Sashe 48
Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wajen da ake sarkafe kaya idan a shigo ta karasa, hankali kwonce ta cire Alkyabarta ta rataya a jikin abin ratayawar, wanda haka sai da ya saka HUZNAH kwarewa da abinda ta saka a bakinta ta dan shiga tari kadan tana sin cire idonta a kanta ama dan jaraba tana karra kallonta
Kasa kasa ya dan dago da dubansa daga abincinsa ya dan kalli HUZNAH
Sai kuma ya kai dubansa inda take kallo tana fan tari hadi da kai kofin ruwa bakinta
Samun kansa da zubawa yarinyar ido ya yi na yan dakiku sai kuma ya dauke kansa a ransa ya ayana' Ta tabata, yar daba ce yarinyar nan, ko irin yan duniyan nan rikaku'
Tana murmushi itama a nata ran tana ayana' Haka nake so, so nake na haukataki, ki yi zaman aure da mijinki mai sunna zaman aure kafin na tatara tsumakaraina na karra gaba Alkur'an, ama kina abu kamar wata bagidajiyar da bata da ilimin adini? Ilimi ai haske ne, kuma ko ni da nake kauye a wannan fannin na san me nake yi sarai!'
Bata tashi idasa neman rikita masu lisafi ba har Auta da ta karra zarro ido, Uwa uba Umma, matar dake bata mamaki, zaman cin abincin dare da ya dace ace ya yi daga shi sai matarsa a dakinsu abinsu aa, ga wata mai zarro ido kamar mai farfadiya, sai wannan rusheshiyar mata mai ruwa da munafukai a saka su tsakiya, ita kuma matar kai a kasa uwa tsohuwar algunguma a gaban mijinta? Uhum, sam basu da tsari gaskiya
sai da ta karaso facing din da yake ta dan kama gefe da gefen rigarta, ta dan baje tsayuwarta kadan sannan ta saki dayan hannunta tana murmushi ta yi wani yannayi da hannun da muryar murmushi tace" Barka da warhaka Aban su Datawa......"
Yanzun kam Umma ce ta ji miya miyar zata sarketa, a dan rikice ta cire dubanta daga kan Nadirar ta maida kan abincinta tana yin iya yinta dan hanna kanta sumewa da tashin hankalin da take kallo
Auta da du take a hali na rashin jin dadi dan an sakata cin tuwo mai nauyi bayan ita bata cika son tuwo irin haka ba , asalima nonon sanuwar dake cikin katon flask na yayanta take so a zuba mata, ama Umma tace wannan zata ci dan maganinta sai ta samu kanta da sakin boyayan murmushi tana sake satar kallon yayanta da abin al'ajabi irin na mahaukatan zamani ya saka shi dafe haba a bayane, duda rawaninsa iya bakinsa da habarsa kadan ya bayanar yana kallon rikakiyar yar gajaliyar nan
Dagowa ta yi tana fadin" Kai kuguna"
Sai kuma ta karasa ta kalli HUZNAH ta sakar mata murmushi a takaice ta ce" Sannu fa"
Sai kuma ta kalli Auta itama ta zarro mata ido yadda take ta zarro mata ta ce" Ke kuwa gyara dubanku mana haba"
Sannan ta sake kallon Umma, ta sakarwa Umma murmushi wace idannuwanta tamkar zasu fado dan kallo itama a takaice ta ce" Sannu dai Ummanmu"
Kujera ta ja ta zauna tana sauke numfashi irin ta sha aikin nan sannan ta ce" Walahu nake fada maki aunty dan kwali na nema na rasa karshe dai haka na taho kar aje na yi lati
'Latti? Dan kwali? Ya Allah ka sakani gane wannan mata tun kafin ta kasheni, wannan wace irin mace ce? Wani lati bayan sai da sarki ya zauna ta zo?, Wani dan kwali a tarin suturunta?, Ta rasa me zata saka sai wannan rigar?, Ta zo ta mana gaisuwa kamar sa'o'inta? Koda yake shima sarkin ga yadda ta gaishe shi uwa uba Umma?, Ya Allah menene wannan ne? Wacece wannan matar ne? Allah ka shiga lamarina da ita ya Allah ka dorani saman kanta kar ta rikita min zamana, ni dai banida matsala da ita, ama sai wani haroni take yi!' HUZNAH ta ayana a ranta sannan ta dauke kanta bata ce mata komai ba, dan baya so ana saman table a ringa yawan magana haka
Baki NADIRAH ta tabe, ita fa ba fa za'a yanka mata baki ba har ya zo yanai mata tsami dan bakin hali da rainawa kai wayo ba walahi, tsaf bakinta na magana ne Allah walahi
Abincin take kallo
Kaf abincin nak babu abinda ya yi mata, ba cika son abinci ta yi bama a rayuwa, hakan ya sa ta fara yin tsuru tana kallonsu daya bayan daya ta ga dai abinci kowa ke ci banda Auta dake dan fama da nata ta kasa ci da kyau
A hankali ta ce" Bakya son tuwon ne?"
Auta ta dago da sauri ta kalleta, a hankali ta saci kallon sauran, gannin babu wanda ya kalleta sai ta amsa NADIRAH da ido
NADIRAH ta dan karra kallonta ta ce" To ki bari mana ko dole ne?, Kina wani abu kamar an wanka maki mari"
Umma ta dago ta zuba mata kakausan kallo kafin ta budi baki a sanyaye ta ce" Allah ya karra maki lafiya, i ya zama dole ta ci abinci dan ta sha maganinta"
NADIRAH sarai ta karanci sakon idannuwan Umma, ama sai ta watsar
Hasalima mikewa ta yi ba kwaramniya ta shiga dan bubude abincin tana rufewa, yannayin da take yiwa fuskarta kamar ta ga wani abinda bata son ci mai warin nan ke karra kunna HUZNAH
Karshe ta maida dubanta kan abubuwan dake gabansa
A soyayarta da nono ko a me aka saka shi kallo daya zata yi masa ta gane menene
Murmushi ta yi ta dauki manyan kofuna na kwalba biyu ta ajiye ta mika hannu ta dauko nonon da ake tofe masa da addu'a daga wajen SHEIK sannan a kawo, nonon da ko Umma bata tabawa bale HUZNAH, ta bude ta cika a kofi daya ta mikawa Auta sannan ta cika a daya tana murmushi ta rufe ta koma ta zauna ta sake kallon Auta ta ce" Ki ajiye abincin sai ki sha wannan, yanada anfani sosai ga lafiyar dan Adam"
"A kan wani dalili zaki taba abin madarar mai martaba?" Muryar HUZNAH, da yannayi na ta fara hasala ta yi maganar
Kafin HUZNAH ta sauke harufanta Umma ta dauki nata itama a dan hasale ta ce" A kan wani dalili zaki saka yarinya ta sha madara bayan tuwo nace ta ci ta sha maganinta ne?"
Idannuwansa ya rintse, hayaniyar ta farra hawa kansa, jira yake ya ji ta yi magana a haukacen da ta saba, sai ya ji shiru
Hakan ya saka shi dago dubansa ya shiga binsu da kallo su dukansu
Su amsa suke jira daga gareta
Ita kuma ta dauki madarar da aka mata magana a kanta dan bakin rashin ji ta kai baki ta lumshe ido tana shanye masa madararsa, madararsa fa, shi fa, shi ASADEEK jama'a Rasulullah (S.A.W) 🚶🏻♀️🚶🏻♀️🚶🏻♀️🚶🏻♀️🚶🏻♀️
NADIRAH kuwa a ranta ayanawa take yi' ku bari na sha na dawo hayacina, sai mu baje idan hali ya kama, ai ba'a gwa da gwa da yinwa kawuna uwa dutsin jifan shedan!'
Tashin hankali, ita bata san me ake nufi ba hala? Mun shigesu🥺🥺🥺🥺
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```

*https://www.facebook.com/106494781436168/*
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
_FREE BOOK_
*Na*
*SAJIDA NIGER*
3️⃣3️⃣
Sai da ta gama shanye madarar nan, ta lumshe ido tana jin yadda take ratsa mata kirjinta, watau sanyi ne da ita madarar, tana matukar son madara mai sanyi ama innarta sai tace aa in dai zata sha ga mai dumi kawai ta sha
Idannuwanta ta bude hankali kwonce ta sake mika hannu ta dauko dan tsinken sakace hakori kamar wace ta ci naman kazi ta dan bude bakinta kadan ta tsatsaka sai kuma ta yi wani tsut tsut da bakin nata sannan ta barshi a ciki tana dan wasa da shi a bakinta
A wajen nan Auta ta fi kowa jin kamar zata kurma ihu, domin tun kallon na mutun biyu ne har ya dawo na mutun uku sunna kallonta, amsa suke jira ama NADIRAH ta gama ta yi shiru abinta da bakinta
Umma, ji take yi, wani irin ashariya, irin na maguzawa, irin na mutanen kafurci na mata yawo a harshenta, so take ta yiwa yarinyar nan abinda bata taba tunanin ana iya yiwa mutun a duniya ba, sai dai wanzuwar UMUGHLUK a wajen ya sakata kasa barkata hakan
Ajiyar zuciya NADIRAH ta sauke ta kalli HUZNAH dake kallonta ta daina cin komai
Murmushi ta yi mata ta ce" Aunty, ba'a taba madararsa ne? Ko nice ban zama ta gida ba?"...........
Sai kuma ta kalli Umma ta ce" Umma, magani ai idan an sha madarama ana iya sha ko? Bata ra'ayin cin tuwon idan aka takurata sai ta samu matsala ai inaga ko?"
"Ba maganar kasancewarki yar gida ko yar wajen gida bane, babu mai taba madararsa, yaya zaki taba baki tambaya ba kanki tsaye"...... HUZNAH ta fada tana dake fuskantar Nadirah
Ko ajiye maganar bata idasa ba Umma ta ce" Bama wannan ba, maganar cin abincin Auta, shanta, komai nata nice a gidan nan, babu macen da zata shigo ta shiga ciki domin nice mamanta, kin gane? Kuma rashin lafiyarta dole ta ringa cin abinci a kai a kai "
HUZNAH ta sake cafewa, dan bata ga a kan me Umma zata hannata fadin nata damuwar itama ba, a birkice ta ce" Aa Umma, ai dolene nima na fada mata ta gane cewa madararsa, abu ne mai matukar mahinmancin da shi kadai ke shan abinsa, ko ke bakya tabawa, haka nima, ta zo ta dauka ba izini ba komai ta sha ta ba Auta?, Ai ba haka ake yi ba, ba wai maganar tana matarsa ko yar uwarsa bane, a gidana ta sameni dole zata bi takun tafiyata!"
NADIRAH ta sake waro ido wata shegiyar dariya na tukota, a hankali ta kai hannunta wajen bakinta ta furta" Toh fah" domin abin ya bata mamaki ainun, bale da kamar hayaniya da yar cacar baki ke neman kaurewa a tsakaninsu, hakan ya sa da sauri auta ta shanye madararta tana sake kallonsu itama
NADIRAH ta kalli wannan, ta kalli wannan mamakinta ya ki barinta, gaba daya sai ta samu kanta da raina masu ajawali walahi