← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 99

Sashe 51

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nutse ta fuskanceta ta ce" Hajia, ya dace zuwa yanzu mu yi abin fahimta, magana ta fahimta wace zamu fitowa junna a mutun, zan so ki gane, wannan hargagin da rikicin babu inda zai kaimu sai mu falasa kanmu, mu tonawa kanku da kanmu asiri, UMUGHLUK ITIBEL fa ba mahaukaci bane, ba makaho bane, ba kuma yaro karami bane, kuma ke kika raini abinki, kin fimu sannin idan ya fara fuskantar lamari irin na rashin yarda zai iya dora ayar tambaya a kai, yarinyar nan kuwa da kika gani abu daya zuwa biyu zai iya sakata ta tona lo meye kowa ya shiga uku, Hajia ita ba baiwa bace, iyayenta suke bauta, kin ga a dole yannayi na sada kansu a taka su ya sha bamban, sannan tanada ra'ayi nata na kanta, wanda ya saka take iya dubanka tace ba zata yi abu ba, ko bata son abu, to irin wannan abin yanna sakawa a sha wahalar zama da mutun, mutun mai ra'ayin kansa inaga ko a bariki yanada wuyar sha'ani, ba'a juya shi yadda aka ga dama, HAJIA tunda ta yarda aka yi wannan abu da ita inaga mu bata damar da zata aikata aikinta ta hanyar da ta ga zai fi gyarata, ba mu hannata sakat ba ta hanyar saka mata ido a dukkanin motsinta da neman hannata rawar gaban hantsi, ki sani, bata shigo gidan nan dan ta gaje ba ko dan ta kwace maki wajenki, idan kika yi hakuri gyaranku ne ku duka , watau in kika bata dama kika dauke kanki shiga jikinsu ba dan ta lalata mana aiki bane, Hajia na san baki taba ce mana da bakinki kina cikin tsarin gannin an kawar da shi ba, ama mu ba makafi bane, ba kuma mahaukata bane, bokon ce kawai bamu je ba, ama mun rayu da sannin me yake faruwa a tare da mu, ba gardawan yan kauye kara zube muke ba Hajia, haka kuma muna kishin kanmu, wannan gigi naki na daga hannu ki kawo kusa da mu matsala ne baba, idan ya zamto mun fara cin kanmu da kanmu ba zamu ji dadin tafiyar ba, shawarmu kanta na iya zuwa ba daidai ba, kin ga a haka ba dadi ko?"

Umma ta ja numfashi, idannuwanta da suka cenza kala da jikinta dake rawa na bacin rai da fargaba ta dubi HINDU ta ce" Ta yaya zan yarda fakat daya cewa ba ni take son zurmawa ba?, Kin ha abinda ta yi kai tsaye, abin mamaki komai bai ce mata ba?, ASADEEK yanada zafi sosai fa, ama take shige masa hanci da dukunkunne?, Ina fata ba kokari take yi idan ta aikata aikin ta sakayani a ciki ba, domin a yau ta saka na yi abinda ban taba yi ba a gabansa, watau hasala da daga murya!"

HINDU ta yi boyayen murmushi, a bayane kuwa ta sake kausasa yannayinta ta karra tabatarwa Umma cewa ta fa yi da aniya, in ba haka ba zata iya saka su a halaka baki dayansu!

Da wannan ta karra rufe Umma har ta mike ta tafi

Bayan ta tafi ta je dakin NADIRAH

Saman salaya ta sameta tana jan carbi dan haka ta zauna tana jiranta har ta gama ta shafa fatiha sannan ta mike ta karasa tana shagwabe fuska ta ce" Innata na kwari cikina da yawa, dubi tumbina ya cika makil walahi"

Murmushi innarta ta yi tana cewa" To ai na ga kin yi sallah zai ragu, tunda itama motsa jiki ce"

Jikin imnarta ta lafe tana sauke ajiyar zuciya

Innarta ta dubeta a sanyaye ta ce" Indina, me ya faru yau?"

NADIRAH ta dago a hankali ta zuba mata ido, sai kuma ta sakar mata murmushi ta mayar da kanta ta dora a hankali saman cinyarta
Muryarta a tausashe ta ce" Abinda na fahimta shine, muguwar yarda, kauna irin ta haihuwa, kusanci mai girma, yarda gaba da baya da ya dauka ya dora mata, bashi da darr ko dari dari a kanta, ransa nan take yake bacewa idan aka tabata, a kanta yana iya yi maka komai, domin yana kiranta da Mamah, mamansa, innata a uwa yake daukanta"

HINDU ta lumshe idannuwanta cike da tunani
Muryarta a raunane ta ce" In kuwa haka ne, juye mata aniyarta zai zamo aiki mafi wahala a gabanmu"

NADIRAH ta ja numfashi itama ta dago ta ce" Innata, jan aiki ne mai wahala, sai dai na fara hango matakin takawa dan karasawa cen, kanwarsa, watau Auta itace matakina, dan kuwa a soyayar tasa da Umma na hangi ta Auta ta maketa, da Auta zan jingina dan ya fara gane yarena, da ita zan jingina dan ya fahimci kumurcin dake tare da shi, domin Innata , Auta da kike ganni, hankalinta rasss, tana dauke da miki ne a tare da ita, da sharin matar cen, ta san yadda ta ci karfinsa har ya yarda cewa kanwarsa mahaukaciya ce, take rayuwa a haka, a zaman da muka yi, na fuskanci shi kadai ke makance da lamarin Umma, domin matarsama bata wani yarda da ita ba, ama kuma bata san girman sharinta ba, a tunaninta kiyaya ce irin ta wasu iyayen mijin, sai dai kashhh, wanda yakeda mahinmancin ne ya yarda da ita, sosai akoy aiki Innata, akoy gagarumin aiki"

Ajiyar zuciya Inna ta sauke, a hankali ta ce" in sha Allah, sannu sannu bata hanna zuwa, ita kuma wancen da izinin Allah sai mun kaita kass, sai halinta ya fito karara a gabansa, wanda take dannewa idan tana gabansa na tsayin shekaru, ba an fara yau ba?, Yanzu muka fara!"

Da wannan suka yi ta tataunawa da wasu shirye shiryensu hankali kwonce dan su cinma manufarsu!

___________________________________

Dawakai ne kwara biyar, tafka tafka irin ginanun nan masu ji da karfi da isa, sunna tafe sunna sakin huci da abubuwan adon dake jikinsu yana bada sautin cas cas cas

Su biyar din dake saman dawakan dukkaninsu manyan mutane ne masu daraja da fada a ji, a cikinsu UMUGHLUK ITIBEL ne a tsakiya, SHEIK a gefensa, sai rikakun yan siyasa, yan kasuwa, sannan jinnin sarautar a gefe da gefe sunna tafe a nutse tafia irin ta ziyara a asibitoci da sanyin safiyar yau, haka kuma sunna tataunawa kan babar Sallar BIANU da bugaje ke yi du shekara shekara

SHEIK ya dubi ASADEEK yana murmushi ya ce" ina fata wannan shekarar , iyayen talakawa zasu yi nasu taron da zaman gaisuwa?"

Linzamin dokinsa ya rike ya dan ja, hakan ya saka dokin tsayawa, sannan ya juyo barin Sheikh ya dan zuba masa ido

Kai ya kada sannan ya kalli gefensa ya ga sauran sunna dan zantawa ne, sannan dogaransu sun barbazu ne sunna tare mutanen dake son yi masu cincirodo

Kasa kasa ya ce" Madarata fa , madarar da kake yi min tofi kulun a jiya ban shata ba"

Da mamaki Sheikh ya dube shi ya ce"

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

3️⃣5️⃣

Da mamaki da kula SHEIK ya ce" Subahanalah, kar dai ka ce min zubewa ta yi?, Ya salam, aya, ka san jiyan nan irin adu'o'in tsarin da muka yi kuwa?, Dan abinda ya dan tunkaro mun nan ko wajen zamanka bi'izinillah daga jiya kulun sai mun masa zama na kansa, dan in mutun ya fi karfinmu bai isa ya ja da ayar Allah ba"

Talaicin da ya tuko shi ya saka shi gyada kai ya sake dan taba gefe da gefen cikin Dokinsa, hakan ya saka dokin sake dagawa suka ci gaba da ziyara, ziyara ce ta ba zata, ba a motoci ba, ba sanarwa, sai sun zo kofar wajen a bude masu, a ziyarar su babu inda basa lekawa, a haka suna kara bada talafi sannan sunna gannin sake na wasu likitocin ana rubutawa domin zai yi zama da su ne na musaman

Sai da suka gama suka fito dogarai tari guda sunna karra sakin hanyar dan a basu waje su wuce har suka karaso makabarta

Sauka suka yi a kafafuwansu suka shige, ADU'A sukaiwa mamata sosai sannan suka ga irin gyare gyare da sharar da za'a yi a makabartar, wasu kaburan sun bude kadan haka, wasu kasar ta baje dai da sauransu,nan ya bada umarnin a saka sanarwar ranar lahadi ana gayata dan a zo a yi gyaran gidan kowa, gidan gaskiya, du wanda yake da lokaci da talafin da ya samu ko menene ana maraba da shi, a saka a redio da TV, a haka har suka gama suka sake fitowa, abokan tafiyar tasa sai da suka masu rakiya har masarautar sannan suka tafi

Ya kasance saura su biyu ne a saman dokin sunna tafe cikin nutsuwa

ASADEEK ya sake tsayar da dokinsa ya kalli SHEIK ya ce" da ace zubewar nema ta yi da na san haka Allah ya hukunta ba rabona bace"

SHEIK ya dube shi, a tausashe ya ce" Me ya samu madarar?"

ASADEEK ya rintse ido, sai kuma ya bude ya dan kalli katon filin, da irin yadda wajen ya dauke sawaye tunda suka shigo, wa'inda ke tsaye du sun duka kawunnansu a kasa irin sunna masa gaisuwa da girmamawa ne
A dan kufule ya ce" Yarinyar nan ta dauke, ta sha, ita da Auta"

Da mamaki Sheikh ya ce" Yarinya?, Wace yarinya? Ko Hajia HUZNAH?"

Baki ya tabe ya ce" HUZNAH ai nutsatsiya ce, baiwar Allah ce, wannan bakuwar dai mai kama da aljannu, itace ta dauka ko kadan bata rage min ba"

Sosai SHEIK ya ji wani irin mamaki, hadi da dariya, bai san me yasa ba, abin ya dace ya bashi tsoro ko haushi? Aa shi dai dariya abin ya bashi, fuskarsa cike da yalwatacen farin ciki ya ce" Kwarai zan so na gaisheta Allah ya karra maka lafiya"

Ido ya tsurawa SHEIK, sai kuma ya ce" Bata da hankali fa, wace gaisuwa zaka yi mata?, Da ta zo ce mana ta yi sasannunku fa, na yi lati ne dan na mance dan kwalina, latin awa daya ta yi ta zo mana ta dibe albarkar alkyabarta ta kallemu tsai tace sasanunmu fa akaramakalahu"
Chapter 51 · 0% Book details