Sashe 45
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sheikh bai san lokacin da ya ringa juya kai yana ambaton Allah da mugun mamaki ba, toh fa, gaskiya ne akoy matsala a tare da yarinyar, yo ko ba yar sarauta bace ai mugun mugun girmansa na sakawa a duka gaishe shi fa, kuma gaisuwar ce kanta sai a hankali gaskiya, oh ya godewa Allah da baya nan😔
Sai kuma ya samu kansa da damuwa da tunanin ama me ya sa Bafan ASADEEK zai aikata haka?
Da yannayin damuwar ya fitar da tambayar
ASADEEK ya dube shi ya ce"Ni bama wannan ba, Bafa ina iya ajiye haka a wani bigiri daban, tambayar da nake son yi yanzu shine Umma, shin UMMA bata san Bahijar bane kafin auren ko menene?, Na ga ita ta amso yarinyar ita kuma ta ci gaba da gabatar da ita matsayin Bahija, ina so a kirawota yanzu dan kaina ya fita daga duhu"
A hankali SHEIK ya fuskanceshi, a sanyaye ya ce" Ni kuwa da zaka amince da na kawo wata shawarar Allah ya karra maka lafiya"
Dubansa ASADEEK yake yi, har ya yi niya dan kansa ya furta" Ina sauraro"
SHEIK ya sauke ajiyar zuciya , cike da yannayi na son convincing dinsa ya ce" a lamarin nan ina hangen wata sarkakiya, wace da son samu na yi, mu bita a hankali, sannan mu hadata da ayar Allah, Allah ya taimakeka na tabata ko a yanzu da muka dan fahimci wani abin, ina nufin wanu abin ya fito fili Allah ne ya haska mana, ba isanmu, da dabararmu ba......, "
UMUGHLUK ITIBEL ya sake dubansa, a nutse yana fitar da harufan a daidaice ya ce" Kana nufin, na yi shiru ko Umma kar na fadawa maganar nan?, Kana nufin na yi shiru a gaban yarinyar nan karama kamar mai shigar aljannu ina kallonta a matsayin wace ba ita ba?, Kennan ni abinda nake jirab sani da wancen din fa ya fadi a banza? Sai na salameta ta tafi tunda babu amfani dama wannan ne anfaninta"
Ido Sheikh ya tsura masa, duba yake yi masa irin na dama na san da wata manufar ka aminta da maganar auren nan,
Fuska ya hade sosai yana dauke kansa, irin baya so a sake dauko maganar kwata kwata, domin ba irin tsarewar da Cheik bai yi masa ba a kan maganar ya nuna masa ba wani abu a kasa aure aka bashi ya amsa,
CHEIK ya gyada kai yana sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Ko me yake boye a cikin lamarin nan kamar yadda nace ne, ba rikicinmu zai bamu ba, sannan ka sani a yanzu ina so ka rufe mata wannan magana, ko me take kunshe da shi ka kyaleta, kuma wannan yarinya da daya rana kar ka nuna mata ka san komai, hasalima ka jata a jikinka ko zamu fahimci abinda yake boye, kar ka manta Allah na fitar da fari a cikin baki, yakan kuma fitar da baki a cikin fari, Allah ya karra maka lafiya da nisan kwana bamu san me hakan yake nufi ba, ama zamu bashi damar bayanar mana da kansa in sha Allah "
Numfashi ya sauke , ya mayar da kansa ya jinginar,
A hankali ya furta" Zan yi tunani a kai"
CHEIK ya amsa da "Allah ya baka ikon yarda da abinda na ce"
Shi dai daga nan bai ce masa komai ba, girmama girman rainin yake yi a zuciyarsa, kuma yana tunanin anya zai iya boyewa Umma kuwa? Idan ya boye mata anya ba zai hadasa masa wata matsala ta rashin yarda da ita ba kuwa? Abin ya tsaye masa a zuciya ainun, har CHEIK ya yi masa salama ya tafi yana fadin sai ya fito Fada in sha Allah
_________________________________
Yadda Umma ta ga dare, haka ta ga rana
Wayar da ta kwana bugawa tun jiya sai yau aka daga
Bata tsaya wata wata ba ta ce" Kina tunanin yarinyar nan da wace ta rakota sunna iya hadasa min da matsala a kan abinda nake gannin mun kawo ga ci?"
Gimbiya ta yi siririn tsaki, da wata masifar ta kwana, BAHIJA ta rikice wai sun yi waya da balarabenta ama yace zai kira shiru har safiya bai kira ba, sai kuka take yi gana ta kira ya ki dagawa, ita kam wannan masifa ta balarabe anya ba zuwa zata yi a nemo mata inda zata ganowa y'arta shi ba?, Wannan abu ya fara daga mata hankali sai ga wani shirmen kuma
A dake ta ce" Ban fahimci yarenki ba"
Umma ta sanar mata dukkan abinda ya faru, daga farko har marin nan na jiya
Da takaici Gimbiya ta ce" Wannan wani irin sake ne? Ita wace ta rakatan me take yi har yanzu a cen? A kan me zaki bari har haka ya ringa faruwa ? Ina fata ba wani tunani gareki a kan yarinyar nan ba ko?, Dan kina iya janyowa kanki wani abin, kuma ki sani idan har muka yi sake mune a ciki, dan haka zan tado mutun ya kawo maganin nan, zan amsa daga wajen Aban Bahija a kawo a saka masa ya ci kowama ya huta!, Ita din bamza yar talakawa zamu yarda ta kawo mana cikas din ne? Bata isa ba, uwartama bata isa ba bale ita, ke kuma idan haukanki ya saka ki aikata aiki irin na sake ai shikenan!"
Da wutar ciki itama ta ce"
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```

*https://www.facebook.com/106494781436168/*
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
_FREE BOOK_
*Na*
*SAJIDA NIGER*
3️⃣1️⃣
*Asalamu alaikum jama'ata yan uwana masoya yan albarka grup SAJIDA PALACE, ina matukar godiya, ina miko maku fa godiyata, ban amsa maku tarin comment bane dan ban zauna ba, ama zan amsa ku kun san son so ne fisabililah💓💓💓, my zuciya na yin bubuduk idan ina karantaku😂, kaunarku da kaunata sun riga sun makaleni a kuluna, shi yasa zan wankeku da biyu matab albarka*
Da wutar ciki itama ta ce" Aikin da kuke fadin zan aikata kina wani karra maimaitawa ai ni ban taba boyewa ba, gwara ni da ke, kema kin san abinda nake nufi, kuma da kike fadin idan sun isa su gwada tambayarki na yi, ki tabatar min domin dan na mareta Matar nan ta min wani kallo da rabona da na ga irinsa tun a lokacin da na rungumi kanwar Asadeek da tana kukan mutuwar iyayenta, idan kun san wata jaraba kuka hadoni da ita sai ku sanar min na dauki mataki, dan ni babu wanda ya fi karfina!"
Tsaki Gimbiya ta ja ta kashe kiran ta wurgar a bayyane ta ce" Shashasha ko ita wa? Idan ta tashi burgarta ta rufe ido ta ringa ihun babu wanda ya isa ya fi karfinta, zaki ga fin karfi ne, domin wannan aiki da za'a aikata tsumi tsumu sai kin samu kanki a ciki, sai na ga ta tsiya, karamar aniya!"
Tana maganar ne tana rufa alkyabarta bata tsaya kula kowa ba ta dauki hanyar bangaren mijinta, dan ta tabata da wahala in ya yi sallar asubahima , ta yiwu yana cen yana rizgar barcin asara
Tana zuwa ta kwashi wani kayan haushin
Sama sama ta ringa jiyo muryarsa yana fadin" Yauwa yar albarka rike da kyau, dan matsa kan kin ji?"
Zama ta yi tana ta karkada kafa a falon har wani yangwamamen ihunsa ya karade wajen sannan ta ji shiru
Mikewa ta yi ta shige dan ta tabata a irin lokacin shi kuma ya shige bayi dan ya wanke jikinsa
Tana shiga ta bi yarinyar da kallo, yarinya karama, sam bata santa a masarautar bama bata taba ganninta ba
A rikice yarinyar dake goge jikinta da ya bata mata da wani ruwan jikinsa mai gari gari ta shiga rarumar kayanta jikinta na rawa tana kallon gimbiya da neman fashewa da kuka
Bata ce mata komai ba sai da ta gama saka kayan nata sannan ta karasa ta mata wani shaka wanda sai da ya saka yarinyar fitar da idannuwanta waje a rikice tana kallonta
A kausashe Gimbiya ta ce" Kin san hukuncin fitar da maganar kin zo dakin nan kin aikata wani abin ko baki sani ba?"
A rikice takebada amsr ta sani muryarta na fita da kyar
Gimbiya ta saketa ta karasa ta buda kayan mijinta ta dauko kudi ta watso mata sannan ta amshe wayarta ta cire layukanta ta nuna mata hanyar fita
A gurguje ta idasa daura nikaf dinta ta fice hankalinta tashe, du gani take yi kamar biyota zata yi ta kasheta, domin a cikin gari sunnanta ya baci iya bacewa
Fitowa ya yi yana dan washe baki dan ya gama zubar da tsiyarsa a titi
Turus ya yi gannin Gimbiya, sai kuma ya daure fuska yana fadin" Meye?"
Gimbiya ta kwashe shi ta watsar tana cire kanta ta ce" Jakadiyar Kasar AGADAZ ta yi kira a kan abinda ya fara fuskantarta, shine nace za'a turo da maganin nan a yi abinda ya dace tunda wuri, dan bana son lamarin wasa, tunda farko na so ace an yi, idan gangancinta ya saka ta aikata abinda za'a gane ta sakamu a matsala kennan"
Dakin ya karra bi da kallo, ya kalleta kamar bai san me tace ba ya ce" Ke ima yar mutane?"
Goshinta ta dafe da takaici ta ce" Ka san dai da ranshi ba zan yi wasan kashe yar mutane ba ko?, Ta tafiyarta "
Kafadu ya dage ya kai zaune yana lalubo wayarsa ya ce" Na sani, abin naki ne wani lokacin kamar baki da imani"
Da takaici ya kumeta kasa ce masa ci kanka ta yi, kawai ta yi zurru tana kallonsa har ya gama rage girman idannuwan nasa da kyar ya lalubo number Umma ya buga mata kira
Takaici ya saka gimbiya girgiza kai, watu bama zai yarda da maganarta ba sai ya ji ta wancen ko?