← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 99

Sashe 73

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na yarda cewa duniya ba matabata bace, na san da cewa idan na guji mutuwa a yanzu zata riskeni wata rana, na kuma san da cewa aikin alkhairina kadai zai sama min sasauci, da ace na yi gudun mutuwar da na gudo da iyalina mun kawo maganar, sai dai sannin da na yi kai tsaye ba zan taba yarda na tunkaroku da wannan maganar a min kallon mai hankali, da kuma sannin da na yi ina iya rufta kaina a ciki , sannan idan sun ci galaba a kaina sunna iya neman wani da aikin ya saka ni amsa, na saka rayuwar yata a hadari, ta matata da ta yar uwarta baki daya a hadari tare da yarda cewa Allah zai karemu, shi zai bamu mafita, shi zai nuna min rana irin ta yau" Aba Salihu ya fada yana sake duban ASADEEK

Kan ASADEEK wani irin zafi yake fitarwa hakama kirjinsa har sama sama yake yi na tashin hankali,
A hargitse ya dubi bangaren da Sheikh yake har yana hade harshe wajen fadin" UMMA, UMMA ce ta yi jagoranci a lamarin dauko amarya, shin bata san wa aka bata ba? Bata san tsare tsarensu ba?"

Gaban SHEIK sai da ya yanke ya fadi, da sauri ya kalli ABA SALIHU gabansa na faduwa ya ce"

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

5️⃣2️⃣

Gaban Sheik sai da ya yanke ya fadi, da sauri ya kalli Aba SALIHU gabansa na sake faduwa, sai kuma ya kalli ASADEEK muryarsa a tausashe ya ce" Me zai hanna mu dakatar da binciken haka? Ka fa san zurfafa bincike kai tsaye bashi da dadi fa, kuka bayan wannan ka gaji sosai dan Allah mu je ka huta"

Murmushi mai daci ASADEEK ya yi yana kallon SHEIK, muryarsa a tausashe ya ce" Kana tunanin a irin yadda nake cakule da al'uma akoy abinda zai sameni daga dan Adam ya summar da ni?, Ina iya jiran komai daga dan Adam, kaine ilimina, nine alkalinsu, babu irin kwababiyar rayuwar da ba'a kawo min, ka daina yi kamar zaka yi kuka fan kawai na ambaci abinda kake son na gani shekara da shekaru, ka sani tunda na ji ba ita aka aura min ba nake bibiyar UMMA!, Tabas a da ina kin hakan dan na ga irin tsakaninta da Auta, kar ka manta UMMA ma'aikaciyar ANNA ce, watau amintaciyarta ta dogon zamani, ka fi kowa sannin amintacen bawa kan iya zama makashin sarki,nawa aka yi, tun kafin a haifeni ake yi, babu abinda kudi baya haifarwa da mulki, ka barshi ya sanar min matar da kuka zo tare shin ya ga wani abu da ta sani a cikin lamarin ko an rufeta a baibai ne?, Ka barshi ya rufa min asiri ya sanar min wanene AMINU?, Wadinnan abubuwan sunne suka kawo ni garin nan idan na ji su a yanzu a yanzu zan juya kasata, idan ban ji su ba kuwa ba zan koma ba!, Ba dan ina tsoron kar a cin min ba, ko daya, hasalima ji na yi ko menene ai bai isa ya riskeni in ba Allah ya hukunta min ba!, Magauta kuwa a cikinsu muke zagaye, ba wai ni ba harta baran gidana!, .......DAN ALLAH ka sanar min ita matar nan mai dan haske gajeriya mai dan jikin kiba kadan wace suka zo tare ta san wani abu a cikin lamarin?" ASADEEK ya karashe yana kallon ABA SALIHU, wanda shima tunda ASADEEK din ya fara magana ya fahimci tabas matar a kusa fa shi take sosai, kuma ya ji sunnan AMINU dainda cikinsa ya so rikicewa, kai jama'a wannan Aminu dai yana wahalar da shi ainun

A sanyayensa ya ce" Allah ya taimakeka, in dai matar da suka zo tare ce kake nufi, wace tamkar itace ja gaban komai a lamarin, ita ta yi tuwo ta yi miya a tafiyar, domin a nanma zuwan sarki biyu wajenta sunna tsare tsarensu, ranar da za'a tafi da NADIRAR ma da kyar matar ta yarda mahaifiyar Nadirar ta ganta, wai kar ta lalata masu shiri a yadda ta sanar min"

Hannaye biyu SHEIK ya saka a gaban goshinsa ya dafe goshin nasa, dan irin dukan da kirjinsa ke yi masa ba na wasa bane, gaba daya bai so ace ASADEEK ya ji irin maganar nan haka ba, ya so ace a hankali ya fahimta da kansa ba wai ya ji daga bakin wani ba

ASADEEK kuwa jajayen idannuwansa ya daga sama yana kallon oankar dake gudu da dukkan karfinta tana busar masu da zufar jikinsu, ama sai yake ji kamar wace take tsatsafo masu da zufa ne, dan a wajen babu wanda baya alamu na zafi yake ji

Idannuwan nasa ya mayar kan Aba yana mai jimke hannunsa, a hankali ya ce " Kana nufin, tana cikin shirin da suke yi?"

"ASADEEK" SHEIK ya fada bayan ya dago kansa

ASADEEK ya dubi SHEIK, ya sake kallon Aba
Kai ya girgiza yana neman soke kansa kasa ya ce" Ba zaka barni na gama jin abinda nake son ji a nutse ba? Ka barni na ji mana ko zan iya musalta abinda nake tunani a kanta, kar ka manta da sunnan da muke kiranta, kar ka manta kanwata a hannunta take, kar ka manta nakan ce da kai ban san dalilin da yasa idan ta zo waje kanwata ke nutsuwa ta daina magana ba, nakan ce da kai ita kadai ce maganin kanwata idan ta rikice da maganar sai ta koma gidan mijinta ita kadai ke rarashinta ta bar maganar sai ta warke, kar manta bata da shamaki da bangarena a kowani irin lokaci, kar kuma ka manta tana da damar da HUZNAH bata da ita a fadata!, Ni a uwa na dauketa shi yasa nake kiranta UMMA, shi yasa nake zama a ci abinci da ita da iyalina!" Ya karashe da wani irin yannayi mai dukan zuciya

Aban NADIRAH gaba daya sai ya ji shima nashi hankalin ya tashi a irin furucin UMUGHLUK ITIBEL
Kennan wannan matar har haka take da kusanci da shi?, Lalle da ace zai bude masa dukkan abinda ya sani a kanta tabas zai ji masa mugun ciwo haka kuma idan har ya ci gaba da ganninsa zai ringa kallonsa matsayin wanda ya kawo masa mugun labarin nan, masoyi masoyi ne a zuciya fa

A sanyaye ya sada kansa ya ce" Allah ya huci zuciyarka, bakin abinda na sani kennan"

Da mamaki UMUGHLUK ya tsareshi da ido, kwarai ya fahimci ba gaskiya ya fada ba, ama kuma sai ya gaza fitar da hanyar da zai saka shi karfi da yaji yin biyaya, hasalima ji ya yi zai iya kyale shi ya zabi abinda yake so, fada masa ko kin fadi ya isa da hakan!

Ajiyar zuciya ya sauke yana hararan SHEIK wanda ya sake soke kai yana sauke ajiyar zuciya da bawan Allahn nan ya gane abinda yake nufi, gaba daya baya so tashi daya ASADEEK ya san irin haka, lalle jarumi ne shi, ama babu wanda déception irin haka ba zata yiwa ila ba, bai san girman ilar da zata iya yi masa ba, ama ya san tabas sai ta yi masa ila, tunda har aka saka shi a hanya to zai idasa gannin abinda shi kadai ne baya gannin, watau halayar matar nan da yake kira UMMA!

Sun jima a haka, sai da ya idasa daidaita dukkan hargitsin zuciyarsa sannan ya sake bude bakinsa, wannan karron muryarsa a wani irin jigace take yana kallon kasa ba ainahin inda ABA SALIHU yake ba , a sanyaye ya ce" Tauyeta kuka yi ko?, Ko ta yarda ta kawar da ni din ne?, Yaya aka yi ta yarda da maganar aurena bayan tana da fada?"

Ido hudu SHEIK da ABA SALIHU suka yi, sai kuma suka kalle shi
Gannin dubansa a kasa ya nuna wata alama da girmamawa da jun kunya irin ta sarakunta
A hankali Aba SALIHU ya kai dubansa kasa shima, muryarsa da datako da girmamawa ya ce" Ka gafarci shiriritar yar HINDU, kwarai bata jin magana, da sakalci a tatare da ita, sai dai tanada amana sosai, tabas Biyaya ta yi mana a kan maganar auren, ta yarda ne da sharadin idan komai ya bayana zata samu salama ta dawo gida"

Idannuwansa da suke da ja ya dago a hankali ya kalli Fuskar Aba, shima Aban a lokacin shi yake kallo, hakan ya saka shi fadin" Ta dawo ta samu AMINU?, Aba wanene AMINU?"

Aba Kam magangannun sun yi masa nauyi ainun, sai dai du urin kauce kaucensa UMUGHLUK bin tambayiyinsa yake yi daya bayan daya, ko ya kaucewa wata amsar a dole zai bayar da wata,

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Shi aminun irin soyayar kauye ne suka yi, shi tuzurun kauye, ita tuzuruwar kauye, tunda a kauye dai mai shekarunsu ya jima bai yi aure ba gaskiya, innarda ta nuna bata so ba zata yarda ba, ita kuma tace zata yi jira har innar tasa ta amince, shirme ne irin na yara, domin sunna tahowa innarsa ta kai kudin yan kata biyu dan badangarci ta masa daki biyu a gidanta ta aura masa, guduwoma ya yi nan din wai na je a raba auren baya sonsu, da kyar da fama muka mayar da shi gudu irin na barewa, sai gashi ko kwana uku ba'a yi ba da kansa ya tardoni yana sheda min an samu karuwa matan nasa na dauke da junna biyu , shin har yanzu babu labarin INDI?, Shine na sheda masa na fa yi mata aure, da fushi dai ya bar wajen nawa"

ASADEEK harda su talabe haba, kai jama'a yanzu Fisabililahi gasa masan da take ashe saurayin ya dane mata har biyu ita tana cen tana cewa kar ya karki abinda yake nasa ba nasa bane?, Um yarinta kennan, kanwar hauka

A hankali ya furta" Allah shi kyauta "

Sheikh da yake kunshe dariyar wai Tuzurun kauye da tuzuruwar kauye ya amsa da amen ya Allah

Agogon hannunsa ya duba, sai kuma ya mike tsaye a nutse ya ce" Aba"
Chapter 73 · 0% Book details