← Book details Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 99

Sashe 32

Zakin Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana cikin hayacinta da bin takun kowa a gidan nan, har yau da ya rage kwana uku a daura aurenta, sunna zaune tana jin yadda mararta ke mata wani irin nauyi aka zo da mota baka sidik da direba daya tak sai GIMBIYA, wace tana fitowa ta ga ikon Allah irin yadda mahaifiyarta da Innarta suka yi dan yi mata barka da sauka

Kanta a sama, ko tace hancinta a sama ta yiwa NADIRAH kallo a hanzarce, sannan da ido ta yiwa Fadime alamun da ya saka Fadime saurin kama NADIRAH suka shige ciki watau uwar dakar FADIME

Cike da isa ta idasa shigowa, fuska babu fara'a a tsaye tana kallon FADIME ta ce" Ina fatan, kin jadada mata wacece ita, haka kuma kin shaida mata me zai kaita BABAR FADA?"

Fadime ta karra sada kanta ta ce" Na sanar Mata Allah ya taimakeki"

Gimbiya ta karra duban NADIRAH sama da kasa tana mamakin kira, kyawun halitar yarinyar, sai ta ji a zuciyarta tana son yin kiran UMMA ta fada mata lalle lalle itama wannan a bata abinda aka ba matarsa ta farko ta sha, kar aje kilu ta janyo masu bam! Yarinyar ba abin wasa bace, bale a yanzu da take tsaye darrr Mahaifiyarta na duke? Ta saka mata wani shaka da tunani mai yawan gaske a ranta

Kanta ta sake cirewa ta kuma duban FADIME ta ce " A nan zaku zauna har bayan auren, a yanzu na zo da BAHIJA, zata tare a nan, Fadime zaki kular min da yarinyata, dukkan abinda take so kamar yadda kika saba, ki sani da waya a gefena, kuma kasamcewarki a nan ba yana nufin kin tashi daga matsayin da kike bane kin fahimta?"

NADIRAH ta sake saka idannuwanta tarr cikin na Gimbiya da ta sake juyowa ta kalleta, Gimbiyar ce ta cire idannuwanta tana kada kai ta dora da fadin" Kar na ji ko na ga labarin an barta ta fita, kuma kar ta yi bako ko bakuwa, domin jarida tuni ta fara yawo cewar za'a daura aurenta da ASADEEK!"

a zabure FADIME ta dago ta kalli Gimbiya, sannan ta mayar da kanta kasa, subahanalah, Gimbiya ce ke kama sunnansa a waje gatsau hankali kwonce? Lalle ta shirya

NADIRAH kuwa baki ta samu kanta da tabewa, a saman lebenta ta maimaita sunnan sannan ta watsra ta sake fuskantar matar nan da ta jima tana fata Allah ya nuna mata ta dauketa da mari a rayuwa

"Sarki ya yanke cewa , ana gobe daurin aure zai zo ya dauketa da kansa ya wuce ta falonsa da ita dan gudun yan magana, ki karra jadadawa yarki biyaya itace makulin samun lafiyarku baki daya!" Ta sake fada a kausashe tana watsawa Nadirah wata mahaulaciyar harara, sai dai kikim din nan irin na yara masu taurin kai haka Nadirah ke tsaye bata sanyaya ba, a dole Gimbiya ta gama dukkan sharudan ta ta juya ta fita tana leleka dakunnan dan gannin wanda y'arta zata iya rayuwa a ciki!

"Innah ki tashi mana ta fita " NADIRAH ta fada muryarta a raunane tana kallon mahaifiyarta

Innarta ta dago tana murmushi ta ce" To indin Hindu bara na je na ga me zan mata?"

Da sauro NADIRAH ta ce" Aa ki zauna bara na je na yi koma menene kin ji Innar Abana?"

Kai ta girgiza tana ficewa, dan ta kula y'ar nan kamar bata jin nasihar a duka a gaban manyan nan sam, yaya NADIRAH zata tsaya kanta da kan Gimbiya? Kai subahanalah

Sai da gimbiya ta samu rantsatsen daki aka saka kayan BAHIJA dake ta aikin waya sannan ta dubi Bahijar da sam bata damu ba ta ce" Daughter, kin dai ji abinda na fada maki ko? Ki yi kokari ku shirya da abanki, sannan ki yi iya yi ki ki rike kafarki da wayarki, ba kowa zaki yi hira da shi ba, ba kowa zai san inda kike ba"

A dan kagauce tana magana da kawarta ta dan dakatar da ta ce" Momcy na fahimta gide, shima Papa din bai hadu da gayen bane, na masa uzuri da zarar sun hadu da kansa zai saka min albarka, momcy kin san Fadime ba zata iya aikina duka ba ko? Gaskiya ki san ta yadda zaki sama min baiwa ko dan murzawar jikina da susar baya, ita sam bata iya sosa baya ba gaskiya"

Kai mahaifiyarta ta gyada tana kallon yar ta gama abinta ta shige dakin tana mayar da iPhone dinta kunnenta

Ajiyar zuciya ta sauke tana ji zata yi missing din yarinyarta, sai dai ba komai zata jure in sha Allah ( uhum)

Har bakin mota Fadime ta raka Gimbiya, har ta kama zata shiga ta juyo ta sake fuskantar FADIME a kausashe ta ce" Ina fata yarki bata fi karfin ki ba?"

Fadime ta sake kallonta da mamaki

Gimbiya ta dage kafadu ta ce" Dan bana son abinda zai je ya dawo, kar ki manta a hannuna ikon ci gaba da walwalarku take!, Na ga ta cika tsaurin ido ko rashin kunya ne? Kaina da nata a daidai da junna bata duka ba"

Ajiyar zuciya Fadime ta yi, a sanyaye ta shiga bata hakuri , ita kuwa ta ja tsaki ta bude ta shige tana umartar Dorevmban kan su tafi

Jiki ba karfi ta dawo dakin nata, dan sai take ji gaba daya gidan kuma a yanzu ya zama ba gidan da zasu wala ba, domin ita ta san wacece Bahija tun yarinyar na zannin goyo

Tana bude dakin ta saka kafarta guda ta ji muryar yarta, kamar tana fada fada tana fadin" Kowani wawa sai ya taka mahaifana? Bayan biyayar da ta masu zata hakura da komai ta barwa Allah sai an biyota da shashashar magana? Idan Innar Abana ta yiwa wancen abar da ka kawo bauta Allah ya tsinen ......"

"Cuta da malati dan ubanki makadi indi!" HINDU ta fada tana tareta hadi da buge mata baki

NADIRAH ta janye tana kama abin gado ta ce" A lokacinda tace ASADEEK yake ko wa? Kiris ya rage na dauke yamutsatsen bakinta da mari!"

"Lahaula wala kuwata ila bilah, NADIRAH, NADIRAH!" HINDU ta fada tana kaiwa zaune hadi da zarro ido

Fadime da ta ji kamar zaninta zai kunce ya fadi dan tsorata ta tare a rikice ta maka kofar ta rufe ta karaso itama ta yi zaman yan borin a kusa da kanwarta

Muryarta a raunane ta ce" Anya kuwa zata iya aikin nan? Innalilahi mun shiga uku,sunnan UMUGHLUK ne fa NADIRAH!"

NADIRAHN ta tsare su da kallon mamaki, sunnansa? Haramun ne kamawa hala?

Tsuru tsuru ta yi tana jin yadda mahaifiyarta ta cenza yare zuwa buzanci take fada makar zata ari baki, sannan ta nuna masu kofa ta kore su ita da Innarta, domin ba zata bari NADIRAH ta saka mata hawan jinni bs!

Daga wannan ranar Nadirah ke gannin abin takaicin da ya fi kona mata zuciya

Yarinya karama, ko wanka sai an cudata

Sau biyu tana satar jiki da nufin zuwa ta cudata dan ta ci uwar babanta a bayin ana kamata a hannata zuwa!

Yarinyar kan mike kafa innar birni ta murza mata

Abubuwa dai da duka saka ta tsani sarauta!, Sai dai kashhhhh.....lamarin normal ne
Fadime dai baiwa ce, Bahija kuwa yar sarki ce
Yin hakan ba laifi bane, idan babu rashin mutunci da wulakanci, domin Bahija ke sanye da alkyaba, ita kuma da hijab irin na bayi.

Kwonci tashi har ya zamto daurin aure za'a gabatar a gobe ranar asabar a sabuwar shekarar musulunci

Cikin gari ya dauka, domin baki sun karaso an sauke su a manyan hotel da manyan gidajen masarautar

Baki ne na gani na fada, baki ne masu daraja, domina ciki harda CHEIK wanda ke rike da sadaki, duda zuciyarsa cike take da zulumin rabuwarsa da UMUGHLUK ITIFAL, domin irin abinda UMUGHLUK ya nuna masa kamar auren nan da wata manufarsa ya amshe shi, uwa uba ya dauki Gimbiya da Auta sun tafi kauye wai, abinda bai taba yi ba, Umma kuwa itace ja gabar matan da zasu amshi yar sarki a matsayin matar UMUGHLUK ITIFAL su sadata da dakinta........................

Cikin masaurauta kuwa karya karyar da ake yi kai zaka yarda cewa eh lalle Bahija ake aurarwa idan ka gani, domin kai da fata baki da bayi sun mayar da hankali sunna gabatar da nasu kalar shirye shiryen aurar da yar tal , kwalin kwal yar gata yar sarki wa baban Sarki, wa zai bari a barshi a baya?

A cen cikin falon mai martaba kuwa su uku ke tsaye, magana suke tamkar zasu kashe kansu, UMMA, SARKI, GIMBIYA

Rai bace ya warci alkyabar da Gimbiya ke bashi wace za'a lulube NADIRAH da ita ya juya ya fice ta cen hanyar dake boyayiya a gidansa ya shiga motar da munafukin amintacensa ke jiransa suka dauki hanya............

A cikin falon kuwa UMMA ta maido dubanta kan GIMBIYA rai bace ta ce"

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*

*SAJIDA NIGER*

2️⃣2️⃣

Rai bace Umma ta ce da Gimbiya" Me yasa kuka cika yin sake da lamarin ASADEEK?, A kan me zaku yarda maganar nan ta fita daga bakunnanku? Dole sai kun sanar da wa'inda ke kasa da ku abinda yake faruwa?, Ashe karfin mulkin da kuke da shi a garin nan ba mai karfi bane da sai kun sanar da bayi da mutanen gari uwa uba mutanen dake karkashinku sunna cin shinkafa abinda yake faruwa?, Yanke hukunci naku ne, su kuma yin biyaya nasu ne, basu da zabi, basuda abin fada!, Ki san kin saka an yi yadda za'a yi da wa'inda suka san ainahin maganar nan, domin ba zan taba yarda maganar nan ta fita ba da sunna na a ciki!"

Itama gimbiya cike da tashin hankali da kuma bacin rai ta ce" Ki daina yi min ihu a kai malama!"

Da gautsi Umma ta ce" An maki ihu me zaki iya yi? Na ce me kike iya yi dan an maki ihu?"

UMMA ta fan matsa dan har yawu Gimbiya ke patsa mata irin ranta ya yi mugun bacin nan
Chapter 32 · 0% Book details