← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 99

Sashe 77

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gidan ubanda kika aikesu!, Fada ya yi da wani mutun mai kama da yan ta'ada, a yadda yan anguwa suka ce mutumen ya masa alkawarin batar da shi da danginsa, maganar da nake maki harta BAHIJA sai da ta wuni a summe bale masu gadinsu, sai da likitoci suka wuni a kansu baki dayansu sannan suka dawo hayacinsu!, Ki gagauta bincikar yarinyar nan dan ni abin nan na kasa amincewa da shi, gashi kina nan kinaa shirme kin ki maida hankali a kan dan aikin da aka baki ba wani ba, ni kam babu abinda zai mayar min da aiki baya na fada maki, wayar uwar ke hannuna sai kira yar uwar tata take yi, ki je ki sanar masu gaskiyar lamari cewa an sace yan uwansu mu babu hannayenmu a ciki, kuma su mayar da hankali su mana aikinmu ko suma da suka rage mu kuma mu salwantar da rayukansu!" Ta sake fada a kausashe

Wata ashariya UMMA ta lailayo ta lailaya mata a haulace ta ce" Ke ama mahaukaciya ce !"

"Kece mahaukaciyar daba da baki san abinda kike yi ba!" Ta rama itama rai bace, hakan ya saka Umma mikewa tana rarumar tufafi domin zannin kansa watsewa ya yi tsabar firgicewa da kidimewa

Zata yi magana Muryar sarkin tanus ta dauke tata muryar, cikin hali naa bacin rai da daguwar hankali ya ce"

Salam

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

5️⃣5️⃣

Cikin hali na bacin rai da daguwar Hankali ya ce" Saurara hakanan mana Laure, kina jina ki san yadda zaki yi da maganar, ni dai ban san ina suke ba, abinda na sani aikina da kike nan kina jan jiki har yanzu ba'a yi ba bayan na tura maki maganin, ke kin san ribarki ce, kamar yada take tawa, shawararki ce ki maida hankali a yi ko kar ki maida na fada maki!"
Daga haka ya kashe kiran ya shiga balbale matarsa da masifar da ba laifinta ba, har hutawa yake yi yana dorawa daga inda ya tsaya, fadi yake du itace mai laifi da bata iyawa kanta a komai sai masifafen la'ananen kishi marar anfani, maimakun ta je ta tsaya a inda y'arta take ta karra gargadinta kan haukan nuna kanta kafin a kashe sarki tana nan tana hauka, wai itace harda gayatar wani kato gida bayan an boyeta ne? To ta yi da kyau , ta maida hankali sosai, idan har ta yarda ta yi shirme ta falasa kanta shi ya san inda zai kai kansa ya tsira, tsakaninta da UMUGHLUK ITIBEL kuwa sai ta san ta yadda zata guje masa! Babu abinda ya dada kansa a kas walahi

Abubuwa suka taru suka yiwa mahaifiyar Bahija yawa , ra rasa ina zata kama, ta ina zata fara, itama kwana uku kennan yau tana kiran number yar uwarta bata samu, ko a whatsup din ko a kira direct, tun ranar da ta sanar mata dan banzan danta ya saka layinsa na Nijar rabonta da su, Allah dai ya sa ba wata jarabar bace ba kuma, domin idan har ta yi wasan da UMUGHLUK ya damke su sun bani walahi
Hijabinta ta saka mai nikaf dan ficewa a boye a taxi dan ta je inda ta boye BAHIJA dake cen kamar mai sabon kamu sai ihu take yi wayoyinta, number balarabenta meye meye, abu dai gayanan ya same su ba shawara ba sasauci ga sarki sai dora mata laifuka yake yi ita daya

____________________________________

Komai take yi jikinta rawa yake har ta gama saka rigar atampar da ta yayumo a cikin suturunta

Bata taba tunanin zata ji dan labarin da zai rikitata a kusa kusa ba har ya sakata fita ba alkyaba irin na yau, to dama hakane a duniya mutun marar gaskiya ya fi kowa saurin kidimewa da neman shiga a rikicewa komai kankantar abu

Hijabin sallarta daya tak wanda yake warin ruwa da ajiya dan ba wani wankeshi ake yi ba, shi da ba alkyaba ba? Ai bashi da wani anfani tunda ba na sakawa a yagawa mutanen masarautar AGADAZ

Idan fa makantar ta nufo zuwa take yi da dukan karfinta

Hankalinta tashe direct bangaren NADIRAH

Tana zuwa ta samu NADIRAR ita kadai a falo tana zaune, kasancewar karfe tara na safiya ta wuce tana kallon film din hausa a TV tana ta doka murmushi, ta sha shiga irin ta hausawa watau riga da zani na atampa dinki mai kyau mai sauki, dauri ne ta rangada ture ka ga tsiya wanda ya yi wani irin kyau a saman kanta, kanshin da jikinta ke fitarwa kuwa kadai abin takamar kowace mace ne ace tana fitar da shi, sansanyan kanshi mai saka nutsuwa, babu inda baya fitar da kanshin a sasan jikinta har zuwa gashin kanta, akaifunta kuwa har wani daukan ido suke na gyara

Ido cikin ido suke kallon junna ita da UMMA
Da mamaki take bin UMMAN da kallo har ta zauna saman kujera tana ta wani dan tabe tabe haka a jikinta, ta kalli nan, ta kalli cen

Sai da ta gama waige waige irin na munafukai sannan ta dan matso kusa da NADIRAH wace ta kama kanta ta shiga neman hijabinta dan gaba daya bata son wata mu'amula da matar walahi

Umma kasa kasa sosai ta ce" Kin ga jiya bamu zauna ba ko NADIRAH?, Du irin yadda na so na salami baki da wuri mu zauna mu sha dariyar diramarki abin ya gagara, gaskiya kin kware ina matukar sara maki, idan kika gama aikin nan ina mai tabatar maki nima sai na maki kyauta taki ta bajinta"

Irin kallon da NADIRAH ke yi mata da tana cikin hayacinta da ba zata taba amincewa da shi ba, ta yiwu sanadiyarsa har sai ta kawo kararta wajen ASADEEK, ama da yake yanzu hankalin nata gaba daya ba a jikinta yake ba sai bata gani ba

Kullin dake boye a jikinta ta fitar, kasa kasa sosai ta miko mata tana fadin" Shin yaushe ne zaki yi anfani da wannan? Lokaci fa sai ja yake yi NADIRAH"

Gaban NADIRAH sai da ya kwonci kwonci ya fadi, ta tsurawa abin ido ta ki tabawa ko da hannunta ne

Umma zata sake mika mata AUTA ta fito daga daki dan Inna ta gama mata abinda take yi mata tuni, Innar cema ke ta bige bigen waya bata samu yanzu dai ta ji ta samu mijinta shi yasa ta fito ta bata waje

Da sauri UMMA ta mayar da hannunta tana soke Maganin gabanta na faduwa, lokaci daya kuma ta hade girar sama da ta kasa tana jira Auta ta gaisheta ta koreta daga wajen su gama magana da NADIRAH, dan so take yi yanzu yanzu ta bata abin nan idan da hali a yau yau ta zuba masa a abincin kowama ya huta

Ba tare da sakewa ba ta gaisar da Umma, daga nesa nesa , sannan zuciyarta cike da mamakin shigar ta UMMA, ashe Umma zata iya zuwa wani waje ba Alkyaba? Ai ita tana iya rantsewa tunda aka yanta Umma da saka alkyaba bata taba ganninta babu ita ba

Gefen NADIRAH ta zauna a hankali ta sadda kanta, dan ba zata taba iya sakewa a gaban UMMA ba

Kasa kasa sosai NADIRAH ta ce " Dago min kanki!"

A hankali ta dan juyo zata kalleta, sai ta sake sinne kan nata gabanta na faduwa

NADIRAH ta ja tsakin da ya saka UMMA kallonta, zata yi magana a zafafe salatin INNA Hindu ya katseta

"Lah Ha ila Ha illalahu, Muhamadu Rasulullahi Sallallahu alaihi Wa salam, HABU ka yiwa darajar sy gwagwo ka daina ce min ba'a san inda su aunty suke ba, wani irin ba'a san inda suke ba, Habu wannan wani irin magana ne? Shine bake kiranka jiya wuni guda cirrrr ka ki dagan waya?, Habu ina yar uwata da mijinta suke? Wa bilahilazi ana neman a mutu, ana nan a shiga uku! In na yarda Ubana goma!, Kan uba wayo na shiga ukuna!" Ta karashe a haukace, tana idasa fitowa falon gaba dayanta, lokaci daya tana cuje dan kwalin kanta ta yar

"Innata lafiya?, Menene?" NADIRAH ta fada muryarta na amayara da alamun tashin hankali

Hannaye kawai take ta watsawa, ta yi nan ta yi nan tamkar wace ke hali na maye, gaba daya Nadirah da auta suka kasa tsayar da ita daga yawon , tana yi kumatana rusa kuka tamkar wace aka yiwa mutuwa

Da kyar hankalinta ya kawo kan UMMA , wace ta yi tsaye itama hankalinta a matukar tashe tana kallonsu fargaba shinfide a saman fuskarta

Hannunta da NADIRAH ke rike da shi ta janye a birkice ba tsoro ko dar ta karasa kusa da Inna idannuwanta tarr cikin nata ta ce" Ina yayata?, Ke ina yar uwata?"

Umma ta ringa son nuna mata ba fa su kadai bane ta hanyar fadin" Ban gane hausarki ba fa ni, wace yayarki kike tambayata a nan ni kadai ce mutun?"

Inna ta kunce zaninta ta mayar da shi saman cikinta ta daure shi tam, ta fuskanci Umma muryarta a matukar tashe ta ce" baki gane cewar a yanzu na kai matakin da bana tsoron kowa da komai sai mahalicina ba? Ya dace ace kin jima da karantar haka a cikin idannuwana, Habu yace yau dare na biyu kennan da ba'a ga yayata da mijinta ba, wai wata magana kamar ta yan giya ya yi musu da wani mutun ya masa alkawarin karar da danginsa, bari ki ji , gabs daya a tsarin nan da kuka yi babu abinda na yarda da shi, ku kuka sacen yar uwata da mijinta, ku fito min da su ko tarayar tamu ta yi gagawar watsewar da bakwa tunani na rantse maki da Allah a kan haka ko kaina aka sare bani da damuwa dan ban zabi duniyar fiye da kiyamar ba, na san cewa zamani muke ciki mai shudewa tunda uwata da ubana sun mutu nima tawa na kusa mutuwar, ke ina AUNTY FATIME DA MIJINTA!"
Chapter 77 · 0% Book details