← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 99

Sashe 46

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata tashi kallonsa a zabure ba sai da ta ji ya ce" To ke uban wa ya aike ki marin yar Fadimata?, Ku walahi kun cika neman jaraba, su fa basa dukkan ƴaƴansu, a laluma ya dace ku bita ba da masifa ba, sam baku iya cin ribar duniya ba kunna abu kamar mahaukata, ke baki tambayeta ta gwada maki gaisuwar ba kika dauketa firkyau firkyau kuka tafi?, Tunda kuka kwana ku dukanku har yanzu bai neme ku ba lafiyar ce, ki tashi kawai ki je yadda kika saba kicin da sauransu tunda kece da ikon komai matarsa hoto ce tana labe!, Zan gani zuwa jibi za'a kawo maganin sai ta gani in ta daidaita lokacin ta ga ya dace kawai ta bada masa, ke ko shaka masa ne ta yi a wuce wajen"

A haka suka yi salama, gombiya na yi masa wani irin mugun kallon da ya sakashi rafka tagumi ya ce" Wani lokacin sai na ga kinai min kallon nan kamar zaki kasheni ki huta walahi"

A ranta ta ayyana ' Dama inada wannan damar, da ina mai tabatar maka ba zaka kara minti daya ba'

A bayane kuma ta ce" Kai kake bani mamaki, ina tsoron idan Allah ya tashi kamaka ka tube zirr ka bi Fadime da gudu, Allah shi kyauta" tana gama fada ta juya ta kama hanyar ficewa, shi kuma ya daga murya yana fadin" Ba amen ba bilahilazi, yar bakin ciki ni da ita ai yar daka ce ba yar hanya ba, sai dai ki mutu!" ( Wannan shine huldarsu, fahimtarsu, cin kansu, Allah ka sa mu dace)

_____________________________________

Da yamacin ranar ta samu iso zuwa bangaren HUZNAH, ziyarar da UMMA bata ji ba kwata kwata, sai bayan isarta labari ya je mata daga bakin masu kai mata tsegumi, watau daidaikun mabiya bayanta

Tarba ce ta salu ta gani ta fada, tarbar da ta bata mamaki, haka ta zuba ido tana bin yadfa suke gabatar da huldarsu zuciyarta cike da mamakinsu baki dayansu

Bayan sun gaisa, su biyu ne a saman kujerun, sai bayin dake duke a kasa kowace kanta a kas , ba'a basu damar fita ba, dole zasu zauna ko me zai faru ya faru a gaban idannuwansu da kuma kunnayensu

NADIRAH dake zaune, tauna kalmar da aka ce ta zo ta bada ta hakuri da abinda ya faru jiya take yi a harshenta, sai dai sam ta rasa ta yaya zata fara, domin a aunawarta bata ga menene girman laifinta ba, hasalima bambancinta da su shine bayar da hakuri a lokacin da ba'a aikata laifin komai ba

Bayin nan kwaya hudu take kallo, kalmar dake saman harshenta ta samu fitowa a hankali ta furta" Ku bamu waje "

Sai dai bayin da aka ce nata ne kadai ta ga sun mike sun fice bayan sun yi mata fatan a yi hira lafiya

A nutse ta dora shemamun idannuwanta saman biyun da suka rage, wa'inda daya ce hasalin baiwar HUZNAR, dayar sunnanta dai ne baiwarta ama dukkan motsinta tana kaishi ne gaban UMMA

Kallon da take yi masu, da hanna kanta dura masu ashariya gannin jam'u ta yi furucinta ama biyu basu basu wajen ba ya sakata muimui da baki tana karra kausasa dubanta a kansu

Da yan yatsunta, ta masu alamun su fice, wanda hakan ya ba NADIRAH mamaki ainun, watau an nuna mata ga yadda ake sarautar ko? Sai dai kashhh, bata san ko a tsuman ranta ba domin ba wannan ne a gabanta ba

Sunna fita ta dago dubanta ta dora saman Huznah
Matar dai ta girmwga gaskiya, dan a yadda ta kiyasta zata kai shekaru talatin haka, ko da doriya, ama gatan wata zullu abinta ba'a cewa komai
Akoy fa kyau dan kyau sai baranci....ta ayana a zuciyarta

Kai tsaye, ta ce" Me yasa, a matsayinki na wace ta isa ta saka, ko ta hanna, kike zaune bakya shiga kicin ki girkawa mijinki abinci, ko baki iya ba?"

Da sauri HUZNAH ta dago da idannuwanta, duba ta sauke a fuskar NADIRAH, wace take yiwa kallon BAHIJA,
Sai ta ji kamar zaginta yarinyar ke son yi, ko tana so ta nuna mata cewa ita bakuwar jiya tsal har ta kai wajen da zata iya nuna mata son mijinta? Ko tana so ta nuna mata bata iya girki bane?, Sai ta samu kanta da tsare NADIRAH da ido, sakon da aka kawo mata an ce mata ne zata zo gaisheta, da bayar da hakuri, ama a zuwanta ko gaisuwar ce mata ta yi sannu fa da hutawa tanai mata wani kallo kamar ka tile kayan wankin nan, a tunaninta ko dan girmarta da ta yi ai ya dace ta girmamata ko?, Ko dan da ake cewa kishiya kishiya ce zata yi kishi da ita?, Ko nuna mata zata yi kusa ta fi kusa ne?, Ko kuwa tana so ta nuna mata ita yar sarauta ce?, To ai itama yar sarautar ce, idan bata da labari bara ta sanar mata

A nutsenta ta ce" Mahaifina, shima sarautar ba cira ya yi ba ALLAH ya dattar da ke da tsufa a bisa girman darajarki BAHIJA"

NADIRAH ta dan yi tsuru, gaba daya bata gane ina ta dosa ba, to ana zancen girki me ya kawo maganar mahaifi? Allah ta tuba itama nata uban ai sarkin ne, na dogarai,kowani sarki kuwa ai sarki ne a fadarsa wa bilahilazi!

Baki ta tabe, ta ari yaren nutsuwar, domin ta kula idan ba halayar da Allah baya so ka dan aro ba ba zasu fahimceka ba, watau girman kai, ta yafa , a nutse ta ce" Allah ya huci zuciyarki....."
Ta ajiye zancen tana tabe baki da tunanin me aka yiwa zuciyartama?

Ta sake fuskantarta ta ce" Ban zo gidanki, fadarki, duniyarki, balbalin mijinki, dan na koya maki tafiyar da dukkan abinda ya dace ace naki ne......., Ki gane ban kuma fada dan na hadasa husuma bane...
.., kawai gani na yi shi sarki mijin sarauniya ne, ba mijin makaraban gidan sarauta ba"

Ta ajiye maganar tana wana manyan idannuwanta zuwa tsarin falon mai masifar kyau da daukan hankali

A hankali ta mike tsaye , sannan ta dakata ta juyo tana kallonta ta ce" komin jimawar zaki a dawa, cikin kogo a boye, ba zai hanna kuraye wadaka da kai kawo ba, idan har ba giga ya yi ba, sunnansa na loko , fili kuwa na kuraye ne, Yin girki ba laifi bane a tunanina, idan har ba iya sarafa abin bane ya zamto gagarare a gareki Allah ya karra maki lafiya"

Daga haka ta sakar mata malalacin murmushi sannan ta juya ta fice daga falon

A rikice HUZNAH ta mike tsaye tana kallon hanyar da NADIRAH ta bi

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

3️⃣2️⃣

A rikice HUZNAH ta mike tana bin hanyar da NADIRAH ta bi ta fita da ido

Daidai nan Bayinta suka dawo, ita kuma a lokacin ta shiga kai kawo tana kai yar yatsarta karama ta dantse a bakinta cike da jin radadi da rukuki a zuciyarta

A ranta ta shiga ayana magana kamar haka' Kin zo gidan nan ne da nufin takani?, A tunaninki sangartaciyar inna nake wace ke ci ta bar kwano a nan yashe?, Lalle ba zan yarda ki zo gidana ki sameni da mijina ba ki fara kawo min tsare tsare, ni nan ni zan fara yiwa mijina girki kuma zaki samu gayata a yau ba sai gobe ba!'

Fuska a hade ta bada umarnin ko me ake yi a je a sanar a baban kicin na bangaren mai martaba zata shigo kicin da kanta

A zabure yar rahoton Umma ta dubeta, sai kuma ta sada, a tausashe ta ce" Allah ya taimaki uwar bayin Allah, me ya hada ki da girki? Fatarki ai ba ta shiga kicin bace, sannan Allah ya karra maki lafiya kin manta Maman Ja gaba ce keda wannan alhakin?"

Samun kanta ta yi da tsare matar da kallo, idan har tana iya irgawa a gidan nan ai komaima maman Ja gaban ce keda alhakinsa, ciki harda hurumin da ya dace ace nata ne ita matarsa, ya dace ace Umma tana kula ne da abinda ya shafi abincin bayi, ta bar mata na mijinta ita ta kula da shi, ama ya zamto har mutanen da suke bayi a gareta sunna neman yi mata katanga da haka dan ta zubar da hakan ta yi watsi da shi wa wasu? Har ake ce mata fatarta ba ta shiga kicin bace dan aikata aiki mafi hatsari da kaiwa jiki irin na abincin mijinta?

A dan kausashen da basu saba ganninta ba ta dubi matar ta ce" Jayaya kike yi da umarnina?"

Da sauri ta sada kai, ta sake dukawa tana mai neman afuwa

Da umarni ta ce" ki rike magiyarki!, Ki maida hankali kan abinda na saka ki, sannan ki je dakin sako a rubuta takardar gayata cin abinci a falon mai martaba, karfe takwas na dare, a turawa SARAUNIYA BAHIJA!"

Daga haka dakinta ta wuce dayar ta bi bayanta da sauri dan fitar mata da dukkan abinda take bukata

Ita kuma a lokacin tana fitowa sai da ta dokawa Umma waya ta sanar mata cewa wai HUZNAH ce zata zo Kicin na bangaren Sultan,
A lokacin kuwa Umma bata jima da baro bangaren ba tunda aka sheda NADIRAH ta dawo bangarenta, ta zo tana son jin dalilin da ya sa Nadirar har ta fito ta je wani wajen ba da izininta ba

Innar Nadirah kam, uffan bataa ce ba, har Umma ta gama maganarta, hakama NADIRAH kallonta kawai take yi har ta ajiye maganarta, a nan ne ta samu kiran nan wanda ya kusan sumar da ita

Da tuhuma ta dubi NADIRAH ta ce" Shekara tara kennan yarinyar cen na masarautar nan, bata taba cewa zata shiga ta yi masa girki ba sai yau da kika je bangarenta? Me kika ce mata?"

Da dan kosawa Nadirah dake bale dan kunnen kunnanta ta dubi Umma

Lalle matar ta gama samun waje ne gaba da baya, ya zama wajibi kuwa ta bita a hankali har ta durmiyata a cikin ramin da ta haka da kanta
Chapter 46 · 0% Book details