← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 99

Sashe 67

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jajayen idanuwansa da har jan ya kafe ya fara yin duhun baki ya zuba mata, muryarsa a jigace ya ce " na ce ki je ki yi sallah, idan kin gama ki huta zan tashi nima na shiga wanka"

A hankali ta sake shi ta dan matsa tana kallon yadda ya mike a hankali ya ja abu ya rufe jikinsa sannan ya nufi bayi da kyar yana wata irin tafiyar da take tambayar kanta a haka yaya zai iya tafia masalaci?

Rufowar bayin ya sakata sauke ajiyar zuciya ta mike jiki a sabule ta nufi wajen alkyabarta ta mayar ta sake juyowa ta kalli bed din sannan ta fice ba tare da ta gyara ba, domin ba su ke gyaran komai ba akoy masu yi (🤔 harda gadon da kika gama baza sirrin nan?)

Da kyar ya iya yin wankan sama sama ya dauro alwallah ya fito

Sallar kanta da kyar ya iya gabatar da ita, bale idan zai kai sujada sai ya ji kamar mararsa zata fashe biyu, kunnayensa na jiyo masa adu'ar masalaci watau har an gama sallah an yi karatu ana shafa fatiha ana ta yi masa adu'o'in alkhairi

Idannuwansa ya lumshe ya kama abu ya mike da kyar ya nufo hanyar fitowa

Sauka yake yi ko rawani bashi da shi a kansa, daga shi sai doguwar rigarsa da wandonta sai carbin dake rataye a jikin yan yatsunsa ya ringa sauka a hankali har ya saukowa hankali kwonce ya nufi boyayiyar hanyar falonsa ya bude ya shiga ratsawa yana dubawa har ya karasa kofar nata falon sannan ya dora yatsarsa wajen budewar ya cire lock din ya murda abin budewar ya dan bude shi kafin ya dakata ya shiga dan bubugawa yana sake jinginar da bayansa da garun

Daga cikin falon kuwa, zaune suke Auta na kallon yadda Inna ke yiwa NADIRAH gyaran kai, bayan sun gama sallar asubahin Innar ce da kanta ta je ta dora masu abin kari sai kuma tace su zauna a falo su sha hirarsu, sai daria take sha idan Innar ta yi magana, tana matukar son sannin wacece innar? Ama ta kasa tambaya, hasalima tun jiya da suka karaso bangaren nan suka dan taba hira da ta so tafia fakat NADIRAH tace ba inda zata je ta yi zamanta a bangarenta yaya zata iya yin barci ita kadai a nata bangaren bata jin kadaita ne?, Ta daina kadaice kanta ita kadai ba kyau, sai gashi ta kwonta daki daya da wannan mata Inna sun sha hira da kayan dariya kafin su yi barci, asubahi na tashi kuma ta tasheta suka yi sallah suka taba karatu sannan suka fito dan dora abin kari, domin yanzu haske har ya fan fara fitowa kadan kadan, gaba daya jinta take wani iri, wani banbarakwai, ta gaza sakewa ta sha hira da dariya ne dan wannan lamarin kam bako yake a rayuwarta

Sake bugawar da aka yi a hankali ya saka su juyawa su biyun

Juyo da kan nata Inna ta yi ta hanyar jan gashin hakan ya saka Nadirah furta" Wayo kaina innata"

Inna ta ce" Ke dilla juyo, ana maka kitso kana kauce kaucen kai da iya iskanci, ke ba za'a taba maku kanki ba ko?, To sai na caje maki"

"Innata kamar ana buga wancen hanyar fa, dama a bude take?" NADIRAH ta fada tana dago kanta ta kalli innarta

Auta kuwa da sauri ta mike tsaye tana kallon hanyar ta ce" Dama wani na iya bude kofar cen banda Abahna?, Idan a rufe take da ky ta ciki Abahna kadai ke iya budewa da yatsarsa kar aje wani abu ke faruwa a masarautar?"

Inna da sauri ta mike tana daura zanninta a saman cikinta ta kalli hanyar sai kuma ta kalli Auta ta ce" Yar nan ban gane wani abu na faruwa ba? Abu irin na a tardomu a kashemu?"

Auta ta yi tsuru tsuru, hakama Innar NADIRAH

Nadirah ta kalli Auta ta kalli innarta itama tana jin hankalinta na neman tashi

Zata yi magana ya dan miko hannunsa kadan ya rike abin kamawar ta ciki kadan sannan ya janye, hakan ya saka Auta zarro idannuwanta ta ce" Abahna ne"

Gaban NADIRAH sai da ya kwonci kwonci ya rufto kasa, innarta kuwa ta dake kallon Auta ta ce" Makashin? Waye Abanki wai? Ki bude baki mana kina magana a kuryar makogwaro"

"Inna wai ASADEEK take nufi" NADIRAH ta fada muryarya a sanyaye sosai

Innarta ta zarro ido, sai kuma ta kame baki ta karasa kusan NADIRAH ta rankwasa mata dankwashi kasa kasa ta ce" Dan ubanki ban hannaki kama sunnan nan ba?, Kina nufin shine a cen?"

NADIRAH ta dora hannunta saman kanta ta kwashashabe fuska ta gyada kanta

Innarta ta tafa hannu ta duke kasa da hannunta ta tura NADIRAH kasa kasa ta ce" Jeki jeki yi maza jeki"

NADIRAH ta turo baki tana kallon innarta ta ce" Ni kuma Innata?"

Innarta ta sake dora hannunta a gefen fuskarta tana salalami kasa kasa sosai ta dubi Auta da abu biyu suka tsaye mata a rai, muguwar dariya da kuma tunanin me yake damun yayanta? Dama yana zuwa nan da kansa ne?, Ta ce" Ke kin ga wani bakon islanci ko? Tambaya take yi wa zai je, ce nai mata ni, nace ni Indi, in baki je wajen cen kika ji me Babanmu ke so ba sai na ci abinda habu baya so ina fada a gidan nan !"

Da sauri ta nufi hanyar tana matsar kwallah, ta karasa ta bude tana leka shi suka yi ido hudu da junna, fuskarsa ta zama jajajir, yannayinsa ya zama abin tsoro, lebensa kuwa ya karra yin ja yana walwali , idannuwansa kuwa sam badu da dadin kallo

A hankali ta kalli hannunsa da ya miko mata yana karra shanye dubansa , hannun ya karra girma fiye da da, yannayinsa ya taurara sosai a idannuwanta, jijiyoyinsa sun yi birde birde, sai ta ga ya karra yi mata girma fiye da jiya da dare

Da sauri ta juya da nufin guduwa, dan sam sai ta ji wannan yannayi kamar za'a zalinceta ne

Dan dagowa ya yi ya damko bulememen hijabinta ya yi baya da ita, a dole ta dawo ta daki kirjinsa har sai da ta ji tsoro domin buguwa ta yi sosai a bayansa , hakan ya sa ta dago da sauri ta juyo ta dago dubanta tana kallonsa, muryarta na rarabuwa ta ce " Me, me yake faruwa? Me yake damunka?"

Janyota ya sake yi jikinsa, a hankali ya rungumeta sosai a jikinsa, kanta dake bude an kame gefe, gefen a barbaje yana fitar da kanshi man kai na mata ya ringa sinsinawa a hankali, a hankali , sai kuma ya saketa ya dago fuskarta yana kallo irin yadda fuskar tata gaba daya ta fara daukan ja alamun tsoro take ji ko kinsa take ne oho

Tana jikinsa ya shiga nufar nasa bangaren da ita, du yadda ta saki jikinta yake tafe da ita dan ya saketa watau ta ki taka kaffafuwanta dan ya barta kar ya tafi da ita sai ta ji idan ya daga kafarsa du irin yadda jikinsa ke mace da ita yake dagawa har ya karasa kofarsa ya bude ya shiga da ita sannan ta ga ya dora yatsarsa a kai watau ya yi block din kofar har sai idan shine ya bude da kansa , dama babar kofa ba za'a budeta ba sai idan ya bada damar haka, sai ta ji hankalinta ya fara tashi har ta fara yi masa tambayar me ta zo yi ne? Kitso fa ake yi mata, kar a ga bata dawo ba

Idan ya tankata tabas dakinma ya tankata, a haka har ya karasa dayan dakinsa da ita ya bude ya shiga ya mayar da kofar ya rufe

Tsaye take tana kallon wajen kofar har haske ya mamaye dakin

Da sauri ta ringa kallon yannayin dakin sai kuma ta juyo inda yake dan ce masa dan Allah ya bude mata mana ta tafi
Idannuwanta ta wara tana kallonsa cike da faduwar gaba
Da sauri ta sada kanta, watau ta sada dubanta tana jin kamar zata summe a wajen

Idannuwansa ya lumshe a hankali ya yi murmushi yana kallon yannayinta, kasa kasa ya ce " Ba zaki kalleni ba?"

Cike da matsananciyar kunya ta kasa koda daga kan bale ta iya bashi amsa, a hakan dan bashi da riga ne, domin da wandonsa a jikinsa

A sanyaye ya shiga gabatar mata da kansa, ba da tsawalawa ba, ba kuma da fin karfi ba, sai dai idan da ace zata iya dago kanta ta dube shi ido cikin ido da ta gane a halin da yake ciki yana iya hadiyeta danya

Muryarta da nauyi ta ce" Dan Allah kar ka ringa sabawa da ni......., Ka daina tabani ka ji?"

Sake kure fuskarta ya yi da kallo, har sai da ta ji shirun ya yi yawa ta dan dago dan gannin ko ya daina matsota har ya kawwota kusa da bed din ne?
Tana sauke idannuwanta cikin nasa gabanta na bugawa shi kuma a lokacin ya hade bakinsa da nata damatsunnan hannayensa har motsi suke yi su kadai
A yauma NADIRAH ta ga yaren Kato, yare marar taushi , domin taushin na dan lokaci ne a matsayinta na farin shiga, sai dai shima farin shigar ne, idan ya fara burinsa ya samu nutsuwar da yake so
Chapter 67 · 0% Book details