Sashe 11
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idannuwanta sun gama rufewa, neman binsu take yi a lokacin ne mace yar uwarta cikin shiga harda nikaf da safar hannun ta tareta tana mai yi mata salama da fara kwatanta mata da tambayarta bata basu dakin da ta dauka ba kuma tana neman shiga lft
Ido ta ringa zarrowa, hankalinta na neman tashi
Ta san a nan kasar da ta sauko darajarta daya da baiwarta
Babu wanda zata yiwa tinkaho ko isa, hasalima ba kowani balarabe yale mu'amalantar bak'ar fata da mu'amala mai kyau ba, duda ita din fara ce kal , ama kuma bakinta baya dauke da larabcin da matar nan ta yi mata
A hankali ta ce" S'il vous plaît pouvez vous m'expliquer en français ? Je ne comprends pas très bien l'arabe " ( Dan Allah ko zaki kwatanta min da french, domin bana fahimtar larabci da kyau)
Matar ta dan yatsina fuska ta juya ta koma ta fada a cen cewa matar cen freinch kawai take ji, dan haka aka turo mata wanda ke jin freinch
A nan ya fada mata komai cikin nutsuwa
A sanyaye ta ce" Kennan idan har mutun mai dauki daki tun daga gidansa ba, ba zai iya samu ba?"
A tausashe ya ce" Gaskiya da wahala, ama bara na tambaya idan har akoy dakin da ba'a kama ba sai ki kama"
Tana tsaye ana ta aiki da computer, kwararun ma'aikatan sunna ta aikinsu
Wata mata da ta kama wani daki ta ce kawarta ta kamama suka sake tabowa, nan ta sheda masu kawar tata tace bata san dakin a wani hotel bravia zata sauka, dan haka sai suka cenza sunnan suka bata dakin sunna yi mata bayani kamar haka" Zaki ji dadin Hotel Nozol royal, domin a wannan waje akoy tsafta, akoy restaurant, sannan tsakaninta da kofar baban masalaci Al-masjid al nabawi tafia ce ta yan mintuna 10, kana yi kana hailala, sunnada gadaje uku, baban gado na Queen royal, da gadaje biyu, sunnada bayi tankameme guda mai dauke da jakuzi, ruwa na shower, WC, da kuma Buta ta karfe, a kulun za'a cenza maka abin shinfida da na rufa koda baka kwonta a sama ba, sunnada kur'anai da abubuwan sallah, idan budurwa ce ke bakida damar kawo maza wajenki, idan matar aure ce ke wanda yake da damar shiga wajenki mijinki ne,kina iya shiga dakin motsa jiki na mata, sannan akoy parking space idan kina iya hayar motar da za'a yi yawo da ke domin bakuwa kike ba zaki yi tuki da kanki a Madina ba, bakida takardar yar kasa, kudin parking din du minti talatin sarl biyar ne ba tsada........."
Ita kam dakin ta shige tana kallonsa ta ce" Na gode"
Kai ya gyada ya yi baya dan ya kula ta gaji ya fice
Da sauri ta cire Alkyabarta da abin wuyanta ta ajiye a nan ta ringa kai kawo farcenta daya a cikin bakinta kanta tamkar zai tarwatse da tunani
A hankali baiwarta ta dan duka ta ce" Allah ya karra maki lafiya, me kike da muradi kafin ki shiga wanka? Sai kin shiga kin fito zaki ci abinci ko kafin ki shiga za......"
"Dan Allah ki barni da maganar abinci da dukkan abinda ya shafe shi, ba kin ga mutumen da muka taho tare ba, ga wannan kudin ki rike idan kin ji yinwa ki nemi abinci ki ci, ki sauka ki samo min wani daki yake, kar ki dawo sai kim samo min kin ji abinda na fada!"
Jiki a sanyaye ta amshi kudin, zuciyarta na bugawa
Wai mutumen da suka biyo wanda ke tare da baban bawan garin AGADAZ? To ita bata ji numbobin dakunnan da suka dauka bane? Ko kuwa?
Har ta juya zata fita sai kuma ta dawo ta sake zubewa a kasa ta sheda mata ai gafa numbobinsu na dakunnansu
Wani irin ajiyar zuciya ta sauke tana jin wani sanyi mai dadi na ratsata
Har ta daga kafarta zata fice, sai kuma ta ja tana kallon jikinta
Muryarta har rawa take ta ce" Ki bude akwatina ki ciro min abayata wace ta fi kyau, ki fitar da turare ki yi mata wanka sannan ki shigo bayi ki cudan bayana....." Haka kawai ta ga ya dace ta dauki wankan da ya dace dan ta leka bawan Allahn cen, ya Allah bata taba jin namiji ya shiga zuciyarta irin na yau ba, ji take kamar zata summa, gaba daya ta manta tabo kawar tata da tace ta sanar mata Hotel din da ta sauka dan tace mata ko ta kama mata daki a Hotel din da suka sauka da mahaifiyarta ko me? Ita kuma ta kiya domin ba zata so ta shiga dakin yaku bayi ba gaskiya, ta so ta je Hotel din da suke sauka sai gata a nan, duda kudin dakin ya bata mamaki tsadarsa haka ta dauki adadin kwanakin da take so ta saka masu kudin.....bata tunanin zata iya barin wancen gayen a yau
Bayan ta shige ne aka sake kira, kawar tata ce, a dole baiwarta ta daga dan idan bata daga din ba tana iya jawa kanta matsala
Da girmamawa ta sheda mata cewa ai a Hotel Nozol royal ne suka sauka
Da mamaki kawar tata ta ce" A wani daki? Nima a nan din nake ai, nan din ne na kama mata ta saka na yi annuler, gani nan zuwa!"
Wannan kennan
______________________________________
Hasken farin watan na yau ya masifar haska lungu fa sako na kauyen LABA
Ga kuma fitilun aci balbal fa suka kunna harda gagan samarin da suke da Uba sanjo ya kasa watau wannan fitila mai shegen hasken tsiya sun kunna sun dage kafa sunna kallon yan matansu na wake ana shewa da tafawa abin gwanin birgewa
Aminu ne ya yi murmushi yana kallon NADIRAH ya ce" Ta Aminu kin tabata yau zaki yi rawa a dandalin nan? Ta Aminu a kanki in ba sai na yi karin hamsin ba ubana goma!"
Fari ta yi da idannuwanta ta kara gyara tsayuwarta ta ce" Aminun Indirah, sha kuruminla ka huta, mu bakwai ne zamu shiga ai yanzu yanzu, dan haka gyara aljihunka, ka dan dai ido a kanmu gaskiya yau ka saki kudi ka ji Aminuna?"
Wani irin murmushi ya yi ya cira kai ya ce" Barama ki ga na karo a wajen Mutaha"
Da ido ta rakashi har ya bacewa ganninta, haka kawai ta samu kanta da sakin yar dariya har tana rufe bakinta a lokacin da ya bacewa ganninta
Yar dubu da ta dawo dan kamota su je su shige rawar ta tsaya kallonta ta ce" Dariyar me kike yi haka ke kuwa?"
Murmushi ta yi tana sake dora daurin zanninta a saman rigarta mai hoto ta ce" Wai ki ji fa Hindu cewa ta yi walahi ifan Aminu na tafia kamar wuyan rakumin jeji, shine yau na ga ya yi gaba wuyan ashe zolo zolo yake biyarsa......" Ta karashe tana sake fashewa fa dariya dan har ga Allah abin ya shamaceta, kai Innarta? Innarta sai ta kasheta wata rana,
Itama dariyar take yi ta girgiza kai ta ce" Ai kuwa ke kin san du kauyen nan babu ya Aminunki a gayu, zo muje dan Allah daga lamratu fa sai ni sai ke a wale, yau Adamu ya zo kallo Allah ya sa ya dubeni"
Binta ta yi suka shige layin yan matan dake wake, kowace idan ta shigo da kalar bajintarta take kada abinda ta san tanada shi ta wake samrayinta ta koma, idan da yan cenjinsa tsaf ,ai shigo ya zuba mata su, idan babu kuwa abinda yake da shi zai yiwa makadin kyauta da shi
Murmushi take yi a lokacin da Yar dubu ta yi wakenta tana kallon wajen Adamu, ama sam sai ya ki shigowa ya mata kari, karshema hala ta kusan gamawa ba'a yi mata ba
Tana rangaji ta je ta dauko Uba sanjon Aminu hankali kwonce ta kai gaban makadi ta ajiye ta rada masa magana kamar haka" Na yiwa kawata kari da Uba sanjon nan, in da budurwar da ta isa ta tarbi uba sanjon saurayinta ta dauka ta yi kari da ita bismillah, Aminu ya saka min albarka, kuma zan yi rawa da kalabina a saman kaina idan ya fadi na yi alkawarin yiwa Aminu gabar kwana biyu!"
Ihu aka dauka, makadin nan har saba babar rigarsa yake ya mike ya biyo bayanta ya sanar da danarwarta sannan ya gyara yar gagarsa ta kofi ya shiga kada mata
Sai da ta yi gamo da fan kwalinta ta dora saman kanta sannan ta gyara tsayuwarta cike da bege ta shiga rerawa Aminu waka , ga fitinaniyar rawar da HINDU ta koya mata, wai rawar daka, jama'a rawa ce tamkar babu yayan hanji a cikin mutun, rawa ce tamkar kugu zai tsinke ana wani irin abu kamar babu komai sai duwawun, watau rawa dai irin ta SHAKIRA
Har zanzana Aminu yake yi a lokacin da ya shige filin nan ya ringa mana mata yan goma goma a goshi yana bubudewa
A kadan sai da ya zuba mata sitin da biyar ya laluba ya laluba sai kudin innarsa da ta aike shi kaiwa na dashi
Wani irin zigashi da ake yi a yau ko mai gari ya ji sai gabansa ya fadi, shi ya san a kan NADIRAH ya shiga gaban maza, dan haka ya zarro kudin zubin dashin Innarsa ba tare da tunanin komai ba ya kalli makadi, makadi ya kalle shi ya shiga zarra yana zuba masa jiki har rawa yake
NADIRAH ta fara zarro ido tana kallonsa, hakama jama'ar gari, ihu fa waje ya zagaye kira ake Aminun Indirah wuta Aminu wuta aminu, Aminu na wuta ba ji ba ganni
Kanwarsa ta juya ta dankara a guje ta nufi gidansu har taka karangiya take yi, ama bata damu ba, baban burinta ta kaiwa Innarsu labarin cewa lokaci ya yi da zasu kai bayin Allan cen baban birni a masu tsakani, ga danta cen ya haukace ko kudin teburin nasa ya amsa yau yake bayarwa ko yayane? Abu dai ya giga Aminu ya bale
☹️☹️☹️☹️ Aminu ya balle jama'a mun shiga uku, Nadirah mata saman kanki ga inna nan tafe🤣😁😁😁
Cmmnt, sabon posting 😁
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```

*https://www.facebook.com/106494781436168/*