← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 99

Sashe 62

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakatawa ta yi da maganar tana sake dubansu, gannin Inna ta fuskanceta sosai tana kallonta, ita kuwa NADIRAH ta yi dan tsai alamun tana sauraronta ta ce" Shi din uba ne a garemu, ya kasance mai kwana da damuwarmu a zuciyarsa da kuma aikinsa........, Bari ki ji, walahi shi din bango ne, majinginar talakawa ne,, majinginar masu da shi din ne, Abah muke kiransa, yaro da tsoho"

A hankali ta fan juyo ta zuba mata ido, Muryarta ciki ciki ta furta" Yaya kuke kiransa Aba bayan bashi da shekaru sosai a kansa?"

Matar SHEIK ta yi murmushi ta ce" Idan kika ga an yiwa ja gaban wata tafia sunna ko wani iri ne, ki dauka cencenta ta saka ya samu sunnan, kuma sunna ne da zai iya fitowa daga bakin talakawa, watau ba daga bakin masu yi masa fadanci ba, shekarunsa basu kai wajen da SHEIK zai duka ya kireshi ABAH ba, ama ko kwanan gobe Humaira Auta takan ce da Sheikh tanna so a kawota wajen Aban SHEIK, a tunaninta mahaifi ne a wajensa domin bakinsa kan girmamashi a bayan idannuwansa ta hanyar kiransa ABAN TALAKAWA, "

NADIRAH ta tabe bakinta a hankali ta sake juyawa

Matar SHEIK bata yi kasa da gwuiwa ba ta dora da fadin" Dalilin da ya sakani dauko maganar nan, dan na roki alfarmaa ne, dan Allah ki kasance cikon farin cikinsa ko yayane, ki yi hakuri idan har na bata maki "

Shiru ne ta sake yi masu, hakan ya saka Innarta budar bakinta da ya yi mata nauyi kadan a hankali ta ce" In sha Allah, ita fin zata zamto daya daga cikin abinda zai kwontar masa da hankali, baki bats mats rai ba, asalima na ji dadin hakan, Allah ya biya, shi kuma Allah ya dafa masa"

Da amen amen Matar SHEIK ta amsa sannan ta mike dan tafia

Har kan kofar Inna ta rakata tans faman godiya

Aa hankali tas dawo ta zauna tana duban kayan, gaba daya ta rasa me zata ce, kayan nan ya zamaa wajibi ta fitar da su cikin sirri tun kafin Umma ta san da zamansu bale har taa nemi sannin dalilin da ya sa aka bata su, gefe daya kuma yannayin y'arta na damunta matuka

Muryarta a raunane ta ce" Ama, ina cewa dazu muka gama maganar cewaa kin amince, zaki karra yin hakuri kadan har mu gaa karshen abin nan ko?, Ki duba ki ga tarin dukiyar nan, shin bai cencenci ki yi masa godiya da namijin kokarinsa ba?"

Muryarta a mugun raunane ta juyo ta ce " Innata, Innata na yarda fa, nace na amince zan ci gaba da kwatanta bin hanyar da zai fahimci abinda ya kawoni fadar nan, na ce na yarda a gobema zan je na yi zaman da suka saba, ama Innata............"
A hankali ta lumshe idannuwanta tana nuna kayan muryarta na mugun rawa ta ce" Innata ama bana tare da irin wannan abubuwan, kayan nan bana so, ban zo dan su ba, asalima ya shiga hurumin da ba nashi bane, a kan me zai lalata min tsarin rayuwata???????"

"Bakida hurumin da ya fi shi!, NADIRAH bakida tsarin rayuwar da ta fi tasa, " Innarta ta fada tana tsareta da kakausan kallo

Numfashi taa fitar mai zafi, sannan ta ciciba a hankali ta mije tsaye tana jin sosai jikin nata da karfi yanzun

Muryarta a rine ta ce " yanada masu sonsa, yanada mai matukar kishinsa, ta isheshi rayuwa, su suka saba da rayuwar nan, ni kam ina jina tamkar a kurkuku, wannan daula bana jinta na fi jina a kule a waje guda, ni ba matar gidan sarauta bace, inada nawa zabin nima, idan har na dube shi....dan kun isa da ni ne!"

Tana kauwa karshe ta yi gaba ranta na sake yi mata kunna

HINDU ta rasa me zata ce, walahi idan akoy abinda ke matukar dagaa mata hankali wannan rikici da take hangowa a tatare da y'arta

Kayan nan ta mayar ta shiga shigar da su dakinta tana tura su karkashin gado kafin ta dawo ta kule ko'ina ta koma dakin NADIRAH, ama sai ta tarar ta yi barci, dan haka ta koma nata dakin ta daura alwallah ta haye saman salaya dan kaima mai duka kukanta, ta san karfinta ko dabararta basu isa su bata abinda take so ba, zata karra kaima wanda ya isa ya gyara batatacen al'amari kukanta , shi zai gyara mata cakulalen rikicin nan

___________________________________

*WASHE GARI*

Kamar yadda ta saba shigowa a lati, yauma hakan ce, haka kuma tau a jikin nata babu alkyaba kwata kwata, wani lafcecen hijab ne ta saka har kasa mai hannaye ta fitar da hannayenta sannan ta daure abin daurewar a bayan kanta bayan ta saka baban abin daure gashi, kanshi ne dai take bazawa mai yawan gaske , hankali Kwonce ta ratsa tana tabe baki sanadiyar gannun sun zube kasa kowane kanda a sade ta tabata dan bata da alkyaba ne ba zasu iya yin ido hudu da ita ba

Maimakun zuwanta a lati ya kasance sabo a wajensu, sai bai kasance din ba, asalima hijab din dake jikinta ya saka matan zuba mata ido cike da mamakinta har ita da kanta HUZNAH ta kasa dauke dubanta a kanta

Dan tsai ta yi tana kallon kujerar da HUZNAH ke sama, wace take zama ce kwana biyun nan, wato ta kusa da shi sosai

Kanta ta dauke ta karasa ta ja wata kujerar ta zauna tana dan dago idannuwanta daga lumshe su da take yi muryarta cen ciki ta furta" Sannunku da hutawa"

Shiru ne ya biyo bayan tambayarta, ta kai dubanta wajen Auta ba alamun damuwa da rashin amsa matan kasa kasa ta yi mata kallon sannu fa, sannan ta maida dubanta wajen Umma da lamarin yarinyar ya fara tsoratar da ita kasa kasa ta dan sakar mata murmushin da yake a saman lebe ne kawai sannan ta kai kan HUZNAH
Duban ido cikin ido suka yi tta yatsina fuskarta wanda kiri kiri ana kallo domin a bayane ta yi sai kuma ta sake maidawa kan wankakun farare tas din plate masu wani tsararen launi a ajiye da rantsatsu cokulai biyu a samansu masu ruwan golding an dan nade su da farin tissu abu dai a tsare masha Allah, sam bata yarda ta dubeshi ido cikin idon nan ba tunda ta zo, hasalima gabanta ke yankewa yana faduwa, kuma zaman da matarsa ta yi a kusan shi ya mata daidai domin koda bata yi haka ba itama yau ba zata iya zama a hakan ba

Abincin ta zuzuba cike da isa irin tata itama, harda plate din Nadirar sannan ta koma ta zauna ta dauki cokalinta ta fara ci a hankali

Idannuwanta ta lumshe sanadiyar goshinta da ya dauki gumi na zufa kamar zafi ke hura dakin bayan sanyin AC ne ke tashi

A jikinta take jin kaifagun idannuwa a kanta, a yannayin kallon mutanen da take yi kuwa sai ta ga babu mai kallonta, ta yiwu wanda bata gaisar bane yake kallonta

Murza gaban goshin nata ta yi ta dan dago idannuwanta ta sauke a saman hannayensa , a hankali ta murguda bakinta sannan ta gyatsine hancinta ta mayar da dubanta gefen Auta tana kallonta

Idannuwansa ya lumshe hadi da yin murmushi boyaye sannan ya sake duban kalar abincin da aka yi yau, sai kuma ya dubi Auta dake ta faman tsakura ta kasa ci

A hankali, furucinsa a nutse ya furta " Bakya son abincin ne?"

Kasancewar magana ce ya yi bayan ya dauke dubansa a kan Auta ya saka su kallonsa su hudun baki daya sannan ukun suka dawo da dubansu kan bakuwar cikinsu, domin itace wace t zo masu da firgitaten lamari , kowane yana tunanin da ita yake

Da mamaki HUZNAH ta sake dubansa gabanta na yankewa ya fadi da dan karfi, shi kuwa sai da ya dan yanka steek din dake gabansa ya saka kadan a bakinsa ya dan tauna ya hadiye sannan ya dago idannuwansa ya zuba dubansa a fuskar HUZNAH da ta tsatsareshi da ido

Idannuwansa ya lumshe mata , sannan ya kkai dubansa kan fuskar NADIRAH
Ya taki Sa'a itama a lokacin kallonsa take yi, hakan ya sa suka yi ido hudu da junna
Faduwar gabanta ya sakata jin wani irin rauni ya taso mata a cen kasan zuciyarta da kuma gangar jikinta, tana kallonsa jiki ba karfi shi kuma ya saka kaifafun dubansa a kanta, idannuwan da a jiya ta ringa kallo a matsayin wani bijimin zaki, lebunnan da suka yi ta damkar kan mamanta da dogon karan hancin da ya yi ta saukar mata da zazafan nishi a wuyanta

A hankali ta dauke dubanta tana tare hancinta da ta ji wani lumlumlum da sauri , watau wani dumi na neman biyowa ta hancin nata wanda ta yi tunanin ko tsinkakiyar majinar nan ce? Ta saka hijab dinta da sauri tana jin kanta na sara mata, wannan wani irin kallo ne yake yi mata haka?, Me yasa take ji kamar zata summa dan faduwar gaba?

A hankali ya dauke zazafan idannuwansa daga kanta ya maida kan Auta da ta yi sumnar zaune tana kallon ikon Allah, fuskarsa a sake, sannan a birkice ya ce" Bakya son abincin ne?"

Wata ajiyar zuciya ce HUZNAH ta saki da ta fahimci ba da BAHIJA yake ba, Ummama ta fauke dubanta ta yi kamar bata ga komai ba tana jinjina karfin halin NADIRAH

Auta ta dan kalli madarar dake gabansa, wa'inda yau abu biyu ne a ajiye a shake da madarar sannan ta sada kanta ta kasa cewa komai

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

4️⃣4️⃣

Ba edditing fa

Madarar ya kalla shima, a hankali ya sake fadin" Dama kina son madara ama baki taba nuna min ba?"

Umma ta yatsine fuskarta, a duniya idan ka ji yana magana a tausashen nan yana ta magana dama da mutun biyun nan ne, wancen mugun malamin sai wannan mahaukaciyar kanwar tasa

Wani murmushi Auta ta saki tana dubansa da kula ta ce" Abahna, ina son madara sosai, la manta da ran marigayiya ana kawo min madara sosai?"
Chapter 62 · 0% Book details