Sashe 28
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hindu: Bani na farka ba sai wajajen sha ukun rana shima wayatace aketa aikin kirana a waya ashe Luba ce keta kirana. Cikin muryar bacci na ɗauka. "Hindu mutuniyar taki fa ta haifo ƴan biyu dukka maza wallahi. Ke kinga yadda Sunusi yake ta gigi yadda kika san a kanta aka soma haihuwa kin ganni a asibiti ina hanyar zuwa gidanki" Dariya na saka tare da cewa. Dama a danginta suna da ƴan biyune? " "Sosai kuwa itama ƴan biyu take bi Gambo ce ai. Mahaifiyartama Usainace. Ashe sabida ma hakan Sunusi ya Aureta. Ke dai saina ƙaraso a ajjiyemun abinci dan wallahi yinwa kamar zata halakani" Tsaki nayi mata na datse wayata kana na miƙe na nufi banɗaki, ina jin jiri, na sake gargasa jikina na ɗan ji dama_ dama ba laifi. Riga da siket na jar super na saka bayan na gama lailaye fatata da mai. Kwalli kaɗai na zirara a kumburarrun idanuna da har yanzu basu yi haske ba sunanan a rine. Na shafa humra na ɗan gyara gadon na jona bona na zuba turaren wuta, dana gabatar da sallah, saina fito a hankali dan jikin sai a hankali kawai, ko ta ko ina ciwo ne. Shiru naji halamun babu kowa a gidanne ko bacci suke yi ne oho dai, amman ko'ina a gyare yake fes. Ina tsaye cike da tunanin ina zan dosa falo ko ɗakin Sabira sai naji ta turo ƙofar ɗakinta ta fito. "Ammi kin tashi ashe inata leƙawa sai inga kinata baccinki" Murmushi nayi mata kawai. Me kuka dafa Sabira? " "Ɗumame muka ci Ammi. Amman nace in kika tashi sai in dafa miki taliyar yara akwai shayin Ahmad a filas kije falo yanzu zan gama miki minti goma" Ta ƙarashe da sigar zolayata, dariya nayi mata dan taji daɗi kamar yadda nima tasa naji daɗi. Yarana su suke yayemun damuwar duniya wallahi. Allah yaba duk macen dake neman haihuwa masu albarka. Ki dafa da Ummanki Luba tana hanya kar ki cika yaji. Nasan ma in dai taga taliyar yara wallahi babu abinda zai hanata mita" Ina maganar ina tafiya har zuwa falo. Wayata na buɗe na shiga manhajar WhatsApp domin ganin me ke tafiya a zauren gida game da bikin Salamatu da suka tasamma ƙarya. Nan naga saƙwanni sunfi dubu da ɗari biyar, dariya nayi nasan akwai lallai abinda ya faru tabbas jikina har tsuma yake na shiga. Da hoton motar Salamatu naci karo sabuwar mota fil da rubutu a ƙasanta kamar haka. "Wannan tukuicine Zauji ya bani na amincewa da Aurenshi da nayi a saka mun albarka" Kallon motar na shiga yi a ƙofar gidanmu ma akayi hoton mota ta iso kenan su Salamatu gaskiya ta samu dama tana ta damawa. Gangarawa naci gaba dayi masu zumunci da'ita sosai kamar ƴan ɗakin Inna Mairamu kenan sai habaici suke sakarwa tare da taya ta murna. Waɗanda gaisawa kawai akeyi wasu Allah ya sanya alkhairi suka rubuta wasu ma stikar taya murna kaɗai suka turo harda masu emoji na jinjina. Ƴan ɗakinmu kyakkyawar adda'a sukai mata duk da irin zaman doya da manjan da akeyi. Ayarin masu mata fatan alkhairi da taya murna na shiga. Wannan saƙwannin na jiya da daddarene, da safe misalin goma sai ga hotunan Aure kuma har uku zafafa ta turo shima mijin gashinan yasha kayan hukumar fasa ƙwarri a jikin rigarshi naga matsayin da yake kai, ummm Salamatu tayi kowa ya samu dama dama ya dama. Dake goduwace sosai ta fishi tsayi shi kuma irin siraran fulaninnanne ita kuma ta haɓaka nama wuyanta cike da gwai mai rawun ba mai kwaɗo ba kun dai gane. Kasantuwarta ƙatuwa sai shi ɗin ya zama tsurut a gabanta kamar bakwaini. Anata masha Allah, masha Allah, ni ko ina zaune ina dariya na jiyo muryar Luba suna yi da Sabira. Shigowa tayi tana haki. "Wai Hindu nima wannan taliyar yaran na jaraba zanci? Wallahi bazan iyaba kinsan basir gareni yaushe ma zata riƙe mun ciki tsakani da Allah, kinsan na tsani taliyarnan fa" Ta ƙarashe tana neman waje a ƙasa tare da cire mayafinta ta jefar ta cire ɗankwalinta ta jefar shima. Luba kenan dama nasan da mita zaki shigo wallahi kuwa. Akwai biredi saita soyo miki ƙwai ki haɗa ai Maman Nawata da Gawata" Dariya muka kwashe dashi mune harda tafawa taf tamkar bamu da matsalar komai. "Hmmm tana asibiti dai ta haihu yau ta yaba ma aya zaƙinta ai taji maza, wai kinga bakinta yadda ta saki yake zubar da yawu kuwa ga laɓɓan sun yi dama girma sabida ciki." To ke ya akayi kika kaita asibiti kuma naga kin caɓa ado ke da kika kai mai haihuwa?" "A'a nifa dama na fito zan tafi gidanmu ne acan zan wuni, in barista Saudatu Mustapha ta kira ta bamu adirrshin inda zamu haɗu sai in tawo daga gida, yara tun Juma'a suka tafi gidan ma. To ina kulle ƙofa na hangota tana rarrafe a ƙasa fa wai in taimaka mata zata mutu. Dana fahimci haihuwa ce saina kamata ta miƙe tsaye nace mata lokacin haihuwarta yayine? Wai ranar wa'adin da likitoci suka yanka mata ya cika. Ina kayan yaro wai bata haɗaba suna saman akwatin saman sib ɗinta. Haka na jata muka je har uwarɗakin nata na zaunar da'ita a kan gado, ni kuma na taka gadon na sakko da akwatin na harhaɗa duk abin buƙata ita dake ƴar gaban goshin miji ce komai da ake siyan ɗaya ita biyu aka siya mata. Ta cika gana mas go da kayan jarirai baki gani ba Hindu. Ni nawa yaran da figi da yagi na haifesu kayan fitar suna tun haihuwata ta fari nake yima kaina Sanusi bai taɓa yi mun ba. In banda zuchiyar musulunci yaushe zan kai mishi mata asabiti." Shigowar Sabira da tiren abinci ya katse mana labarin da Luba ta kwalo bani ina amsa. A gaban Luba ta dure abincin harda ragowar ɗumamen da suka ci ashe yayi saura. To shikenan ƙorafi ya ƙare tunda kin samu ɗumame ko? " "Sosai ma wannan taliyar ba ci zanyi ba sai dai kici kayanki, ato yaushe zan iya nifa wallahi a ƙirjina take mannewa ta zamemun olsa ina dalili" Dariya muka saka Sabira ta fita ta bamu waje, na gyara zama ina kan zuba taliyar nace. Kuma danginta dashi Sunusi sun yaba da namijin ƙoƙarin ki ko kuwa a banza man kare? " "Hindu ai ba'a burge kishiya, ba kuma a birge dangin kishiya, kazalika mijinma ba'a burgeshi akan kishiya, duk abinda zaki yi a mazaunin munafurci ko ganin ƙwaƙwaf yake. A gabana yarta take cewa abu baiyi kyau ba kishiya da karɓan haihuwar kishiyarta, babu fa ɓoye ɓoye ni take faɗama hakanma. Sunusi ban tsaya bi ta kanshi ba ƴan uwanta na zuwa nayo nan. Kuma ni wallahi ranar sunane kaɗai zan zauna a gida. Ko mun taso aiki haƙiƙa gidannan zan zo in tare sai dare zan dinga komawa gudun kada ai mun abinda zuchiyata ba zata iya jurewa ba" Dariya na kuma yi kawai. Muna cin abincin ina bata labarin abinda ya faru dani da mijinyawa, amman iyakar gajiya da yace yayi da ƙananun iskanci, da ƙananun labaran da zata iya ji. Tace shi yasa taga halamun bani da lafiya, tasan mutanen sun kawo ziyara. dana gama na shiga nuna mata motar Salamatu da hoton mijinnata. "Hindu ki ɗan sassauta ma mijinyawa kiyi nazari ki kuma hakaito irin rayuwa mai daɗi da kuka gudanar a baya" Dakatar da'ita nayi har ina ƙwarewa. Dakata Luba ke da Sunusi wacce iriyar soyayya ce baku buga ba a rayuwa wanne irin duniyar soyayyane Sanusi bai kaiki ba, ada gani kike yi kinfi ko wacce mace sa'a duk duniya. Me ya faru daga lokacin da Sunusi ya ga mace ƴar uwarki wacce abinda yake jikinta da wanda yake jikinki duk anko ne. Ba baya ya juya miki ba ya dawo da ragamar komai na gidan hannunki ba? Ɗan hamsin da hamsin ɗin da kuke yi ya dena. Me ya hanaki yafe mishi ku dawo kamar da in kunce ni ina da baƙar zuchiya ke mai farar zuchiya ki yafe ma Sunusi. Luba mijinyawa ya cutar dani ba zaku gane girma da zafin ciwon dake zuchiyata ba. Luba amman zaki iya hakaito irin zafin abinda akayi mun. Yau ko gobe mijinyawa yayi Aure ace babu rikicinnan a tsakaninmu Luba bazan taɓa zamemai damuwa ba, bazan canja mishi ba, zamu zauna lafiya sai dai kinsan bazan ɗauki danne hakki da mayar dani koma baya ba, ba kuma zan ɗauki wulakanci ba kema kin sani. Amman Luba ki gane Mijinyawa Asama'u fa ya Aura, bayan ya Aureta ya haɗa jiki da'ita, yaji daɗi da'ita, yayi mata ƙila fiye da abinda yayi mun. Luba mai tausar zuchiyata ta yi sanyi ban ganshi ba ne kawai ba wajen bane" "Amman Hindu bakya tunanin ya bi Umarnin su Nanno yayi Aure, ya watsar dake kamar yadda kika yi mai. Hindu baki san menene asalin haƙiƙatan ɗin me ake nufi da kishiya ba. Kuma babu mai iya kwatanta miki ya masu kishiya suke ji. Daga lokacin da akace bake kaɗai bace a wajen miji ba to ke da kwanciyar hankali ɗorarre har abada fa haƙuri kawai akeyi, musamman masu zama gida ɗaya irinmu" Dariya nayi mata nace. Bambamcina dake kenan Luba. Ni kinsani in abu ya siremun ya siremun kenan komai zaiyi bazai taɓa burgeni ba sam. Ke kina iya jin zafin kishin Sunusi a ƙirjinki, ni kuma ko yanzu mijinyawa ya auro mata uku dashi dasu basa gabana. Luba wallahi so nake yayi auren sannu _sannu tasa ya mance dani daga ƙarshe ya shafeni a rayuwarshi,ya huta in huta. Ni ko ya sakeni wallahi Allah kinji na rantse bazan taɓa ƙara Aure ba, neman kuɗi kawai zan sake sakawa a gabana. Hajiya nake son in zama ƙaƙas" "Wallahi na sani Hindu, nasan kin rufe da mijinyawa tarihinshi ya ƙare. Amman na tausaya mishi" Harararta nayi, tana ta dariya. Me yasa baki wai yafe ma Sunusi bane Luba to?" "To yaushe yazo yace in yafe mishi ne wai. Sunusin da sai dai ya leƙo mu gaisa, daga bakin ƙofa yake tsayawa fa. Wallahi Hindu na tsani Sunusi. " To bare kuma ni" Mun jima muna tattaunawa kafin muka shiga hirar bikin Salamatu har da nuna mata motar Salamatu da