Sashe 38
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idannuwanta ta lumshe hawayenta suka zubo, hakan ya saka shi sauke ajiyar zuciya ya dan jimke hannunta sannan ya mayar da dubansa bakin titi,
Bai san yaya zai kwatanta irin raunin da jarabawar kanwarsa ke hadasa masa ba,
Kanantarta, da innocense dinta na matukar saka shi a hali na tunani, uwa uba yakan rasa me take so, me take so ne a duniya? Mutuwa ai dole ce, itama zata mutu fa, ya dace ta yi hakuri shekara nawa da rasa iyayensu? Ama Auta ta kasa yin hakuri, shi kuma ba zai mikata wajen mijinta a irin wannan halin ba, a wajen mijin natama idan ta koma koda yaushe maganarta shine, bata da aiki sai tambayar ko yaya yake? Ita a kaita wajenshi kar wani abu ya same shi, idan aka kawotan an yi ta tambayarta mafarkai take yi ne wani abu ya same shi ko mene? Amsarta daya ce ba komai.....Yana rokon Allah ya sako hasle a cikin duhun dake tare da lamarin
Kusan sallar La'asar suka karaso har fada, domin kafin su shigo sai da ya yi ta fama da jama'a, duda yau ba wani lafiyar kirki ne da shi ba, gaisuwarma sama sama yake amsawa, ama sai da ya fan tsaya yana dan amsa murnar karra aurensa, a ransa kuwa yana ayana' karin aure......karin yar matsala dai'
A lokacin da suka sauka a falonsa, bayan an gama gaisawa, su Umma du sun zagaye su, Auta na like da shi irin abin nan na da wanda a kwana biyun nan sam bata yi ba, Umma ta dube shi tana murmushi da son cusawa matarsa haushi da kuma sin fara shinfida yarda tsakaninsa da amaryarsa ta ce" Yarona, lalle wannan biki shi ake kira tuwona maina, yar manya ce yarinyar, ba zaka ji kamar a aljana kake ba sai ka ganta, masha Allah ga ladabi, ga biyaya, ga salihanci a wajenta kamar kamar me, ka san meye ga kyauta, tana son talakawanka, masu tarbe sarkar zinarin nan ta basu da awarwarayen gaba daya, baka ga yadda talakawa suka dauketa ba, kwananta daya tak a fadar nan haka ake layin zuwa gaisheta, sai da na takatar dan kar ta kwashi gajiyar da zata kasa gaisheka yadda ya dace"
Dan dagowa ya yi bayan ya gama tofawa Auta addu'a a yatsarta karama ya dan kalli Umma
Dan murmushi ya sakar mata bai ce Um ba, bare um um, sannan bai kalli HUZNAH bama bale abin ya tsaye masa a rai
Umma ta yi murmushi ta karra yin wata yar dariya tana sake satar kallon Huznah ta ce" Yanzu haka, tun kafin magariba aka gama shiryata, kanshi irin na ƴaƴan tubawa ke wasa a tufafinta...., Iso kawai take jira dan ta zo ta gaisheka"
Auta ta kara lafewa dam a jikinsa , tana dan karra rike alkyabarsa da hannunta dan bata so ya tashi ya barta da Umma, matarsa kuwa shi kawai take kallo tana ta dannar zuciyarta da addu'a
Wannan karron bai dago din ba ya ce" TA JIRA"
Daga haka ya shiga kokarin tashi, zurbat Auta ta tashi tana cicira ido da kallonsa
Gefen fuskarta ya shafa kadan ya ce" Kin sha maganinki kuwa?"
Auta ta gyada kai da sauri, dan haka ya sake yin murmushi ya ce" To ki je wajen umanki kin ji? Tun dazu tana maki oyoyo kin shareta?, Ki tafi ta raka ki dakinki ta maki addu'a, kema ki yi kin ji autana?"
Kai ta sada, ta dane kukanta, a hankali ta ce" To Abah"
Murmushi ya yi ya juya yana fadin" Allah ya tashe mu lafia"
Umma kadai ta iya binsa da iya yin da ta saba da adu'o'in da ta saba masa har ya shige sannan ta juyo da wani irin murmushi a lokacin da Auta ta yi wufff ta fita , HUZNAH kuwa na kokarin ficewar itama
Dan takowa ta yi kasa kasa sosai ta ce" Sannu da rashin sannin ciwon kai, na ga harda kokari aka yiwa kishiya, sai dai ta bayar dan inaga bata yarda da ke ba, domin ko sakawa bata yi a wuyanta ba, gashi ita din shi yace yana so kin ga bambancin da nisa sosai"
Du irin tsoro, da shayin Umma da take yi takan mayar mata da magana, dan hakane yauma ta dan gyara rufarta ta ce" Hakane Umma, na ga soyaya , domin tsabar so din nema ya saka shi zumudin karbarta a yau"
Tana gama fadi ta fice da sauri itama tana fatan Allah ya sa kar ta biyota
Umma kuwa kwarai ta shaka , hakan ya sakata yin kasakai da mamaki,
Kai ta gyada tana cije lebe a ranta ta ayana'
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```

*https://www.facebook.com/106494781436168/*
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
_FREE BOOK_
*Na*
*SAJIDA NIGER*
2️⃣6️⃣
A ranta ta ayana' Yaro man kaza, lalle ina sake da lamarinki, ama ke na zan tabaki da kaina ba, radadin kishi da abinfa zai samu Mijinki zai saka ki dabawa kanki wula da kanki ki kashe kanki, domin kima na san kina masa so irin mai tsananin nan, wannan kam ba algus a ciki, hakan zai kaiki ga halaka wawuya!'
Ficewa ta yi ta nufi Bangaren NADIRAH
Tana shiha wani kanshin turaren ne ya sake dakar mata hanci,
Ita fa mamaki take yi na NADIRAH da innarta, irin yadda suke ba tsafta da kanshi mahinmanci sai ido ya gani,
Da safe da ta shigo da sasafe Nadirar ta tardo yana guga, sai da ta tsorata walahi, domin a lokacin kowa na iya shigowa, idan aka tardota tana guga me kennan?, Da kyar ta iya hannata, haka dazu da za'ai mata kwaliyar tarbansa da kyar ta amince domin cewa ta yi bata son hoda da da shafe shafen nan na fusla, a bar mata fuskarta naturel, sai da suka yi mata a taro a taro sannan ta amince, an dauki lokaci ana kwaliyar, hala suturar da aka ciro mata abin sai wanda ya gani, du a burin Umma ta jefi tsuntsu biyu da jifa daya ne, watau ta sakawa ASADEEK yarinyar a rai farat daya, sannan ta kayar da gaban HUZNAH, bayan ta yiwa NADIRAH hudubar du jaraba kar ta yarda ta kwana a bangarensa, bata san tana fada NADIRAH na ayanna nata abubuwa a zuciyarta bane , kala daban daban wa'inda da kunnuwanta zasu jiyo mata da tana iya summa dan firgita da tsorata
Karasowa ta yi falon tana yiwa bayin dake zaune a dan takure alamun su tafi,
Da sauri suka karra dukawa suka yiwa NADIRAH da inna salama suka tafi zulatansu cike da mamakin hira fa Take yi masu su bayi?
Zaunawa Umma ta yi tana karra cika fuska rai a bace ta ce" Ba zai samu ganninki yau ba, yana tare da gajiya ne sai ya huta wai"
Wata irin boyayiyar ajiyar zuciya ta farin ciki NADIRAH ta sauke
A bayane kuwa ta talwakwabe fuska ta irin mugun hade fuskar nan bata ce komai ba
Umma ta sake yatsina fuska ta ce" Ama ya yiwa kansa asara, na tabata da ya yi arba da ke a yau da sai ya mance wanene shi, du takamarsa da mulki da kyau kuwa"
Da mamaki HINDU ta kalleta, sai dai bata ce komai ba ta cira kanta a ranta tana ayana' Toh Fah'
A fili kuwa ta ce" Ai ba zamu gajiya ba in sha Allah, mu da muke so? Dole mu jure har mu kai ga ci"
Ua ta yi murmushi ta kalli HINDU, a ranta ta ayana' shi yasa nake jin ba zan bari ki tafi ba, dan na kula kece ky din bude kwakwaluwar yarinyar nan, dan alamunta tanada ra'ayinta, ama kamar kin isa da ita'
A fili kuwa ta mike tana sake sakarwa da NADIRAH murmushi ta ce" Ki huta lafiya, da safe in sh Allah za'a kuma zo a shirya ki, dan kin san kishiyarki na kusa, ko dan ta saka maki ido tana iya shigowa, duda ke ya dace ki fara zuwa ki gaisheta ama ba zaki je ba, kwa hade a cen fadar uban gidanku ku goga, kin fi karfinta walahi, sai da safe idan na samu damar kaiki zan zo ko na turo yam mata"
HINDU ce kawai ta iya amsawa, NADIRAH ta cika, iya cika, a zuciyarta kuwa fadi take yi' Aikin banza, idam an samu damar a kaini?, Hehehe an fada masa cewa na yi ina son zuwa na gaishe shi ne? Wai takamarsa kyau, wani kyan mutumen da ya haifi su Innar birni da innata? Sunna ce masa Baba?, Ai sai fatiha kawai koda an yi kyan a da, a yanzu an tsufa kuma sai hakuri, oh ta yiwu matarsa fa kishinshi take yi, itama ko yarinyar ce ko tsohuwa ce? Allah dai ya tsareni da cusa kai ki ta Aminu!'
Tana Fita Hindu ta rafka tagumi, sai kuma ta saki hannunta ta ce" Allah, Allah mun tuba Allah, kana zamanka sai shedan ya ringa sako maka tunani kala kala, kim ga kawai sai ta ringa min ka.da kwartaye matar nan"
NADIRAH ta kalleta a zabure tana rufe baki ta ce " Astagfrulah Inna mamansa ce fa aka ce, ni mamakin da nake mamansa wace ta haife shi ko kanwar mamansa?"
"Ke hadimarsa ce, ni da Sarki ya samo min labari sala sala, baki ga jiya har dare muka raba muna tataunawa ba? Kina ji ita wannan a da baiwa ce, irin bauta ta da suka yi wace ba'a biyansuma, kuma da kika ganta a nan kina ji irin aminiyar nan ta kuryar daka mahaifiyarsa ce, domin baiwa ce da ta zama kamar yar uwa, ita ta raine shi, da kanwarsa shi yasa suke ce mata Umma, ba wata mahaifiyarsa, ke yanzu mahaifiyarsa zata neme shi da mugun nufi? Ki duba fa kalamanta, ni abinda nake son ganewa daya me tak da matar nan, shin asiri akai mata ko nuna mata aka yi idan bata yi ba za'a kasheta ko wani nata sosai? In ba wannan ba gaba daya matar nan gaskiya ko shedan dan makarantarta ne, Indi wai bata maki kama da lwartaye?" HINDU ta karashe tana karta kama haba da zarro ido