← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 85

Sashe 84

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Mijinyawa:.
Yana kallon Hindu da Azgar har motarsu ta fice daga cikin gidan. Sabida damuwa da ruÉ—u yasa Qasimu ya mance da batun rufe get a haka suka bar get É—in a hangame sukaita gudu bisa hanya.
Babu me magana a tsakankaninsu tunani kawai mijinyawa yake faman yi, da irin yadda tun a baya lokacin da Hindu bata samu haihuwa ba, akaso a rabasu, aka saka musu wa'adi ko samun ciki, ko sakin Hindu da yin sabon Aure.
A lokacin alƙiyamarshi ce ta tsaya. Sai gashi yau bagatatan sun rabu da Hindu rabuwa irinta har abada, rabuwar da babu batun dawowa aci gaba da rayuwar Aure. A cikin ranshi ya ƙudure sai dai shi da Hindu su haɗu a darrussalami.
Idanunshi ya rufe tare da jingina kanshi yasa hannu ya dafe zuchiyarshi yana tuno É—umbun alkhairan Hindu a cikin rayuwarshi. Hindu mutum ce, yasan tana da taurin kai. Kuma yana girmama taurin kanta tunda bata raina kowa, kuma akan gaskiyarta take taurin kai, bata yadda a takata ko a tauyeta ba. Yasan da taurin kan nata tafi mata dubu, ta yi biyayyar da marasa taurin ma bafa zasu iya ba.
Murmusawa yayi daya tuno ciwon da yayi ta faman dashi, da yadda tayi mishi jinya.

Tunani:
Ina kwance jikin nawa babu daÉ—i gaskiya.
Gambo da mijinyawa Babba su suke jinyata ta ɓangaren kaini banɗaki, tsarki, wanka. Ba dan gazawar Hindu ba, sai dan suma suna ganin iyakar tallafin da zasu yi mun kenan, su ba kuɗi garesu ba shi yasa suke yi da ƙarfinsu.
Hindu kuma itace sha ƙundum na jinyata, tayi da jikinta, tayi da aljihunta, tayi da lokacinta. Itace fita aiki, itace abincinmu, itace kuɗin maganina, ga kuɗin makarantar yara. Watana shida cib a kwance sai an kwantar sai an tayar. Ina tuno sanda ta ɗauki gwal ɗinta ta siyar ranar komawa asibiti ta kaini asibiti, taita jigila dani, a lokacin ma gado aka kuma bamu haka taita turawa ba gajiyawa. A lokacin su Gambo da Mijinyawa duk sun watsar sun gaji, suna dai shigowa da safe abinda nake buƙata su mun, ko wanne ya kama gabanshi. Ko Baba sojanmu ya tambayeta matsala sai tace duk babu matsalar komai, komai anayi mun a gida. Kuma a lokacin ko su Yaya Jamila sau biyu kaɗai suka zo asibitin suka duba ni, babu abinda akayi mun daga gida, tsayuwar kirki basu iya akan jinyarba. Hindun dai jurau ita aka bari da zama dani"

Dawowa daga tunani:.
"Mijinyawa wannan tunani haka daka lula na menene? "
Cewar Qasimu daya katse mishi zaren tunanin nashi.
A hankali ya buÉ—e idanunshi da sukai jawur dasu ya dubi Qasimu. Ya juya ya dubi Sabira wacce har lokacin kuka take yi amman marar sauti, idanunta sun kumbura sun yi jawur dasu.
Laɓenshi ya lasa wanda ya bushe ya zuba ma titi ido kawai.
"Ka kira Lauwali ka sanar dashi mun taso kuwa Gawata? "
Girgiza kai yayi kawai.
"To taimaka dai ka kirashi sabida asan da tasowar tamu ko ba gaskiya ba. Gawata bazan ce komai ba, amman in muka isa sai mu tattauna. Danne ka kira Lauwali. Sabira kun karya ma kuwa? "
Qasimu ya tambayeta a sanyaye, sabida yanayin yarinyar dole a tausaya mata. Shi dai yaso yarinyarnan an barma Hindu ita gaskiya.
Kai kawai ta É—aga alamun aa basu karya ba.
Kafin mijinyawa ya kira Lauwali wayarshi ta shigo shi. A hankali ya É—auka murya a sanyaye yace.
"Lauwali yanzu nake shirin kiranka"
Lauwali yace.
"Da jin muryarka haƙiƙa iyalinka bata amince ta biyoka ba Gawata. To ni abinda nake so dakai tunda Asama'u ka riga ka saketa, ita matarka ta nuna itama ba zata zauna dakai ba, ba shikenan ba Gawata sai ka sauwaƙe mata kawai ka huta. Nasan baka kyauta mata ba daka Auri yarinyar data riƙe ta rene ta ba. Amman ai ƙaddarace yanzu saita riƙe wannan a matsayin dalilin da zata horas dakai. Ka rabu da'ita kawai dan Allah. Kazo Katsina mu da muke da fararen mata. Matana suna da ƙanne kyawawa in kazo ba sai ka zaɓi ɗaya ba? " Da dariya ya ƙarashe zancen nashi. Murmushin takaici kawai Mijinyawa yayi. Lauwali baisan dawar garin ba, iyakar Auren Asama'u ya sani duk da ya kasance abokinsu tare suka taso, amman ba ko wanne aboki bane Amini. Wannan labarin a tsakanin Gawata, Hindu, Qasimu, Baraka sai ita Asama'un aka burgeshi kawai.
"Lauwali kenan. To matan naka har nawa ne haka da kake dukan ƙirji? "
Dariya Lauwali yayi sosai dake É—an yine shi sosai dama.
"Ai kai dai Allah ya kawo ku lafiya. Nifa ba matsoraci bane daka ganni, É—an taran aradu da ka ne"
Da haka sukai sallama Mijinyawa ya sauke wayar a kunnenshi. Ya kalli Qasimu, shima kallonshi yayi sukaima juna murmushi kawai. Shi kaÉ—ai yasa me yake ji.
Saƙone ya shigo wayarshi.
Da mamaki ya buɗe saƙon, gafa abinda saƙon ya ƙunsa.
_ina mai farin cikin sanar maka, ni Asama'u Aurena ya mutu. Sabida Allah ya ƙaddara ni taka ce har abada. Da zaran na kammala iddata zan soma farauto soyayyar mijina, kuma Babana, wannan mai yawan tausayin nawa_
Shiru yayi, tare da lumshe idanunshi, baisan me zaice ba, bai kuma san me zai yi ba.
Mamaki Asama'u take bashi, duk da yasan Halimace ta lalata komai, amman bazai daina mamamaki ba.
Abinda Asama'u da Halima basu sani ba shine. Idan duk duniya zasu taru a kanshi shi da Asama'u har abada.
Yanda bazai iya auren Sabira ba. Haka bazai iya auren Asama'u a karo na biyu ba.
Tafiya kawai suke yi babu magana, sai jujjuya lamura a kanshi yake yi. Allah cikin ikonshi da amincewarshi suka shiga garin katsina lami lafiya cikin aminci.
A ƙofar ƙaura gidan Lauwali yake.
Tsakanin ƙofar ƙaura zuwa kan titin Ibrahim Babangida IBB way inda babban reshen first bank yake a katsina babu nisa. Ba wannan ne kaɗai firat bank ba, akwai sauran dake wasu wajajen amman wannan da aka turo mijinyawa shine Babba. Akwai bankuna da dama a wannan yanki, ga gidajen ma'aikan gwamnati irinsu Lauwali kenan.
A hankali motarsu ta sulala cikin unguwar ana maƙale da Lauwali a waya yana fasalta musu hanya har suka iso inda yake tsaye, a gaban gidan da yayi kama da nashi, saye da jallabiyya mai ruwan toka, da tumbinshi kaya guda a gaba.
"Kaga Lauwali masu gidan ruwa na jihar katsina ba. A taɓaku a kwana da ƙishin ruwa"
Dariya Lauwali ya saka ya miƙa ma Qasimu hannu suka tafa taf har suna tsalle dan jin daɗi.
Mijinyawa da Sabira suna cikin mota basu sakko ba, kallonsu Mijinyawa yake yi yana ji ina ma shine su da basu da damuwar komai .
"Qasimu koma mota a shiga da motarnan ciki kaji. Gawata sai kallonmu yake yi muna ƙular dashi, yadda kasan mu muka kar zomon"
Komawa Qasimu yayi cikin mota.
Maigadin gidan ya buɗe musu get suka shiga cikin madaidaicin farfajiyar gidan, ga motoci fake guda huɗu a tsakar gidan a cikin ƴar rumfa. Su Mijinyawa sai a gefe suka saƙala tasu motar, a kaikaice sabida tsakar gidan ya cushe.
Fitowa suka yi daga motar.
Lauwali yace.
"Sabira kece kika zama haka? Qasimu yarinya ai budurwace sosai"
"Kai da ƴarka ashe baka san ma ta girma haka ba Lauwali, ai ta gama sakandare gamawar kenan. Ta soma jami'arta anan. Shi kuma wanta da muka baro a can ya kammala jami'ar za'ace saura bautama ƙasa kuma."
"Ha'a Azgar ko, to shi ina aka baroshi ne. Ba tare akace za'azo dashi bane da. Ko Hindu taƙi ba da shine, ko sai ya kammala bautar ƙasan?"
"Maimakon ka shiga damu amman ka tsaya sai zance kake mana, kai kuma kana ta biyeshi a gaban Æ´arku"
Cewar Mijinyawa da yake jin haushinsu kamar me.
"Ina wuni Baba"
Sabira ta faÉ—a a sanyaye. Tausayinta ya kuma durama mijinyawa kamar ya zubar mata da hawaye.
Oh ko yaya rayuwarta a cikin ahalin da bata san su ba zai kasance mata oho. Shi tsoronshi Allah kada a lalata mishi tarbiyyar Æ´a shine abinda ke yawo a zuchiyarshi. Da ace Sabira na da saurayi kuma ya cancanta Aurad da'ita zai yi ya huta, wallahi yafi mishi kwanciyar hankali.
"Lafiya lau Sabira sannu ko? Ku biyo ni, in yaso kayan zuwa anjima in kuka huta sai a sakko dashi"
Suna biye dashi har izuwa babban falon gidan inda ga kulolinan an zubesu a ƙasa da kayan sha na tarbar baƙi, da duk abinda za'a buƙata.
Matan gidan su biyu suna falon a zaune. mijinyawa suka shigo.
"Baƙi sannunku da zuwa maraba"
Cewar Amaryar Lauwali Æ´ar katsinawan dikko kenan.
"Yauwa sannunku, da fatan mun same ku lami lafiya ko?"
Nan aka shiga gaggaisawa sai ga Sodangi uwargidan Lauwali kenan Æ´ar mutan Gombawa, tare da Yayanta namiji da ya kawo mata ziyara.
"Ah Sodangi Yaya Jaddo ba dai tafiya zai yi ba ko?
(Jaddo a al'adar fulani ana nufin mutum mai daraja, jarumi, ko dangi nagari) .
" A'a ba tafiya zai yi ba. Yana son kaima wani abokinshi ziyarane. Yama zo ɗaukarshi yana waje. Gawata, Qasimu sannunku da zuwa kun shawo hanya, ashe rai kan ga rai. Ƴata Sabira sannu da hanya. Taso muje kinji? "
Sabira ta miƙe a tsanake ta gaishe da Sodangi, ta juya ta gaishe da Jaddo wanda tunda suka fito idanunshi a kanta.
Juyawa yayi suka gaggaisa da su Qasimu ya fita akan zai dawo da Magriba bazai kai isha ba.
"Sodangi Sabira ta zauna a wajenki, tunda a ɓarayinki akwai ƴan mata har huɗu zata fi sakewa."
"To maigida in sha Allah babu komai zan riƙeta amana. Ina kayanta suke fa? "
Lauwali ya shafi tumbinshi yace.
"Kaya suna mota ko anjima sai asa yara su kwaso"
Hannun Sabira ta kama suka shiga ciki. Tsoro da fargaba duk sai ya shigi Mijinyawa. Sai da matan Lauwali suka basu waje falo ya rage daga su sai su. Mijinyawa yace.
"Lauwali kana da yara mata kuma kake barin namiji ya shige har can can cikin gidanka? "
Qasimu ya tuntsure da dariya shine harda ƙwarewa dan shi tuni ana wannan dudumar gaishe_gaishen yana ta aikin zuba musu tuwo.
Mijinyawa ya dubi Qasimu idanunshi suna layin ciwo, wani irin ciwone yake bijiro mishi ainun.
"Namiji baya shigarmun can cikin gidana. Jaddo da kake gani ɗan uwan Soda ne, baima daɗe da dawowa daga ƙasar waje ba, yayi phd ɗinshi. Likitane babba, sai dai bansan fannin daya karanta ba. Harma ya buɗe ɗan asibiti nashi, muma damu akaje akayi bikin buɗe wannan asibiti. Dalilin barinshi da nayi zuwa ciki shi mutumne wanda in nutsuwa da hankali suna ma mutum yawa to sun yi mishi. Wannan shine karonshi na biyu kacal daya taɓa kawo mana ziyara. Kaji dalilin da yasa na aminta dashi har ya shiga ciki. Akwai ƙannen ita Soda da nake riƙewa su biyu, suna makarantar Jami'a a garinnan, to kaji.
Shiru Mijinyawa baice uffan ba, bashi da abun faɗe, sai kawai juya tuwo a cikin miya da yake yi. Loma uku yayi kacal ya sha kunun ayan da ɗan dama. Jinshi yake yi tamkar ba shine ba sam. Bai tabbatar da haka ba har saida suka koma muhallin saukar baƙi, ciki da falo da banɗaki harda kicin, kuma akwai abun girki, da tukwane.
"Kaga in girkinka ma kake son yi akwai komai har kayan abinci akwai. Akwai wani bawan Allah da yazo daga garin Kano ya zauna damu na shekara biyu.
Ya kasance mai kiyayewa da tsoron Allah, kai harma da mutane tsoronsu yake ji.
Rubutu yazo yayi na littafin hausa wanda ya tattare irin matsalolin da suke kawo mace macen aure, yana da burin ya buga in Allah ya bashi dama. Amman kai kam daga cikin gida za'a dinga kawo maka abinci"
Mijinyawa bama ya jin me yake faÉ—a gabanshi sai sake tsananta faÉ—uwa yake yi. Sannan jikinshi na bashi tamkar za'a lalata mishi Sabira, gata mace balle yace zasu dinga kwana tare. Azgar ne ya faÉ—o mishi. Murmushin dole yayi kawai, baisan wanne fassara zai ba murmushin ba, shi dai yayi ne kawai.
Amman fa fat_fat gabanshi ke faÉ—uwa sai sake tsananta yake yi.
Tunanuka sun cika kanshi, yana hango Talatu bankin farko da Asama'u da suka zama wasilar tarwatsa mishi ginin soyayyar da ya shekara ashirin da biyar zuwa shida yana ginawa.
Amman yasan ya fisu girman laifi, hukuncin da Hindu ta yanke mishi, da Azgar hukuncine mai kyau wanda ya dace dashi. Bai ga laifinsu ba sam. Sai dai ya tabbatar zuchiyarshi ba zata iya É—auka ba, rayuwarshi babu ta yadda zata tafi da kyau babu Hindu da Azgar a cikinta. Abun kamar da wasa kafin Magrib mijinyawa baya iya gane wa yake kanshi ma kwata_kwata, ranga ranga a sume cikin fitar hayyaci su Qasimu suka wuce dashi asibiti a motar Jaddo har da Sabira, sai kuka take yi. Dukane a kanta tako ta ina kawai.
Anan ƙarshen harƙa ta biyu yazo ƙarshe.
Sai mun haɗu a harƙa ta uku sabuwar tafiyar da zaku ji ƙarashen tarihin rayuwar Gawata da Hindu zai zo muku a tafiya ta uku.
Ƴar uwa ki buɗe zuchiyarki sosai, a cikin karatun nazarin da kika yi, ke wanne babban darasin kika koya.
Sannan me kika koya daga Hindu
Wanne darasi a dunƙule zaki ce littafin na bayar
Menene babban jigon labarin?
Wanne saƙo labarin ƙawayen Hindu ya isar miki ke a karan kan ki kanki?
Shin kin jinjinama mrs Bukhari kuwa?
Chapter 84 · 0% Book details