← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 99

Sashe 2

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nutse Ustaz AL'AMEEN ya matso ya shiga bayani kamar haka" _"A shari'a kisa ba tare da haƙƙi ba babban laifi ne, ba tare da mun ja da tsayi ba, ina ga ubangijinmu da ya haliccemu ya tsara mana yadda zamuyi rayuwarmu, Allah bai yarda wani ya tauye ɗan uwansa ba, hakan yasa da kanshi ya faɗa cewa *ya haramta zalinci a kanshi* bare kuma bayinsa? Manzon tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi saboda ya kiyaye rayukan al'ummarshi ya yi hani mai kaushi akan ko da wanda zai tsorata ɗan uwansa ne, haramun ne musulmi ya tsorata musulmi da abunda zai iya cutarwa ko da kuwa ciki d'aya suka fito, sannan duk dan a nuna mana haƙƙin ɗan adam aka faɗa a hadisi ingantacce idan mutum zai yi yanka to ya wasa wuƙarshi da kyau, sannan ya kyautata yankanshi, ma'ana ita kanta dabbar ba'a yarda a wahalar da ita ba. Ina ga wanda zai kashe rai? A suratul Baƙara aya ta 178 Allah yana cewa *Ya ku waɗanda kukayi imani an wajabta a kanku yin ƙisasi a cikin kisa, ɗa mai ƴanci da mai ƴanci, bawa da bawa, mace da mace*... Ma'ana idan ɗane komai gatanshi idan ya kashe ɗa to shima a kasheshi, idan bawa ne shima ko bawan wanene a kasheshi, a yanzu kuma da ya zamana akwai ƙarancin bayi, dole ne muyi ƙisasi ga duka al'ummarmu, dan duk al'ummar da za ta yi shiru bayan an kashe mata rai, to da yiwuwar iftila'i ya saukar mata, dan kuma a suratul Ma'ida aya ta 32 lokacin da Ƴaƴan Annabi Adam Ƙabila ya kashe Habila Allah yace *Saboda wannan muka wajabta akan ƴaƴan bani isra'ila wanda duk ya kashe wata rai ba tare da wata rai ba (ma'ana idan shima ba kisa ya aikata ba) ko kuma ba tare da fasadi ya aikata a ban ƙasa ba, to fa tamkar ya kashe duka mutanen duniya ne gabaɗaya*...kenan da wannan ina ga zamu iya yankewa wannan hukuncin kisa dan kuwa bayan laifin kisa dake kanshi akwai laifin fasadi aban ƙasa, ba wai tausayi bane kuka nuna mishi da kuka ajeshi, dan Allah ma a aya 93 dake cikin suratul nisa'i cewa yayi *duk wanda ya kashe wani dagangan to makomarsa jahanama ce yana mai dawwama a cikinta kuma Allah yana fushi dashi sannan ya tsine masa albarka kuma ya masa alƙawarin azaba mai girma*."_

Gyara tsayuwarsa yayi tare da ƙara jan alkyabbarsa irin ta malamai fara ƙar sannan yace" Hukuncin kisa ne a kanshi ta hanyar jefewa, ba kuma mu ne muka faɗa ba wannan hukunci shari'a ce ta zo dashi, daga cikin mutane ukun da aka hallata jininsu akwai tsoho mazinaci, ba wai tsoho tukuf ba ake nufi, ana nufin wanda ya taɓa aure ko kuma mai auren, dan a nan soyayyar da zamu nunawa wannan mutum ita ce mu jefeshi da duwatsu har sai ya mutu."

Wani irin kuka Matar sarki ta fashe da shi, wanda ta kasa rikewa har sai da hankalin jama'a ya karkata kanta

Da sauri aka riketa ana bata baki kan ta yi shiru za'a saurara masa ta bari a gama magana, an tabata mijinta zai nemawa dan rikonsa sauki a wajen Zakin sarakai!

A dake ya shiga ratsowa duban jama'ar nan, ya zamto an sake budawa masu biye da shi da rumfarsa suna nemi biyo shi, sai dai lokaci daya ya dakata ya masu nuni da kar su biyo shi, hakan ya sa du wani mai makami wanda ke tafe cikin tawagarsa mikar da makaminsa da kuma shiryawa koda ta kwana

Sai da ya zo tsakiya ya tsaya
A nutse ya ringa duban jama'ar dake zagaye , har sai da wajen ya sake daukan wani shirun sosai , a tausashe ya bude bakinsa ya ce" Su wanene mu? Me muka taka? Me muke takama da shi? "
Ya ajiye maganar yana sake duban du wanni wanda ke iya yin ruwa da tsaki a lamarin

Idannuwansa ne basu da sauki a motsinsa, sunne kadai zasu iya nuna maka idan ka tarbi gabansa yana iya cinye namanka danye a masifa, shi yasa ba kowa ke iya ido cikin ido da shi ba, sai wanda ya taki tasa takakiyar shima

A kausashe ya dora da fadin" Laifinsa ne bai isa a zartar da hukuncin da ya dace a kansa ba, ko gatansa ne ya haramta masa daukan hukunci?"

"Mace ce mai daraja, tana dauke da auren kanninsa a kanta, ya shiga dakinta ya haure mata ta hanyar fyade, shedun bayi bakwai muka samu da tsoro ya hanna su magana!, Ya afka mata, ya yi zina da ita, ihun kukan da take yi ya saka shi shake wuyanta da hannayensa idannuwansa sun rufe burinsa ya kai ga ci!, A haka ya kasheta, da Aurenta, da darajarta , shima da nasa auren, ama dan yana dan gata ne za'a boye laifinsa? Dan yana dan gata za'a kasa zartar masa da hukunci? A gobe idan wani ya aikata wani laifin ana iya tura min takarda dan jiran hukuncin da ya dace dan rashin adalci?" Ya karashe wannan karron da dan karfi, domin sai da Dogari ya bude bakinsa da karfi yana fadin" ALLAH ya huci zuciyarka Zakin sarakai, Allah ya huci zuciyarka"

Yan yatsunsa yake ta aukin dannawa da babar yatsarsa dan ya sasauta fushinsa

Sai da ya gamsu zai iya magana ya ce" HUKUNCIN dake kanda, bisa koyarwar Addinin Musulunci shine hukuncin kisa!, Bisa hanya mafi wahalarsa ko Allah zai gafarta masa!, Zai fuskanci horo na kwana uku kafin a jefe shi, WANNAN shine hukuncinsa bisa Adalci!"

A yanzu kam kukanta kasa rikuwa ya yi, harta ita kanta ta kasa rike kanta, da karfi ta kubce har tana neman yadda alkyabarta da ta daka a yanzu yanzu da zata fito itama.
Da gudu ta ringa ratso mutane, lokaci daya mijinta ya hangota haka kuma ya ga sarkin dakin duhu ya ciro sharbebiyar wukarsa ya daga kafa shima ya nufo filin da take kokarin shigowa

Bai taba sannin shekarunsa ba zasu hanna shi sauri dan tare iyalinsa ba, sai da ya ga yana kokarin yin sufa ya durfafeta lokaci daya ya damki hannunta ya fincikota baya ya zubar da ita kasa sannan ya kai kasan shima ya yi anfani da damarsa biyu , ta farko ya riketa dan hannata mikewa, ta biyu kansa a kasa ya ce" ALLAH ya huci zuciyar Mai gida, zuciya ce irin ta Uwa ta dibi sarauniyar Dogon dutsi, In ba wannan ba minana a hukuncin nan? Ai maganar Allah aka bida a kulun ita aka yi, Allah ya huci zuciyarka" (Ai maganar Allah ake bi a kulun)

Uwar gidan sarkin yake kallo da kukanta da ya cika wajen

A nutse ya juya wajen Mahaifiyar yarinyar da aka kashe, wace ta fita hayacinta, ta fige, ta lalace, fuskarta du ta jeme, damuwa ta sakata ta zama wata iri

Kai ya cira ya shiga takawa cikin takunsa na kasaita bai ce da dayansu ufan ba har ya karasa wajen Mota zai shiga an bude ana ta yi masa addu'a ya dakata kasa kasa ya furta Dogari magana kamar haka"

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

0️⃣2️⃣

Kai ya cira ya shiga takawa cikin takunsa na kasaita, ba tare da ya cewa dayan su ufan ba har ya karasa wajen motar da aka bude tuni ana ta kirari irin nasa wanda ake binsa da shi da Adu'ar gamawa da duniya da mulki lafiya

Ja ya yi ya tsaya ya karra juyowa wajen daukacin jama'ar garin Dogon Dutsi yanai masu kallo irin wanda shi kadai ya san tarin bege, da kaunarsu dake zuciyarsa, ba dan komai ba sai dan kasancewar su yan kasarsa, sannan musulmi, duk da a wannan gari an ribanci jama'a da dama an saka su a harkar bautama wannin ALLAH, ama sai yake jin ciwonsu a cen kasan zuciyarsa harma da son sake tsayawa da jagoran garinsu ko za'a dace a kan abinda yake son fara gabatarwa?

Shi din yaro ne a cikin jerin sarakunan KASATA NIJAR, sai dai kuma shine ZAKIN SARAKAN kasata NIJAR

kasa kasa ya dubi dogarin ya ce" Idan na je da garaje, na kone baban wajen taronsu dan karra yardarsu wa doguwa, wace itama halitarta wanda ya halici samai da kasai ya yi....me zai faru?"

Kansa a kasa yake, yana matukar tatauna abubuwan dake bakinsa, Cheik na gefensa shima da nashi a bakinsa ama bai fada ba domin ba'a bashi damar yin maganar ba

A nutse ya ce" Kana da damar yin hakan Allah ya taimakeka, kana da damar konnewa dukan wani lungu da sako babu wanda zai maka fito na fito sai dai ya bi ta kasan kasa ko wanene!, Umarninka muke jira mu zartar ANNEMOKAL ITIBAL!" Ya karashe yana rage tsayinsa sosai kansa a sade

Kallon Dogarin nasa yake yi, na hannun damarsa,
Sai kuma ya yi dan murmushin da shi kadai ya san ya yi, ya dubi CHEIK a tausashe ya ce" KA FADA MIN GASKIYA CHEIK da abinda fiyayen halita ya yi, ka kwatanta min yadda zan yi koyi....domin na san ba isata ta kawoni inda nake a yanzu ba!"

CHEIK ya sauke ajiyar zuciya, domin dama zuciyarsa cike da tsoron kar dai a bada damar yake, dan ya yarda dari bisa dari cewa ba haka bane zai samar da zaman lafiya a kasar nan baki daya ba, daukan makami ba shi bane zaman lafiya, idan aka dauka aka tafi ya tabata wani sai ya shiga an kone abinda ya yarda da shi tare, dan ya samu cetonsa, subahanalah, idan hakan ya faru kuwa zai zamto ne an fara daukan makamai ana yakar junna......

A hankali ya gyara tsayuwarsa ya fuskanci UMUGHLUK ya ce" Shi tsafi gaskiyar mai shi ne, haka kuma sihiri akoy shi mugwayen sihiri kuwa,.........."
Chapter 2 · 0% Book details