta yi
A hankali ta saka hannunta ta tare Auta dake son mikar da Nadirar dan ta wuce da ita ciki, sannan ta dora hannunta a gefen fuskar Nadirah a hankali tana dan shafawa, muryarta a raunane ta ce" Ki nutsu mana, ki daina kuka, ko so kike ki yiwa babynmu ilah ne?, Ki dubi mijinki, a yau ki karra tabatarwa SARKI kike aure, a dole mijinki ya yi hakuri, a dole ya shanye damuwarsa, a dole ya hadiye kowani bugu, a dole ya iya jure koma menene, kin ga dubi mijinki nan yake kallo, ki dago ko hankalinsa zai kwonta mana?, Ki taimaka mu bi shi da addu'a, ita kadai ce abinda yake da bukata daga garemu............"
Hannunta ta saka cikin nata ta jimke, sannan ta maido dubanta idna yake tsayen yana kallonsu
A hankali ya sanyayar da dubansa, sannan ya dawo da hannunsa dake jimke a bayansa ya ware shi ya dora a kirjinsa, sai kuma ya safa kansa gaba daya sannan ya dago ya sake sanyayar da dubansa, kafin ya maida inda Mai Damagaram ya ci gaba da magana
A harzuke, a kuma tausashe, a hasale a kuma garaje Mai damagaram ya ringa fadin laifukan Umma, tun kafin yayan su girma, har ya kawo wajen rasuwar GIMBIYA, ya fadi cewa laifin UMMA shine ta ga lokacin da Asaraki ya zuba guba ya bada aka ba Gimbiya, ta kuma ga lokacin da take fitar rai har ind ata mutu, ta kama y'arta ta kule a daki , wato ta yi shiru tama yi farin cikin haka, dan dama so take a bata waje!
Ya dora da fadin irin azabtar da Auta da ta ringa yi, ta hanyoyi daban daban
Zuwan HUZNAH cikinsu, maganin da ta ba Huznah a cikin lipton wanda ya saka ta samu cuta ta rashin gamsar da mijinta, ake tafe a haka, da irin zaluncin da take gabatarwa a cikin masarautar, da auren Auta, da irin cutar da Auta da ta yi, zuwa neman auta da Madigo, da rabata da gidan mijinta da ta yi, zuwa maganar Aurensa da aka ce za'a bashi yar sarkin Tanut da aurensa da ya juye kan NADIRAH wace aka nunota da irin abinda aka dora mata kan zuwanta fadar, irin sakota a gaban da aka yi, irin gwagwarmayar da ta fuskanta, irin yadda Umma ke kawo mata magungunna ne menene burinta daya ne dai a kashe wannan bawan Allah da yake tsaye a kan dukkan uzuririkanta, yake kiranta da sunna mai daraja, yake yi mata biyaya, ta makantar da shi da matsalolin cikin gidansa, tana neman ransa ido rufe, bata duba halaci, adalci , amana da suka yi zama tun tana baiwa irin ta siye, ta dawo ta zama babar hadimar gimbiya, karshe ta zama UMMA a wajen MARIYA da ASADEEK , ta take ta murje ta lalata ya'yan mutane da yawa ta hanyar sako su a aikin madigo, sannan ta zamto ta hannun damar Asaraki..........,
A rikice HUZNAH ta kalli NADIRAH dake kallon ASADEEK
A rikice ta ce" Dama abinfa kike son na gani kennan na kasa gani?"