← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 85

Sashe 55

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

MIJINYAWA:.

"Mijinyawa shikenan mutanenta sun rabketa ni dama nayi tunanin za'a rina, la'akari da irin yadda Hindu take da nacin abinda ta saka a gaba. Haƙiƙa ni kaina wannan yarinya ta bani tausayi. Muje ka saukemu a gida kayi tafiyarka wajen aiki kasan yanayin aikinku ba aiki bane na wasa ba"
Gabaki ɗaya mijinyawa a dame yake, yama kasa magana sai karatun Qur'ani ya saka ƙira'ar malam Sulaiman maja baƙin malam Kabiru Gombe, a haka har suka iso gida ga ofis sai kiranshi akeyi a waya, wasa da aikinshi su suke ganin yanayi, babu mamaki yana da alaƙa da abinda ya taso a wajen aikin ma ga wannan fargabar a ranshi, ga kuma halin da Hindu ta shiga ga damuwar su Nanno, damuwa ce fal kanshi goma da ashirin fireja na neman halakashi.
Su Nanno suna tsakar gida Yaya Jamila na musu wanki mijinyawa ya buɗe babbar ƙofa, kana ya fita ya shigo da motar Hindu suna zaune suna kallon ikon Allah, suka fito da Hindu ranga_ranga babu yadda take suka yi ciki aka shimfiɗeta a gado.
Nanno da Yaya Jamila ne suka shiga har uwarÉ—akin Hindun.
"Wai lafiya aka dawo da'ita a cikin wannan halin ne. Yanzu mijinyawa rayuwar da kai a naka hankalin kake ganin ya dace kaci gaba da gudanarwa da wannan yarinyar kenan? Iyayenta sun zuba maka idanu sai aikin wahala kake yi da'ita, wannan wacce rayuwace haka. Ka saketa kaƙi, ka sake aure saika taramun dattawan gari suita godona. Yanzu ta fita ta kwana a waje, kaida ka fita aiki ka baro aikinka kazo sarama kare ciyawa...."
Shi da Luba adda'a kawai suke ta ma Hindu, har Allah yasa ta dawo hayyacinta.

Hindu:.
Da Nanno da Jamila na soma haÉ—a idanu. Jamila sai kallon É—akina take yi tana mayawa.
Na dubi Luba, na dubi Mijinyawa. Kafin ince komai Yaya Jamila tace.
"Duka wannan mimmiƙewar ta borin kunyace ai. Sabida taje ta kwana a wajen gantal.... "
Muƙewa nayi sai gani a gabanta.
Me kike cewa?
Na faÉ—a cikin É—aga murya.
"Ai kinji me nace, kuma kin gane me nak...."
Tas na gaura mata mari, na sake dallah mata mari. Na dubeta nace.
Kinci abu ta kaza kazan......
Daga yau in kuka sake shigomun gidana na rantse da Allah zaku sha mamaki.
Wai ku wanne irin mutanene, me nene laifin da nayi muku dan kawai na so ɗanku, ashe soyayya na zama ƙiyayyane"
Jamila a fusace ta ɗaga hannunta zata sauke a fuskata. Mijinyawa yayi saurin matsowa, yana ƙoƙari riƙe hannunta, na fishi zafin nama tuni na caɓe hannun, na murɗashi zuwa bayanta, wallahi saida ta saki tusa.
Daga haka ina na zama bani ba.

Mijinyawa:.

"Kana kallo zata kashema Æ´ar uwa kana gani.
Kana jin duk abinda take cewa ai?
Wallahi komai yazo ƙarshe saika saketa. Ƴar iskar yarinyar ƴar mutanen banz...... "
Wallahi kafin ta ƙarashe Hindu ta sureta ta bugata da ƙasa, taje bayanta ya daki katakon kwalliya, sai ga Nanno daɓas a ƙasa tayi zaman daɓaro wanda ya haddasa sai da ƙashin ƙugunta yayi ƙara ƙaƙaƙaƙaƙa_ raɓaɓaɓas.
Hindu bata yi wata _wata ba, ta shaƙe Yaya Jamila Mijinyawa da Luba suka yi suka yi suka kasa ƙwace Yaya Jamila, idanunta sai firfitowa suke yi. Da Luba da Mijinyawa sun sha duka duk wanda ya matso sai a zubar dashi ƙasa, idanun Hindu sun kafe babu baƙi ko ɗis sai wani irin gurnani take yi na rashin hayyaci. Bai taɓa ganin idanunta a haka ba.
Nanno da rarrafe ta fita waje tana kukan a kawo musu ɗauki, amman dake unguwar ba irin wannan unguwar bace babu ruwan kowa da kowa, kowa na cikin gidanshi ƙofa a ɓame.
Nanno ta bugu iyakar buguwa, ko miƙewa tsaye ba zata iyaba sam, bayanta tana jinshi tamkar ba nata bane, kuka take yi ƙaƙas. Hayaƙinta Mijinyawa ya lalubo ya wuce Kicin a guje nan ya tadda Nanno a zaune tana kuka wiwi, bai bi ta kanta ba ya kunna gawayin kanti ya koma ya bunke ɗakin da hayaƙi yana karatu yana tofa ma Hindu tana kawo duka da hannu ɗaya, ɗayan hannun tana riƙe da wuyan Yaya Jamila wanda a halin da ake ciki ta riga da ta sume ma. Dan da dokata da ƙasa da akayi har sau biyu, har fitsari tayishi a tsaye. Mijinyawa ma bakinshi a fashe yake, Luba kuma hannunta ta murɗeshi zuwa baya, harya samu targaɗene ko tsagewar ƙashi, ba'a dai sani ba, amman harya aune ya kumbura, banda mari da tasha, idanunta ya tara jini.
A hankali riƙon ya soma sassautawa har dai ta soma shirin faɗuwa luu, mijinyawa yayi saurin tareta, wallahi yama mance da Yaya Jamila sai ji kuke rututum ta faɗi, da aka ce tsautsayi baya wuce ranarshi, ai saita faɗi a hannunta ya karye ɓararars hatta su Luba sunji rushewar ƙashi.
Shikenan mijinyawa yasan komai na iya faruwa kuma, gado ya mayar da Hindu ya lulluɓeta ya koma kan Yaya Jamila da Luba take ta yinƙurin yayyafa mata ruwa, isowarshi wajen farfaɗowar Yaya Jamila amman fa kafin ma idanunta su gama buɗewa ta sake sumewa.
"Luba taimaka mun mu kaita mota gara aje asibiti da dukkan halamu hannunta ne ya karye."
Da ƙyar suka iya sakata a mota kaya hamago guda, ita kanta Nanno tana buƙatar ganin likita, bata sume ba, amman ta shiga cikin yanayi sai maganar bebaye take yi, idanunta basa ko buɗuwa.
"Luba zan turo Azgar yazo ya taya ki zama da Hindu zan dawo zuwa anjima, ko da ta tashi bata dawo daidai ba hayaƙin yana ajjiye a gaban madubi, da kin turara zata samu bacci. Zamma dawo zan dawo Luba, ki kirani, zan dawo zan dawo"
Mijinyawa ya zauce fireja iya fireja yau.
Nanno ta fashe mishi da kuka da sauri ya shige motar, dama ya riga da ya buɗe get ya fice da motar sai Luba ce ta rufe ƙofar.
"Ciɓiri nannagi wannan karon bayin Allahn nan sun ɗebo mana da zafi Allah masanin abinda ka iya faruwa. Dama su da suke neman dalili bare sun sameshi mai girma kuwa, dan wallahi tsohuwa ta sha bugu Allah yasa sifana kot ɗinta bai zare ba, ga waccan tsohuwar maras mutumcin ni wallahi daɗin abinda suka yi mata naji, suma dama suna da cikin makira. Makaran Hindu yau sun burgeni. Duk da nasan rikicine zai ɓalle gagarumin gaske. Igiyar aurensu tama ɓalle Allah ta gama"
Wucewa ciki tayi da sauri Hindu dai bacci take yi lokaci zuwa lokaci kuma tana É—an zabura. Waya luba ta ciro ta kira Yaya Saratu ta sanar mata Hindu fa ba lafiya.
"Yaya Saratu in da hali ki baro ofis kizo wallahi Allah da akwai babbar matsala sosai"
Hankali tashe tace.
"Ganinan tawowa Luba"
Ƙit ta kashe wayarta Luba na tubkewa da warwarar abubuwan da suka faru, Azgar ya dawo gidan, bai jima da dawowa ba sai ga Yaya Saratu ta'iso itama. Bayan duk an gaggaisa Sai Luba tace da Azgar yaje ya ɗaura abincin rana, dan Hindu da yinwa zata farka bata tsammanin ta karyama. Yana fita Yaya Saratu tace.
"Menene Luba naga dai Halamun mutanenta ne suka motsa me ya jawo hakan, naga ko'ina kaca kaca halamun anyi dambarwar tsiya"
Luba ta kwashe labari silar komai duk ta faÉ—ama Yaya Saratu.
Ta nuna mata hannunta yadda yake ta daÉ—a kumbura. Mayafi ta cire tsabar ruÉ—ani.
"Tabbb lallai wannan karon sun ɓaro aiki babba, dukan suruka da Yayar miji, ai aurenma ƙarshenta dole igiya ta tsinke. Luba ko ni sai inda ƙarfina ya ƙare ace yau matar ɗaya daga cikin ƙannena ta hau iska ta dakar mun uwa, gaskiya za'ayi abunda dai bazai yi daɗi ba gaskiya dai wannan makarai sun jawo mana wata rigima narkakkiya, wannan tarihine da abadan bazai gogu ba, anyi ta gorantama yaran Hindu kenan. Duk da Kinga wannan Jamila tsohuwar maras mutumci kenan dama ita ba wannan ne karon farko da haka ta faru da'itaba. Bana mance lokacin sunan Azgar ne ko irin yadda tai ta abubuwa, tai ta cakale_cakalen rigima har sai da akayi tukunna.
Haka lokacin biki ma meye bata yi ba."
Luba tace.
"Ai ita take zuga ma uwar akan Hindu. Baƙin ciki ke cin ƙasan ranta, zamanine muke ciki wallahi in ba sa'a kaci ba wanda kuka fito ciki ɗaya ma sai ya nuna baƙin cikinshi a bisa ni'imar da kake ciki, ko wata ɗaukaka. Yanzu fa baka isa miji ya soka ya nuna miki kulawa ba, sai ace asirine kayi sabida soyayya ta mutu a ra'ayoyinsu. In kuma kashi miji ke baka kana ɗiban gashi, sai kiji ana Allah sarki Murja Kabiru mijinta bashi da mutumci baki ga yadda yake wulaƙantata ba. Yayin da a gefe guda dariya suke yi miki. Da yawan dangin miji sunfi so suga matar yayyensu ko matan ƙannensu a tagaiyare, suna musu dariya harma a ba wata ɗan kwancan kayan sakawa ko ita ko yaranta. Amman infa cikin rufin asiri suka ganka shikenan ka zama abokin yaƙi. Magana ta domin Allah Nanno ta bani tausayi dan ta bugu sosai, saida bayanta ya amsa da rarrafe ta fita kuka wiwi. Amman uzirin daya kamata aima Hindu shine ba'a cikin hayyacinta take ba, in a cikin hayyacinta take ko sa'insa bata da lokacin yi dasu bare har akai ga haka. Amman wannan uzirin shine zai yi wuya Yaya Saratu. Kuma sun ƙureta sun kaita ƙarshen tuƙewa"
"Hmmm Luba lamarin fa da girma Allah kedai bari kiga in kira Innarmu tasan halin da ake ciki, amman Allah yasa muji alkairi jikina yana bani za'a samu matsala babba."
Wayar Yaya Saratu ke ruri ta ciro a jaka.
"Kinga ga Zubaida na kirana"
ÆŠagawa tayi bayan sun gaisa take sanar da'ita halin da ake ciki, ai take tace gatanan zuwa. Tana kashe kiran ta kira Innarmu ta sanar da'ita halin da ake ciki.
"Wannan maganar tana da girma sosai gaskiya. Zan sanarma Baba Sojanku domin yasan halin da ake ciki, wannan lamarin yafi ƙarfin ya tsaya iyakar Hindu da mijinyawa, dole manya sai sun shiga lamarin gaskiya, amman in sun so adalci sai su duba yarinyarnan ba lafiya gareta ba shi yasa ta aikata hakan. Amman tunda uwar Mijinyawa ba mace bace mai son a zauna lafiya ba nasan abunnan zama zaiyi babban abu. Kinga ga Baba sojanku ya shigo zan kiraki bari in yi mishi bayanin halin da duk ake ciki"
Innarmu ta kashe wayarta, Yaya Saratu ta sauke a sanyaye ta zuba ma Hindu idanu sai zabure_zabure take yi tana ɗan mimmiƙewa kamar ciwo zai sake tashi ai Yaya Saratu da gudu ta bar ɗakin tana haki, tana mugun tsoron masu aljanu a lokacin da aljanun suka tashi musu.
Ganin fitowarta da Gudu Azgar dake tsaye a Kicin yana girki sai yayi ɗakin Ummmanshi da gudu, daidai lokacin suna turka _turka da Luba tana yinƙurin fita Luba na tareta.
Azgarne ya rungumeta yana kuka ya ruƙunƙumeta ƙam yana ta karatun Qur'ani. A haka Luba ta fita ta kunno gaushi ta dawo lokacin Hindu ta wancakalar da Azgar, harta falla mishi mari bakinshi ya fashe idanunshi ya tara jini shima, sai dukanshi take yi tako ta ina. Shi kuma karatu yake yi mata da ƙarfinshi.
"Subhanallahi. Haba bayin Allah wannan É—anku ne Azgar fa. Ku bar Hindu ta huta taji da bom É—inma da kuka haÉ—a mata mana."
Hayaƙi ta barbaɗa a wuta, daga nesa Hindu ta soma shaƙar ƙamshin, azgar yayi saurin tareta yaga tana yinƙurin faɗuwa. Hannunshi ta faɗo ya riƙeta sosai hannunshi na rawa dan tayi mishi nauyi, luba ce tazo ta taimaka mishi suka mayar da'ita gado. Wayar Azgar tana ta ruri lokacin da ake wannan abu saida suka shimfiɗe Hindu kafin ya zaro wayar a ajjihunshi.
"Abbanmune tun É—azu yake ta kirana"
Ya faÉ—a yana kallon Luba, hawaye kaca_kaca fuskarshi, gaban rigarshi duk jini.
"Ɗauki kace mishi da sauƙi jikin kaji? "
Kai ya É—aga mata tare da É—aukar wayar.
"Azgar ya jikin Hindu ta farka kuwa ko har yanzu bata farka ba, sannan basu dawo ba dai ko? "
"A_a bata farka ba Abba, bacci take yi babu wani matsala Umma Saratu ma tazo duk muna tare"
"Toh shikenan zan kiraka anjima inji ko ta farka. Muma yanzu aka shiga da su Nanno ciki jikin Nanno ya tsananta sosai ku taya ta da adda'a, da ƙyar Nanno ta yi rai. Azgar kayi Alwala yayi sallah ka roƙa mana Allah ya tashi kafaɗun Nanno, da Hindu"
"Allah ya basu lafiya duka Abba, in sha Allah zanyi yanzu"
Chapter 55 · 0% Book details